Hanyoyi biyar na kauce wa kamuwa da cutuka daga abinci

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ware duk ranar 16 ga watan Oktoba a matsayin Ranar Abinci ta Duniya.

An ƙirƙiri wannan rana ne da manufar tunawa da muhimmancin abinci mai inganci ga rayuwa da kuma ƙalubalen da duniya ke fuskanta wajen samar da abinci mai kyau da lafiya ga kowa.

Wannan rana tana ba da dama ga ƙasashe su tunatar da jama'a muhimmancin tsafta, inganci, da amincin abinci da ake ci a kullum.

Albarkacin wannan rana, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta jaddada muhimmancin kiyaye tsafta wajen shiryawa da sarrafa abinci, tana mai cewa ana kamuwa da cututtuka 200 sakamakon cin abinci da ya gurɓace da ƙwayoyin cuta irin su bacteria, virus, ƙwayoyin halitta ko kuma sinadarai masu haɗari kamar da ke ɗauke da ɓaraguzan ƙarfe a ciki.

WHO ta bayyana hakan ne a sakon da ta wallafa a shafinta na X (Twitter) domin tunawa da Ranar Abinci ta Duniya.

Hukumar ta ce, cin abinci da ya gurɓace na iya janyo matsaloli daga ƙaramin rashin lafiya har zuwa mummunan ciwo ko ma mutuwa, musamman ga yara ƙanana da tsofaffi, da masu raunin garkuwar jiki.

WHO ta jaddada cewa ingancin abinci ba wai kawai ya ta'allaka ne ga yawan abinci ba, har da tsabtarsa da yadda ake sarrafa shi daga matakin noma da girbi da ajiya har zuwa lokacin da zai shiga bakin mutum da cikin jikinsa.

Domin rage haɗarin kamuwa da waɗannan cututtuka, WHO ta fitar da shawarwari guda biyar da waɗanda suke taimakawa wajen tabbatar da cewa abinci yana da tsafta kuma bai zama barazana ga lafiyar mai ci ba.

Tabbatar da tsafta a kodayause

WHO ta ce tsafta ita ce matakin farko wajen kare abinci daga gurɓacewa.

A riƙa wanke hannuwa da kyau kafin fara girki da bayan shiga banɗaki ko bayan taɓa dabbobi.

A kuma kula da tsabtace kayan girki da wurin da ake dafawa. Kwayoyin cuta suna iya yaɗuwa cikin sauri idan babu tsafta, saboda haka tsafta tana da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiya.

Ware dafaffan abinci da ɗanye

WHO ta ce yana da muhimmanci a raba abincin da ba a dafa ba da wanda aka dafa, a tabbatar an ajiye su a wurare daban-daban.

Abinci da ba a dafa ba kamar nama, kifi, da kaji za su iya kasancewa suna ɗauke da ƙwayoyin cuta waɗanda za su iya gurɓata abincin da aka dafa idan aka haɗa su.

Wannan mataki yana hana haddasa kamuwa da cuta.

Dafa abinci ya nuna sosai

Yawancin ƙwayoyin cuta da ke cikin abinci suna mutuwa ne idan an dafa abincin kyau kuma yadda ya kamata.

WHO ta ce a tabbatar nama da kifi da kaji sun dafu sosai, babu sassan da suka rage da ƙarfi.

Idan ana amfani da na'urar ɗumama abinci, microwave, a tabbatar abincin ya dafa duka sassa saboda wasu lokuta wutar microwave tana iya dafa ɓangarori kaɗan ne kawai.

Ajiye abinci a wurin da ya dace

WHO ta ce bai kamata a bar abinci da aka dafa a waje fiye da sa'o'i biyu ba.

Ta ce a ajiye abinci a cikin firiji idan ba za a ci nan da nan ba ko kuma wurin da bai da zafi domin ƙwayoyin cuta na iya yawaita cikin sauri a yanayin zafi.

Haka kuma, idan za a sake dumama abinci, a tabbatar an dumama shi sosai kafin ci.

Amfani da ruwa mai kyau wajen dafa abinci

...

Asalin hoton, Getty Images

Ruwa mai tsabta da kayan abinci masu kyau suna da muhimmanci. Kada a yi amfani da kayan da suka lalace ko ruwa mara tsafta wajen dafawa ko wanke kayan abinci.

A riƙa duba ƙarewar wa'adin ingancin kayan abinci kafin a saya.

Abincin da ka iya haddasa cututtuka
...

Asalin hoton, AFP

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa akwai wasu nau'in abinci da kan zama hanyar da ƙwayoyin cuta za sui shiga cikin jikin ɗan adam idan aka ci su ba tare da kulawa ba da kuma tsaftacesu ba. sun haɗa da

  • Abincin da aka sarrafa
  • Abinci da ke ɗauke da sinadarai masu haɗari
  • Madarar da ba a tafasa ba-
  • Kayan lambu da ganyayyaki
  • Shinkafa ko abincin da aka bari a waje na dogon lokaci
  • Naman da ba a dafa ba sosai
  • Kifin da ba tsaftace shi ba
  • Ƙwan da bai dahu ko soyu ba
....

Asalin hoton, Getty Images