Matan Somaliya da ke sakata su wala a gidajen gyaran jiki

Wakiliyar BBC Mary Harper ta yi nazari kan abubuwan da ke faruwa a gidajen gyaran jikin mata a Somaliya.

A kishingide nake ina hutawa a kan wata kujera, wata mace ta tunkaro inda nake rike da wata zungureriyar wuka a hannunta, mai kaifin gaske.

Abu na farko da na ji, shi ne firgici da tsoro.

A yanzu ina haduwa da matan da ke zuwa inda nake da reza. Wai duk wannan ana yi ne da nufin kwalliya.

Ana amfani da kananan wukake masu kaifin gaske a wuraren gyaran jikin mata, domin kankare zanen lalle da aka yi musu a hannu, da kafa, da ado a wasu sassan jikinsu, wanda ba ya daukar lokaci zai goge sannu a hankali.

A duk lokacin da na je birnin Nairobi na kasar Kenya, kawata Suheyba takan same ni a Eastleigh, wata unguwa mai cike da hada-hadar 'yan Somalia, wadda ake yi wa lakabi da "Karamar Mogadishu". Bayan mun gama cin abincin rana da aka yi da naman rakumi, sai mu nufi gidan lalle.

Shagon wankin gashi na karshe da muka ziyarta dan kankani ne, an dan yi amfani da katako wajen katange shi daga hada-hadar tituna, sun yi amfani da wani yagaggyen tsumma a matsayin labule.

Da zarar ka shiga, komai sauyawa yake yi.

A al'umar da ake sa ran mata su rufe jikinsu ruf, tun daga fuska har kafafu, da yin shiru kar a ji muryarsu, a wurin gyaran jiki matan kan sakata su wala, su shaki iskar 'yanci da walwala.

Yawancin lokuta hakan na faruwa lokaci zuwa lokaci. A wata ziyara da muka kai, wata mata ta yi korafin wurin ya cika zafi. Sai ta cire gyalen jikinta, da doguwar rigar da ke jikinta, kai da dukkan kayan jikinta ciki har da rigar-mama.

Halattacciyar soyayya

Haka lamarin yake a kasar Somalia, inda dole ne duk wata mace baliga ta rufe jikinta tun daga sama har kasa. Yawancinsu kan hada da nikabi na rufe fuska, idanunsu kadai ake iya gani.

Rana ta farko da na fara zuwa wurin gyaran jiki a Somalia, na lura da wani abun ban mamaki ga wata mata na bude kofa.

An dauki lokaci kafin na lura ba ta sanye da hijabi, kyakkyawan gajin ta mai tsawo ya kwanta a kafadunta.

"Ki cire wannan abin banzan daga jikinki," ita ce kalma ta farko da ta fara da ita ina shiga wurin, ta taimaka min na cire dan kwalina da sauran kayan jikina.

Da muka shiga can ciki, ta tattare min dogon domin tofi na tare da soke shi jikin gajeren wandon da ke jikina domin na ji dadin tafiya ba tare da na fadi ba.

Ta kai ni dakin da mata da 'yan mata da yawa suke, sanye da tufafi daban-daban. Wasu daga ciki sun sanya matsattsen wandon turawa, da bingilar riga, yawanci suna rufe wannan shiga da doguwar rigar Abaya da suke sanyawa a bainar jama'a.

Mun shafe daukacin rana cikin annashuwa, inda muke magana a kan halattacciyar soyayya, da kek, da yadda mace za ta dinga haihuwa kusan a kowacce shekara, idan ba ta son mijinta ya kara aure. Da kuma fatan 'ya'yan nan su kasance maza.

Sinadarin rinawa maza gashi

Ranar farko da aka fara yi min lalle a Somalia, matar da ta yi min ta kawo wani dan karamin akwati da aka yi shi da kwali. A cikinsa hoton wani mutum mai bakin gashi yana murmushi.

Wannan garin sinadarin rina gashi ne dan Indonesia. Ta zuba wannan garin cikin lallen da take kwabawa, ta juya shi sosai kana ta fara zanen adon fulawa a jikina.

Da lallen ya bushe, ya fito rangadadau, bakikkirin da yake burge matan Somalia, sai dai a gare ni lamarin ba haka yake ba. An dauki watanni kafin ya goge.

Daga nan kuma sai yankin Somaliland suka ayyana cin gashin kai. Abin da ya fi komai sanya ni farin ciki a Hargeisa, shi ne shiga mota tare da kawayena 'yan mata mu nufi wurin gyaran jiki na Bella Rosa Day Spa.

Wata mace 'yar Somalia da ta yi zaman Canada na shekara da shekaru domin tserewa yakin basasar da suka fuskanta, ta yanke shawarar bude wurin lokacin da ta dawo gida.

Dukkan ma'aikatan wurin 'yan Kenya ne. Yawancinsu sun shafe shekaru suna aikin gyaran jiki da kwalliyar mata a kasashen Larabawa.

Yawanci sun sha bakar wahala ta zahiri da badini, da cin zarafi a Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen yankin Gabas ta Tsakiya. Sun ce duk da sun yi nisa da gida kuma kudin da ake ba su babu yawa, sun gwammace zama a birnin Somali.

Na koyi darussa da dama a hirar da muke yi da matan idan mun hadu da su. Suna bankada sirrin zukatansu, ko na aure da kalubalen da suke fuskanta, da farin ciki, da wuya, da tsoro da kuma firgicin da sukan shiga saboda wasu dalilai.

A watannin da suka gabata, an dauko wannan batu a fannin siyasa lokacin da wata kwararriya a fannin kwalliya daga Birtaniya ta kai ziyara kasar.

'Yar asalin Eritrea ce, kuma tana da dan karamin wurin gyaran gashi a yankin Brixton.

Ta shaida min yadda kungiyarsu ta 'yan kasashen Habasha da Eritrea a kasashen waje ta samu rarrabuwar kawuna, sadaniyyar yakin da Habasha ke yi da 'yan tawayen Tigray, wanda su ma sojojin Eritrea suka shiga ciki domin taimakawa. Rabuwar kawuna kan kabilanci ta janyo kawayenta sun juya mata baya.

Tashin hankalin kera wukake

Bari mu koma kan batun mata masu wukake. Duk inda suke samo su, ba zan taba mantawa da wata mace 'yar Somalia da ita wukar da ta mallaka ba ta kankare lalle ba ce.

Lamarin ya faru bayan mun yi wata hira da ita a birnin Bur'ao. Ta na zaune a wata rumfar kwano, a kasuwar dabbobi, ta na juya abinci a tukunya. A rahoto na, na bayyana ta a talaka.

Lokacin da ta saurari rahotona, ran ta ya yi matukar baci. Don me zan kira ta da talaka?

Sai da ta nemo mutumin da ya kai ni kasuwar lokacin hada rahoton. A lokacin da ta gan shi, ta fito da wata sharbebeiyar wuka daga kugunta, ta yi masa barazanar za ta kashe ni har lahira idan ta kara gani na.

Abu na farko da ke zukatan wadanda suka san Somalia, shi ne kashe-kashe da shekaru 30 da aka kwashe ana yaki a kasar.

An kwatanta somalia da kasa mafi hatsari a duniya. Sakamakon fama da matsalar barayin teku da hare-haren 'yan kunar bakin wake.

Ban yi mamaki ba da matar ta ce duk inda ta kara gani na za ta kashe ni, saboda na bayyanata da talaka, saboda mutanen Somalia suna da alfahari da ji da kai.

Wannan alfahari da ji da kai ne ya ja hankali na har na fara zuwa gidan gyaran jiki, anna za ka ga samfurin gyaran gashi kala-kala, da zanen lalle mai ban sha'awa da daukar hankali, da kyakkyawan sura da suturar da suke sanyawa wadda hijabi ko abaya ke rufewa, da kyawawan fuskokinsu da suka sha adon janbaki da hoda da gazal, amma niqabi ya rufe su ruf.

Fata na shi ne kada Allah ya sake hada ni da matar nan ta kasuwar dabbobi, kuma kullum batun sharbebiyar wukar nan ke tada min hankali ba kadan ba. Ba kuma na fatan ganin yadda mata ke amfani da wuka domin kankare zanen lalle da sunan kwalliya.