Yadda ake kashe ma'aikatan lafiya masu aikin ceton rai a Gaza

Yadda abokin Mahmoud ke ƙoƙarin rarrashin sa a lokacin da ya gano gawar mahaifinsa bayan kashe shi

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Yadda abokin Mahmoud ke ƙoƙarin rarrashin sa a lokacin da ya gano gawar mahaifinsa bayan kashe shi
    • Marubuci, Ethar Shalaby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Arabic

Gargaɗi: Wannan rahoto na ƙunshe da bayanai na raunuka da mace-mace.

Labarin ya zo ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana. Ma'aikacin lafiya Mahmoud al-Masry tare da sauran abokan aikinsa na jiran lokacin da za su sake komawa kan aiki a asibitin al-Awda da ke arewacin Gaza.

Sai aka sanar cewa wani makami ya faɗa kan motar ɗaukar marasa lafiya mai lamba 5-15, wadda ke ɗauke da mahaifin Mahmoud da abokan aikinsa. Shi ma ma'aikacin lafiya ne.

Sai Mahmoud da sauran abokan aikinsa suka garzaya domin ganin abin da ya faru.

Lokacin da suka isa inda motar take, sai suka iske motar ta yi kaca-kaca a gefen hanya. Mahmoud ya matsa kusa domin dubawa da kyau, sai ya iske duk mutanen da ke cikin motar "sun ƙone ƙurmus."

Wani rahoto na musamman da BBC ta tattara na ayyukan ma'aikatan lafiya a watan farko bayan ɓarkewar yaƙin, ya haɗa da halin da Mahmoud ya tsinci kansa a lokacin da ya gane cewa mahaifinsa, Yosri da mutane biyu da ke tare da shi sun rasa rayukansu.

Mahmoud ya ce "Babu sauran wani abu da za a iya ganewa a fuskarsa."

Masu aikin ceto sun iske motar kai agaji wadda hari ya lalata sannan an kashe dukkanin jami'ai uku da ke cikin ta

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Masu aikin ceto sun iske motar kai agaji wadda hari ya lalata sannan an kashe dukkanin jami'ai uku da ke cikin ta

Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Oktoba, kwana biyar bayan ɓarkewar yaƙin.

An nannaɗe gawar Yosri Al-Masry cikin likkafani tare da hular kwanon da ke kansa wadda ta yi caɓa-caɓa da jini.

A lokacin binne mahaifin nasa, Mahmoud ya durƙusa gaban gawar mahaifin nasa yana sharɓar kuka tare da girgiza kansa, yayin da sauran abokan aikinsa ke zagaye da shi.

Ɗan jarida a yankin Gaza. Feras Al Ajrami ne ya ɗauki bidiyon abubuwan da suka faru da ma'aikatan lafiya a yankin Gaza a wani rahoto na musamman da ya haɗa mai taken 'Gaza 101: Ceton gaggawa.'

Bayan kashe mahaifin nasa, Mahmoud, mai shekara 29 a duniya wanda ke da yara uku, ya ɗauki hutun makwanni daga bakin aiki.

Sai dai ya ce duk da irin takaicin da ya shiga, ya ji cewa yana so ya koma bakin aiki.

Ya ce "Babu abin da ke a cikin raina face na yi wa al'ummar Falasɗinawa hidima."

Ya sanya hoton mahaifinsa a wayarsa "domin na rika ganin shi a kodayaushe, dare da rana".

Mahaifin Mahmoud, Yosri Al-Masry a bakin aiki kafin a kashe shi.

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Mahaifin Mahmoud, Yosri Al-Masry a bakin aiki kafin a kashe shi.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mahmoud na tare da mahaifinsa, awanni kaɗan kafin ya haɗu da ajalinsa.

Ya buƙaci Mahmoud ya haɗa masa shayi, wanda ya sha kafin a kira shi domin fita aiki da tsakar rana.

Kwana biyu kafin rasuwar mahaifinsa, shi kansa Mahmoud ya ji rauni inda aka kai shi asibiti yayin da wani tartsarin makamin da ya fashe ya shige masa ta gefen wuya da bayansa.

Mahmoud ya ce a lokacin da ya samu rauni mahaifin nasa "ya yi kuka tare da nuna damuwa."

Sai dai a yanzu Mahmooud babu abin da ke zuwa masa a zuciyarsa da zarar ya tuna da mahaifinsa sai abin da ya gani, na lalatacciyar mota a gefen titi.

Ya ce "A duk lokacin da nake ni kaɗai, abin yana zuwa min a rai, Ina ta sauri zuwa wurin motar, na kaɗu sosai a lokacin da na ga gwarasa ta yi kaca-kaca.

Mahmoud ya kasance yana aikin lafiya tsawon shekara bakwai, inda a baya yake aiki a garin Jabalia da ke arewacin Gaza a matsayin jami'in ƙungiyar Red Crescent ta yankin Falaɗinawa.

Rahoton na musamman ya riƙa bibiyar motocin ɗaukar marasa lafiya daga wannan cibiyar na tsawon fiye da wata ɗaya bayan ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da Hamas ta ƙaddamar da harin da ya yi sanadin mutuwar ƴan Isra'ila 1,200 da kuma yin garkuwa da kimanin 250 - wanda daga lokacin ne Isra'ila ta ƙaddamar da nata harin.

Rami ya ce ganin yara mata uku kwance a mace ya tuna masa da nasa yaran mata guda uku

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Rami ya ce ganin yara mata uku kwance a mace ya tuna masa da nasa yaran mata guda uku

Mazauna Gaza sama da 10,000 ne aka kashe a watan farko bayan ɓarkewar yaƙin, kamar yadda ma'aikatar lafiya da ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana, kuma hukumar ta ce yawan mutanen da aka kashe ya karu zuwa sama da 28,000 tun daga wancan lokacin.

Ɗaukar bidiyon yadda ma'aikata lafiya ke ratsa hanyoyin da ke cike da gawawwakin mutane da ƙananan yara waɗanda aka raunata ya nuna yadda a lokuta da dama yanayi na mutuntaka kan shiga cikin ayyukansu.

Ya nuna irin matsanancin damuwar da suke faɗawa musamman a lokutan da suke ta'ammuli da gawawwakin ƙananan yara.

A kwanakin farko-farko bayan ɓarkewar faɗan, wani ma'aikacin lafiya, Rami Khamis ya durƙusa gefen motarsa ta ɗaukar marasa lafiya yana sharɓar kuka.

Ya ce an kira shi domin kai ɗauki a wani gida wanda ya rufta kan mata da yara.

Lokacin da ya shiga wani ɗaki sai ya iske yara mata uku suna kwance a mace, sai abin ya tuna masa da yaransa mata uku.

Ya ce: Na kasa jurewa, sai na fashe da kuka a lokacin da na gan su."

A wancan lokacin hotunansa sun karaɗe shafukan intanet.

A wajen ƙarshen watan Oktoba, ɗaya daga cikin ma'aikatan lafiyar, Alaa Al-Halaby ya samu kiran waya daga wani ɗan'uwansa.

Wani harin sama da Isra'ila ta kai ya faɗa kan gidan kawunsa cikin kwana biyu da suka gabata, amma har ya zuwa lokacin da aka kira shi gawawwakin wasu da suka rasa rayukansu na a ƙarƙashin ginin.

An zaro gawar ɗan'uwansa daga cikin ɓaraguzai, inda yake da aniyar ɗaukar sa zuwa asibiti.

A daidai lokacin da yake ƙoƙarin wucewa sai ya ci karo da wasu gungun masu ceto da suke ƙoƙarin kawar da tulin ginin kankare, ɗaya daga cikin ƴan'uwansa ya shaida masa cewa: "Akwai wata yarinya da gini ya danne a nan, ko dai dukkanin jikinta ne ko kuma wani ɓangare na jikinta."

Sai ya tsaya, ya ja dogon numfashi, ya ce musu: "Rabin gangar jikin yarinyar na can haka, ku haɗa su wuri ɗaya."

Duk a rana guda, Alaa ya je wani gida inda aka zaro yara biyar waɗanda suka ƙone ƙurmus. An ɗauki uku daga cikin su aka saka a motarsa ta ɗaukar marasa lafiya.

Ya ce "Abu na farko da ke zuwa min a rai idan na ɗauki gawar yaro shi ne yarana."

"Hakan na sanyawa...", ya yi ƙoƙarin ci gaba da bayani amma sai aka kira shi domin kai ɗaukin gaggawa a wani wurin.

Alaa, sanye da takunkumin kariya lokacin da yake taimakawa domin kwashe gawawwaki a gidan kawunsa ranar 27 ga watan Oktoba 2023

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Alaa, sanye da takunkumin kariya lokacin da yake taimakawa domin kwashe gawawwaki a gidan kawunsa ranar 27 ga watan Oktoba 2023

Mako ɗaya bayan ɓarkewar yaƙin sai Isra'ila ta umarci fararen hula mazauuna arewacin Gaza su yi hijira zuwa kudancin yankin domin kada yaƙin ya shafe su.

Saboda haka da yawa daga cikin iyalan ma'aikatan lafiyar sun yi hijira zuwa kudancin, inda suka bar ma'aikatan lafiya a arewacin.

Sun riƙa jin halin da iyalan nasu ke ciki ne ta hanyar waya, a lokacin da suka samu damar hakan ko kuma ta hanyar wayar aiki ta ƙungiyar Red Crescent a yankin Falasɗinawa.

Rami ya kwashe shekara 20 yana aikin lafiya, amma ya ce ƴaƴansa mata kan maƙalƙale shi a duk lokacin da aka samu ɓarkewar faɗa a Gaza, a ƙoƙarin su na roƙon shi kada ya je wurin aiki.

Alaa ya ce shi ma yaransa sukan fashe da kuka a duk lokacin da zai tafi aiki, ya ce yakan riƙa yin addu'a a lokacin da yake tuƙa mota yayin gudanar da aiki, yana roƙon "Allah Ya mayar da mu gida lafiya."

Hatsarin da ma'aikatan ƙungiyar Red Crescent a yankin Falasɗinawa ke fuskanta abu ne a bayyane ƙarara.

A wani lokacin, yayin da wasu daga cikin ma'aikatan lafiyan ke jiran a kira su a bakin asibitin al-Awda, sai aka samu wata fashewa mai ƙarfi, wadda ta sa suka gudu domin neman mafaka.

Motocin ɗaukar marasa lafiya biyu ne aka lalata a lokacin. Ɗaya daga cikin ma'aikatan ya ce sojojin Isra'ila sun yi aniyar kai hari ne kan wani gida da ke kusa da asibitin.

Isra'ila ta ce ba ta kai hari a yankin ba, sai dai ta kai harin ne a kan "wani wurin sojoji da ke da nisan fiye da mita 100 daga wurin."

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent a yankin Falasɗinawa ta ce an kashe jami'anta 14 a yankin Gaza tun bayan ɓarkewar yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba.

Mai magana da yawun ƙungiyar, Nebal Farsakh ta ce "Jami'anmu na samun kansu cikin hatsari a duk wani hari da aka kai," inda ta lissafo lokuta da dama da aka kashe ma'aikatanta a lokacin irin waɗannan hare-hare.

Ta ce "Ana kai wa jami'anmu hari a lokacin da suke kan aiki, kuma yanayin da muke aiki a ciki na cike da hatsari da ban-tsoro."

Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent a yankin Falaɗinawa ƙungiya ce mai zaman kanta, wadda ɗaya ce daga cikin ƙungiyoyin da ke ƙarƙashin Babbar ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya (IFRC).

A ƙarƙashin dokar yaƙi, ana la'akari da tambarin ƙungiyar a matsayin ta masu kai ɗaukin ceton rai, waɗanda suke samun kariya, kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar Geneva.

Yadda wani mai aikin agaji ya ɗauko wata yarinya

Asalin hoton, Feras Al Ajrami

Bayanan hoto, Yadda wani mai aikin agaji ya ɗauko wata yarinya

Ms Farsakh ta ce akwai tambarin ƙungiyar a sama da kuma gefen motocin ƙungiyar, ciki har da motar ɗaukan marasa lafiya mai lamba 5-15 wadda a cikinta ne aka kashe mahaifin Mahmoud.

Ƙungiyar ta PRCS ta yi amannar cewa a kan motocinta "sojojin Isra'ila suka kai hari kai-tsaye."

Ta ce "Babu yadda za a yi a ce duk da ƙwarewar fasaha da Isra'ila ke amfani da shi a ce ba ta ga tambarin ba."

Sai dai hukumar sojin Isra'ila (IDF) ta ce "ba ta kai hari kan ma'aikatan lafiya, ciki har da ma'aikatan ƙungiyar PRCS da gangan."

A game da harin da aka kai kan motar ɗaukan marasa lafiya mai lamba 5-15, IDF ta ce ta kai hari ne "kan wata cibiyar soji wadda ba ta da nisa daga inda motar take", amma ba "motar ta kai wa hari ba."

Ta ƙara da cewa "hare-haren da ake kai wa ta sama ba za su iya lalata motar ba kamar yadda aka bayyana."

Isra'ila ta ce hare-harenta tana kai su ne a kan mayaƙan Hamas, kuma sojojinta "na ɗaukan matakan da za su yiwu wajen hana hare-haren shafar fararen hula."

Rundunar sojin Isra'ila ta kuma zargi Hamas da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa tare kuma da ɓoyewa a cibiyoyin kiwon lafiya.

Isra'ilar ta wallafa wasu hotuna na wasu hanyoyin ƙarƙashin ƙasa waɗanda ta ce ta gano a kusa ko kuma ƙarƙashin asibitoci, sannan kuma ta ce sojojinta sun gano makamai a cikin asibitoci.

Haka nan kuma sojojin Isra'ila sun zargi Hamas da yin amfani da motocin ɗaukar marasa lafiya - duk da ba su ambaci ƙungiyar PRCS ba - wajen safarar mayaƙa da kuma makamai.

Ƙungiyar PRCS ta ce motocinta 16 ne aka lalata tun bayan ɓarkewar rikicin a ranar 7 ga watan Oktoba - kuma jimilla, an lalata motocinta na ɗaukar marasa lafiya guda 59 a faɗin Gaza.

Farsakh ta ce mayaƙan Falasɗinawa ba su "taɓa" tsoma baki cikin ayyukan kungiyar ba.

"Ta ce "aikinmu shi ne mu samar da tallafin jinƙai ga al'umma."

An raunata Mahmoud Al-Masry lokacin da ɓurɓushin makami ya soke shi a wuya da baya kwana biyu kafin kashe mahaifinsa

Asalin hoton, Feras Al Ajramy

Bayanan hoto, An raunata Mahmoud Al-Masry lokacin da ɓurɓushin makami ya soke shi a wuya da baya kwana biyu kafin kashe mahaifinsa

Ta ƙara da cewa "Manufarmu iri ɗaya ce da ta ƙungiyar International Red Cross da kuma International Red Crescent, waɗanda suka ƙunshi tsayawa kan gaskiya da kuma cin gashin kai, babu wani da ke yi mana katsalandan cikin aiki."

A cikin watan Disamba ƙungiyar PRCS ta rage yawan aikin da take yi a arewacin Gaza bayan da ta ce sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan cibiyarta da ke a Jabalia.

Dakarun Isra'ila sun musanta buɗe wuta a kan, ko kuma a cikin asibiti, inda ta ce "ta gano wani wararen tsare mutane na Hamas a wani asibitin ƙungiyar Red Crescent, kuma wasu daga cikin su na sanye da kaya mai tambarin ƙungiyar."

Farsakh ta ce :babu ƙamshin gaskiya" kan labarin, ta kuma ce babu komai a asibitin sai motocin ɗaukar marasa lafiya da ma'aikatan lafiya da masu aikin sa-kai da mutanen da suka samu rauni da kuma mutanen da aka tarwatsa daga gidajensu.

Alaa da Rami da kuma Mahmoud duk sun yi hijira zuwa kudancin Gaza inda suke aiki a matsayin ma'aikatan lafiya a birnin Khan Younis - duk da dai Rami ya sake komawa arewacin Gaza cikin kwanakin nan.

A ƙarshe-ƙarshen watan Janairu lokacin da faɗa ya ƙazance a Khan Younis, Mahmoud ya mayar da matarsa da ƴaƴansa - Mohamed mai shekara 6, Leila ƴar shekara 5 da Layan mai shekara 3 zuwa al-Mawasi, wani sansani da a baya Isra'ila ta ayyana a matsayin tudun mun-tsira, inda suke rayuwa cikin tanti.

Wata huɗu bayan rasuwar mahaifinsa, Mahmoud ya ce guyawunsa ba su yi sanyi ba game da ƙudurinsa na tallafa wa marasa lafiya da waɗanda aka raunata.

Ya ce: "Wannan wasiyya ce daga mahaifina kuma wajibi ne na ci gaba da aiwatarwa."