Isra'ila ta hana shigar da abinci Gaza - MDD

Asalin hoton, Reuters
Hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya ta ce dakarun Isra’ila, sun hana yunkurinta na farko a cikin mako biyu na kai kayan agaji na abinci zuwa arewacin Gaza, inda ake matukar bukatar abincin.
Manyan motoci 14 ne dauke da kayan abincin suka nufi arewacin Gaza, da nufin komawa kai agajin, inda hukumar ta ce mutum 500,000 na cikin yunwa.
Sai dai hukumar ta ce dakarun Isra’ila, sun hana motocin shiga bayan sun shafe sa’a uku suna jira a wajen shingen binciken ababan hawa na Wadi Gaza suka kuma umarce su da su koma.
Wannan ne ya sa suka dauki wata hanyar ta daban, daga can kuma tarin mutane da ke cikin wahala da bukata suka wawashe kayan da suka kai tan 200.
Hukumar ta ce ta hanyar kasa ne kawai za ta iya kai kayan abinci mai yawa haka, domin kauce wa fadawar jama’a cikin já’ibar yunwa a arewacin Gaza, tare da yin kira da a samar da karin hanyoyin shiga ta kasa da kuma ta ruwa.
Tun da farko kafin sojojin Isra’ilar su hana kai kayan, hukumar samar da abincin ta majalisar dinkin duniya tare da taimakon sojojin sama na Jordan, ta jefa wa kusan mutum 20,000 kayan abinci, tan shida ta sama a arewacin Gaza.
Jefa kayan ta sama shi ne zabi na karshe na kai kayan tallafin, kuma hakan ba zai iya magance matsalar yunwa da ake famada ita ba a can.
Hukumar ta ce suna bukatar hanyoyin shiga arewacin Gaza, domin kai wadatattun kayan abincin da ake matukar bukata.
Yunwa ta kai matakin masifa a yankin na arewacin Gaza, inda yara ke mutuwa saboda cutuka masu nasaba da yunwa, wasu kuma sun kamu da tamowa.
Ana bukatar dakatar da bude wuta cikin gaggawa a Gaza, domin gudanar da aiki irin wannan.
Ta hakan ne ma’aikatan hukumar da masu hadin gwiwa da su za su iya gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali ba tare da wani hadari ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi Isra'ila cewa ba ta da hujjar hana a kai kayan agaji Gaza.
Ya fada wa 'yan jarida cewa za a shiga yanayi mai hadarin gaske idan aka gagara cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas kafin a soma azumin watan Ramadana.
Mista Biden ya zargi Hamas da haifar da matsala a kokarin cimma yarjejeniyar sulhu.
Hare-haren Isra'ila a Gaza sun haddasa karancin abinci da ruwan sha da magunguna.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce sama da marassa lafiya 8,000 a Gaza -- akasarinsu dauke da munanan raunuka sakamakon hare-haren Isra'ila -- na bukatar a kwashe su daga yankin a cikin gaggawa.
A ranar Alhamis da ta wuce aka kashe Falasdinawa sama da 100 a gefen birnin Gaza, lokacin da tarin jama’a suka yi cincirundo a wajen wasu jerin manyan motoci da ke dauke da kayan tallafi a gaban, manyan motocin yaki na Isra’ila.
Sojojin Isra'ila sun bude wa mutanen wuta, bisa abin da suka ce mutanen sun kasance barazana a garesu.











