Jarirai na mutuwa a Gaza saboda tsananin yunwa

.

Asalin hoton, family photo

Bayanan hoto, Hoton Jamal al-Kaferna, bayan an haife shi a watan Agustan shekara ta 2023
    • Marubuci, Amira Mhadhbi and Stephanie Hegarty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Jamal ya kasance yaron da ya fi kowanne kyau a asibitin, kamar yadda Abeer al-Kaferna ta bayyana yayin da ta ke kallon hotunansa a wayarta ta salula cikin alhini.

"Kalli yadda ya ke da kyau. Masoyina."

Abun da ta mallaka ke nan wanda ya shafi yaron. Jamal ya mutu ranar 18 ga watan Janairu.

Ya kwanta rashin lafiya ya na da wata uku a duniya.

Wata ɗaya da fara yaƙi, bayan iyayensa sun tsere daga sansanin ƴan gudun hijira sakamakon harin da Isra'ila ta kai ta sama.

An gano ya kamu da cuta bayan an yi masa gwaje-gwaje, daga nan aka ba shi magunguna amma bai samu sauƙi ba.

Zuwa farkon watan Disamban bara kashi 90 na iyalai a Arewacin Gaza na kwana ba tare da sun ci abinci ba kamar yadda Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Abeer ta ci gaba da ƙoƙarin shayar da jaririnta.

Saboda ƙarancin abinci mai gina jiki da rashin isasshen ruwan sha a jikinta, ba ta iya samar da isasshen nonon da jaririn zai sha. Abincin yara kuma ya na wahalar samuwa.

A watan Nuwamba, Jamal ya kasance cikin ƙoshin lafiya, nauyinsa kilo 7, daga baya sai ya fara ramewa cikin makonni ƙalilan sai nauyin jikinsa ya koma kilo 3.5.

Kakarsa mai suna Esmahan ta ce ''kafin watan Janairu kamanninsa sun koma kamar na ƙwarangwal.''

"Mun kasa samo masa madara," in ji mahaifinsa Mahmoud al-Kaferna. "Mun yi ƙoƙarin ba shi ruwa to amma ruwan a gurɓace ya ke."

.

Asalin hoton, family photo

Bayanan hoto, Nauyin Jamal kilo 7 ne lokacin da ya kai watanni uku kafin yaƙi ya fara tasiri
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An rubuta musu magunguna da za su ba shi to amma sun kasa samo magungunan. A ƙarshe an kwantar da shi a asibiti sai dai Jamal ya fara samun sauƙi suka bar asibitin.

"Asibitin sun ce babu sauran abun da za su iya yi masa kuma akwai yaran da suke buƙatar kulawarsu," cewar mahaifinsa.

A daren 17 ga watan Janairu, jikin Jamal ya fara rikicewa bayan ya fara tari wani farin ruwa na fitowa daga hancinsa.

"A guje muka koma asibitin ana ruwan bama-bamai cikin dare," in ji Mahmoud.

"Sun yi ƙoƙarin ceto ransa na tsawon minti 30 amma hakan bai yiwu ba, yunwa da rashin ruwa da kuma rashin magani a lokacin da ya kamata su ne suka kashe min ɗa”

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi ta kokarin ganin an samu karin tallafin magunguna da kayan jinya a Arewacin kasar. Uku daga cikin ayyukanta 16 ne Sojojin Isra'ila suka ba damar shiga cikin watan Janairu. A watan Fabarairu kuwa ba a bayar da izinin shiga ba.

Lokacin da Hukumar Lafiya ta duniya ta samu damar isa Arewacin Gaza a farkon watan Maris, tawagarta ta gano cewa yara 10 sun mutu sakamakon 'rashin abinci' a wani asibiti.

Ma'aikatar Lafiya ta Hamas ta ce yara 27 sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki da tsaftataccen ruwa a Gaza tun farko fara yaƙin, ana sa rai adadin zai ƙaru.

Kusan Falasɗinawa 300,000 ne suka rage a Arewacin Gaza.

Bayan sojin ruwan Isra'ila sun kai wa jerin gwanon motoci ɗauke da abinci na Majalisar Dinkin Duniya hari yayin da suke jiran a kammala bincike a wani shinge, Majalisar Dinkin Duniya ta rage yawan ayyukanta. Daga cikin 24 da suka shirya a watan Fabrairu dakarun Israila (IDF) sun amince da shida.

"Damar da Majalisar Dinkin Duniya ta samu ta shiga Arewa bai kamata ta zama abin tambaya ba," in ji Tess Ingram jami'in yaɗa labarai a Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya shafe mako guda a Gaza a watan Janairu ya na yunƙurin shiga Arewacin a lokuta da dama.

Isra'ila ta ce ba a iyakance kayan agajin da za a iya shigarwa ba, ta kuma ɗora alhakin rashin raba kayan agajin kan Majalisar Dinkin Duniya.

...

Ta bar mutanen Arewaci cikin ƙaranci da rashi.

Khalid ya fake a garin Jabalia tare da ƴaƴansa biyar da kuma danginsa 90. Ya shaida wa BBC cewa iyalansa na rayuwa ne ta hanyar cin ciyawa da abincin dabbobi.

"Kamar cin tsakuwa ne, bayan kammala cin abinci sai ya fara ganin jini a bayan gidansa.

Iyalansa sun yi sa'a sun samu buhun shinkafa cike da tsakuwa a ɓaraguzan wani gini, suna kuma dafa wata ciyawa da ta ke fitowa lambun gidajen da bom ya ragargaza.

Kasashen Labarawa da ƙasashen yamma su na saukar da abinci ta sama a Gaza. Khalid da iyalansa sun sake yin sa'a da suka kama ƙunshin shinkafa da nama da aka jefo daga sama.

Amma ƙungiyoyin agaji sun bayyana cewa wannan hanya ce mai tsada da kuma rashin inganci ta shigar da abinci yankin.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ƙunshin kayan agaji na sauka a Arewacin Gaza ranar 8 ga watan Maris

Aseel, wanda ya kasance a Arewacin Gaza ya shaida wa BBC cewar, da dama daga cikin kayan agajin na faɗawa cikin teku abun da ya sa mutane ke kaurewa da faɗa kafin su isa ga kayan agajin.

Ɗan'uwansa da ya tafi cibiyar da ake saukar da kayan tun da ƙarfe shida na safe bai samo komai ba sai gwangwanin kifi. Kashegari da ya sake komawa ya samo ruwa.

Wasu daga cikin kayan agajin sun sauka a yankunan da ke kusa da iyakar Isra'ila inda dakarun IDF suka gargadi mutane kar su je kusa.

"Kowa ya na gudu zuwa inda kayan agajin za su sauka, har daga ƙarshe mu haƙura mu koma ba tare da samun komai ba,'' in ji Aseel.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce saura ƙiris Falasɗinawa 576,000 su samu kawunansu a yanayin matsananciyar yunwa.

Ta kuma yi gargaɗin lokaci ya na ƙaratowa inda mutanen Arewaci za su faɗa cikin mummunan ƙarancin abinci da ruwa mai tsafta.

Kafin a ayyana yunwa, sai kashi 20 na al'umma sun yi fama da tsananin ƙarancin abinci, sannan an samu kashi 30 na yara ƙanana sun yi fama da rashin abinci mai gina jiki da kuma mutuwar mutum biyu cikin mutane 10,000 kullum saboda yunwa ko cutuka.

Tun a watan Disamban bara Majalisar Dinkin Duniya ta fara gargadi game da yunwa.

Kuma tun daga wancan lokaci yawan kayan agajin da ake shigarwa Gaza bai ƙaru ba.

A watan Janairu, aƙalla motocin dakon kayan abinci 150 na shiga Gaza kowacce rana, ƙalilan daga cikin motocin 500 ɗauke da kayan agaji da kayan sayarwa da suke tsallaka iyakoki kafin yaƙin.

A watan Fabarairu abin ya fi tsanani domin motocin kayan agaji 97 ne suke shiga Gaza kowace rana.

Bayani kan yawan tirelolin da ke shiga da abinci zuwa cikin Gaza a cikin watan Maris
Bayanan hoto, Bayani kan yawan tirelolin da ke shiga da abinci zuwa cikin Gaza a cikin watan Maris

Hatta a kudancin Gaza da ke samun kayan agajin da dama, yawancin iyalai na samun cin abinci sau ɗaya ne kawai a rana.

Kayan marmari da ƙwai da kuma nama suna wahalar samu kuma farashinsu ya ƙaru da kashi 10 kafin yaƙin.

"Ina buƙatar bashi daga ƙasashen ƙetare don in ciyar da iyalina," cewar Muhammad al-Najjar cikin fara'a, wanda yaƙin ya rabo daga Jabalia zuwa Rafah a Kudanci tare da mutane 11 daga cikin iyalinsa.

Nagham Mazid wata likitar sa kai ce a asibitin Al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza. Ta shaida yadda majinyata da dama suka mutu saboda rashin ruwa da ciwon ciki sakamakon yawaitar cin kayan gwangwani da aka sarrafa. An kuma samu wadanda suka kamu da cuta bayan cin gurɓataccen abinci.

Iyalan da Jariri Jamal ya bari, ba su da abinci a yanzu. Danginsa takwas da iyayensu na fama da yunwa.

Fatan su shi ne su yi sa'ar samun kayan agajin da ake jefowa daga sama ko ta teku ko kuma ta ƙasa.