Shawarwari 15 da ƴan sanda suka bayar don kare kai a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayar da umarnin daukar matakan tsaro domin kare makarantu da asibitoci da ma'aikatan lafiya da muhimman kayayyakin jin dadin jama'a a fadin kasar.
Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan nan na Agusta, 2022, kan yanayin tsaron kasar baki daya.
Shugaban 'yan-sandan ya kuma umarci jami'an da su rika gudanar da sintiri da bincike akai-akai domin rage yawan aikata miyagun laifuka a Najeriya.
A kan hakan ne hukumar 'yan sanda ta roki al'ummar kasar da su yi hakuri da yadda za su rika ganin jami'ansu a wurare daban-daban da dama suna kuma tsayar da su domin gudanar da bincike.
Dangane da hakan hukumar 'yan-sandan ta Najeriya ta fitar da wasu shawarwari ko matakai 15 da jama'a za su iya bi domin kare kai daga matsalolin tsaro.
Matakan kariya
Shawara ta 1. Kada ka yi manna takarda ko wata alama da za ta nuna aikinka ko wurin da kake aiki, musamman idan aikin naka babba ne.
Shawara ta 2. Kada ta sa hoton danta ko 'ya'yanka sanye da kayan makaranta ko bajon makarantarsu a shafukan intanet. Ku kare 'ya'yanku.
Shawara ta 3. Idan ka je wajen wani taron biki kada ka rika likin kudi, maimakon haka ka sa kudin a wata takarda ko ambulan ka ba makadan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shawara ta 4. Kada ka je na'urar cirar kudi ta ATM ka dauki kudi masu yawan gaske ko ma ka nemi karar da kudin da ke ciki. Ba sai ka sa Naira dubu 50 ba a 'yar karamar jakar za ka nuna kai mai kudi ne.
Shawara ta 5. A kodayaushe ka goge sakon da banki ke turo maka ta waya na hada-hadarka ta banki. Za ka iya haddace bayanin yawan kudin da suka rage maka a asusunka ba sai ka bari a wayarka ba. Ka yaga rasitinka na POS ko ATM ka jefar.
Shawara ta 6. Kada ka bi wajen da yake da duhu ko ba mutane sosai a lokacin da kake motsa jiki. Idan har za ka yi haka to ya kasance kana tare da wani da ka yarda da shi.
Shawara ta 7. Kodayaushe ka tabbatar da ka rufe kofarka ko da za ka fita ne kawai ka kashe jannaretonka.
Shawara ta 8. Kada ka taba sanyawa ko barin katinka na wurin aiki rataye a wuyanka idan ka fita daga wurin aiki. Ba wanda ke bukatar sanin inda kake aiki.
Shawara ta 9. ka rika sanar da iyayenka ko iyalinka duk inda kake a kodayaushe.
Shawara ta 10. Kada ka aiki yaro shi kadai waje. Ka tabbatar ka hada shi da wani babba.
Shawara ta 11. Kada ka rika nuna kanka cewa ki babban mutum ne ko mai kudi ne a unguwarku. Kana rabon manyan kudi ko wasu abubuwa.
Shawara ta 12. Ka rika yi a cikin sirri ya fi.
Shawara ta 13. Kada ka rika dadewa bayan an tashi daga aiki a ofis ko wurin aiki har ka yi dare. Za ka iya barin aikin da ya rage maka nan gaba ko ma a gida.
Shawara ta 14. Har kullum ka rika kawo matakan kariya ko yadda za ka kauce wa wata matsala a duk abin da za ka yi ko inda za ka je.
Shawara ta 15. Ka san irin abubuwan da za ka sanya game da kanka a shafukan intanet.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Matsalar tsaro a Najeriya
A yanzu dai jama'a na cikin wani mawuyacin hali na matsalar tsaro a Najeriya, inda ake fama da sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa da kuma kisan da barayin daji kan yi.
Duk da cewa wannan matsala kusan ta zama ruwan-dare a kasar to amma ana ganin ta fi kamari a yankin arewa maso yammacin kasar inda garuruwa da dama suka kasance kusan kufai a jihohin Naija da Katsina da Kaduna.











