Ko jagoran ƙungiyar Fatah, Marwan Barghouti zai iya zama shugaban Falasɗinawa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, By Manar Hafez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic, Amman
Shirin musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas ya ɓullo da sunan jagoran ƙungiyar Fatah, Marwan Al-Barghouti wanda ke zaman gidan yari. Ya ɓulla a matsayin wanda zai iya zama shugaban Falasɗinawa. Ƙungiyar Hamas ta jijirce cewa dole ne duk wata yarjejeniyar musayar fursunoni da za a ƙulla ta haɗa har da batun sakin sa, idan har ana so ta sako mutanen da ta yi garkuwa da su.
Osama Hamdan, wani jagoran Falasɗinawa ya shaida wa BBC Arabic cewa "A matsayin ƙungiya, mun amince da matsayar da muka cimma wadda ita ce aiwatar da musayar fursunonin ba tare da wani sharaɗi ba."
Hamdan ya ƙara da cewa, "Muna kallon wannan a matsayin wani aiki na ceton ƙasa. Dole ne duk wani fursuna da ya yi gwagwarmaya da sadaukarwa ga Falasɗinu ya ci gajiyar yarjejeniyar da aka cimma ba tare da nuna fifiko ba. Wannan ce matsayar da muka yarda da ita a yarjejeniyar Wafa al-Ahrar ta 2006."
Jaridar Ma'ariv ta Isra'ila ta ruwaito cewa an sauya wa Barghouti gidan yari daga Ofer da ake tsare da shi tun da farko zuwa wani gidan yari da ba a tabbatar ba, a cikin watan Fabarairu, bayan hukumomin gidan yarin Isra'ila sun bankaɗo bayanan da ke cewa al-Barghouti yana kitsa bore a gidan yarin da ke gaɓar yamma da kogin Jordan."

Asalin hoton, Getty Images
Ministan tsaron Isra'ila Itamar Ben-Gvir ya yi maraba da matakin canza wa Barghouti gidan yari, da kuma ɓoye shi a waje na musamman.
Sai dai hukumar kula da fursunonin Falasɗinawa ta yi alla-wadai da matakin da aka ɗauka kan Barghouti.
Kuma Isra'ila ta ƙi yarda ta saki Barghouti.
Ƙungiyar Fatah
Barghouti ya fara gwagwarmayar siyasa ne yana da shekara 15 a ƙungiyar Fatah, ƙarƙashin jagorancin marigayi Yasser Arafat.
Ya yi ƙarfi sosai a siyasance, kuma ya samar da goyon baya ga fafutukar neman kafa ƙasar Falasɗinu.

Asalin hoton, Getty Images
A 2002, ya rubuta a jaridar Washington post cewa "Ni da ƙungiyar Fatah da nake ciki muna nuna rashin amincewa da kai hari kan fararen hular Isra'ila maƙwabtanmu, ina da ƴancin kare kaina, da kare ƙasata da kuma neman ƴancinta,"
"Har yanzu ina fafutukar neman wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinu a matsayin ƙasashe masu ƴancin kansu, a bisa sharaɗin cewa Isra'ila ta janye daga yankin Falasɗinawa da ta mamaye tun a 1967...
“Gaskiyar magana ita ce mun gaji da ɗaukar laifi a kan abubuwan da Isra'ila ta aikata, bayan mu muna gwagwarmaya ne domin tabbatar da aiki da dokar ƙasa da ƙasa.”
Masu sharhi kan harkokin siysa sun shaida wa BBC Arabic cewa Barghouti, wanda ake tsare da shi a Isra'ila tun a 2002 zai iya zama zaɓin dukkan ɓangarori domin zama shugaban Falasdinawa, idan aka kai ga cimma yarjejeniya.
Ƙungiyar mayaƙa ta Al-Aqsa Martyrs' Brigades
An kama Barghouti ne a 2002 lokacin da Isra'ila ta zarge shi da ɗaukar nauyin wata ƙungiyar mayaƙa masu neman shahada, zargin da ya musanta.
Kungiyar ta kai munanan hare-hare a kan sojojin Isra'ila da kuma Yahudawa ƴan kama waje zauna.

Asalin hoton, Getty Images
An yanke wa Barghouti ɗaurin rai da rai har sau biyar, da kuma hukuncin shekara 40 a gidan yari saboda ɗaukar nauyin ƙungiyar.
Ya ƙi amincewa da ikon kotun Isra'ila a kan sa.
Matarsa, Fadwa, ta shaida wa BBC Arabic cewa "An gurfanar da shi ne saboda zaman sa jagora, ba don ya aikata wani laifi ba."
Fadwa, wadda lauya ce ta ce a yayin zaman kotun, Barghouti ya musanta zargin da ake masa.”

Asalin hoton, Getty Images
Ta ya ya Barghouti zai zama shugaban ƙasa?
Wakilin Hamas Osama Hamdan ya gamsu cewa ficen da Barghouti ya yi zai bashi damar ɗɗarewa shugabancin Falasɗinawa. "Babu shakka, mutum ɗan gwagwarmaya irin Marwan Barghouti yana da tarihin fafutuka kuma wasu na yi masa kallon jagora, kuma muna mutunta hakan, amma a matsayin ƙungiya ba mu tattauna ko cimma matsaya a kan hakan ba...
"Muna da yaƙinin cewa muradunmu a bayyane suke ƙarara: Falasɗinawa ne za su zaɓi wanda zai jagorance su ta hanyar kaɗa ƙuri'a kuma dole kowa ya mutunta wannan zaɓi."
A wani zaɓen jin ra'ayin jama'a da aka yi cikin watan Disamban 2023, alƙaluma sun nuna cewa ya fi sauran masu takara da shi yin suna.

Hamas ta daɗe tana gangamin neman a sako Barghouti daga gidan yari.
Wata sanarwa da shugaban ofishin hulɗa da ƙasashen Larabawa na Hamas Khalil al-Hayya ya fitar a shafin ƙungiyar na Telegram, a 2021 ta ce "Mun buƙaci a sanya jagora Marwan Barghouti da kuma sakatare janar na ƙungiyar kwato ƴancin Falasɗinawa Ahmed Saadat a cikin fursunonin da za a yi musayarsu."
Isra'ila ta ƙi yarda ta saki Barghouti a 2011, a lokacin da aka yi musayar fursunoni, inda har aka saki sojin Isra'ila Gilad Shalit da kuma jagoran Hamas, Yahya Sinwar.

Asalin hoton, Getty Images
Mai sharhi a kan siyasa, Oraib Al-Rantawi ya ce yiwuwar sakin Barghouti tana da alaƙa da tattaunawar musayar fursunoni da ke gudana tsakanin Hamas da Isra'ila.
Hamdan ya ce Isra'ila ta ƙi amincewa da yarjejeniyar.
Musayar fursunoni
Al-Rantawi ya shaida wa BBC Arabic cewa sakin Barghouti ya danganta ga irin sadaukarwar da Isra'ila za ta iya yi domin karɓo ƴan ƙasarta da Hamas ta yi garkuwa da su.
Sai dai kuma, ya yi amanna cewa ''Matsin lamba daga Amurka da masu faɗa a jin cikin gida na Isra'ila zai tilasta wa Netanyahu ya ƙi amincewa da wannan buƙata, sai dai yana iya bayar da fifiko ga yarjejeniyar musayar mutanen da aka yi garkuwa da su.''
Benjamin Netanyahu ya bayyana buƙatar Hamas ta sakin Falasɗinawa da yawa a matsayin son rai.

Asalin hoton, Getty Images
Yiwuwar sakinshi daga yari
A 2009, Barghouti ya yi tsokaci a yiwuwar takararsa, inda ya ce "Idan aka cimma matsayar sasanci da kuma gudanar da zaɓe, zan ɗauki matakin da ya kamata."
Duk da cewa ana tsare da shi, a 2021 Barghouti ya tsaya takarar shugaban ƙasa. Shugaba mai ci, Mahmoud Abbas ya soke zaɓen, yana mai kafa hujja da rashin amincewa a bai wa kudancin Ƙudus ƴanci daga Isr'ila a matsayin dalili.
Amma Al-Rantawi ya ce, "Ƴan gwagwarmayar za su yi tsayin daka a kan buƙatarsu ta sakin Marwan da muƙarrabansa."

Asalin hoton, Getty Images
Zaɓin samar da ƙasashe biyu
A watan Janairu marubucin Isra'ila, Gershon Baskin ya rubuta cewa "Wani jagoran Falasɗinawa mai ƙarfin ikon haɗa kan yankin na nan tafe. Ba wani bane illa Barghouti."
Baskin ya yi nuni da cewa har yanzu Barghouti yana goyon bayan kafa ƙasashe biyu masu ƴancin kansu wajen magance matsalar.
Amma masanin hulɗar diflomasiyya ɗan Amurka, Gina Winstanley, ya shaida wa BBC Arabic cewa "Gwamnatin Isra'ila ta bayyana ƙarara cewa ba ta da aniyar goyon bayan kafa ƙasashe biyu don warware dambarwar. Kuma ba ƙaramin aiki bane neman shawo kanta."
Winstanley ya ƙara da cewa koda an saki Barghouti, babu tabbacin cimma nasarar kafa ƙasashen biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Me ya sa ake ganin Barghouti a matsayin mafita?
Tarek Fahmi, na cibiyar nazarin harkokin gabas ta tsakiya ya ce da wuya Isra'ila ta amince da sakin Barghouti.
Ya shaida wa BBC cewa "Marwan yana da tarihin gwagwarmaya, amma Isra'ila ba za ta amince da sakinsa har ya nemi zama shugaban Falasɗinawa ba. Sai dai ta goyo bayan wasu ƴan takarar.

Asalin hoton, Getty Images
Al-Rantawi ya yi amanna cewa sakin Barghouti zai zamo kamar an cika muradin Hamas ne. Ya ce zai sake kafa ƙungiyar Fatah, da farfaɗo da ƙungiyar gwagwarmayar neman ƴancin Falasɗinawa da samar da hanyoyin sasanci.
Amma Barghouti zai iya takarar shugabancin Falasɗinawa daga gidan yari?
Al-Rantawi ya ce zaɓin shi ne Barghouti zai karɓi shugabanci daga gidan yari, ta yadda mataimakinsa zai zamo shugaba mai tafiyar da gwamnati. Daga baya kuma a tilasta wa Isra'ila har ta saki Barghoutti.
A gefe guda kuma, Meir Masri na ganin cewa abu ne mai wuyar gaske Barghouti ya hau karagar mulki daga gidan yari.
Hukumomin Falasɗinu dai ba su amince sun yi tsokaci a kan batun ba kawo yanzu.











