Yadda mutane ke neman taimakon kuɗi don biyan fansar ƴan uwansu da aka sace

Asalin hoton, AFP
Daga Imam Saleh
Matsalar satar mutane don neman fansa na ƙara zama tamkar tsinkewar carbi a Najeriya.
Sai dai wani baƙon abu shi ne yadda waɗanda aka sace ƴan uwansu ke gwammacewa su nemi tallafin kudi daga jama'ar gari, don tattarawa su biya kudin fansa don sakin waɗanda aka sace.
Masana dai na ganin a ƙa'ida gwamnati ce ya kamata a ce ta hana idonta bacci, don ganin ta ceto duk wani ɗan Najeriya da aka sace, tun da gazawarta wajen sauke nauyin kare shi ce ta kai ga sace shi.
A lokuta da dama mahukunta musamman a ɓangaren tsaro na hana jama'a biyan fansa don ceto ƴan uwansu, a cewarsu, babu abin da hakan zai haifar, illa ƙara wa Borno dawaki.
A watannin baya-bayan nan ma sai da Majalisar Dokokin Najeriyar ta zartar da wata doka, ta hukunta duk wanda aka samu da biyan kudin fansa don ceto wani ɗan uwansa daga wajen masu garkuwa.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Me ya sa wasu suka gwammace su nemi taimako?

Idan ba don dole ba, mutane da dama na jin nauyin neman taimakon jama'a musamman ta fuskar abin da ya shafi kuɗi, sai dai ga waɗanda aka sace ƴan uwansu, a yanzu wannan kunyar ta kau.
Injiniya Magaji Tukur Sambo, shi ne shugaban wani asusu da aka kafa musamman da zummar kuɓutar da wasu mutane biyu, dukkansu almajiran Shehu Ibrahim Nyass, da ke cikin mutanen da aka sace a jirgin ƙasan nan na Abuja zuwa Kaduna.
Ya shaida wa BBC Hausa cewa a yanzu, ba su da wani zaɓi da ya wuce yin hakan, domin suna zargin sai da aka biya kudin fansa kafin sakin wasu daga cikin fasinjojin jirgin da aka saki a baya-bayan nan.
''Muna tarawa ne domin idan an tuntuɓe mu mu biya, don a yanzu ba mu da abin da za mu bayar idan aka buƙaci kudi daga gare mu'' in ji shi.
Ya ƙara da cewa sun yanke shawarar kafa asusun ne bayan ɓullar bidiyon baya-bayan nan da ya nuna yadda ake dukan ƴan uwan nasu a inda ake tsare da su.
''Ba haka aka so ba''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yawan wadanda ke neman taimakon kudi don kubutar da 'yan uwansu na cewa suna yin hakan ne don kawai babu yadda za su yi.
Injiniya Magaji Tukur Sambo, ya ce tun farko ba haka suka so ba, sun so a ce akwai wani tartibin shirin da ake yi daga bangaren gwamnati, wanda za sa su samu nutsuwa.
A cewarsa ''Ba a ko tuntubarmu, ba a zama da mu a fada mana ga halin da ake ciki game da binciken da ake cewa ana yi da irin nasarar da ake samu lokaci zuwa lokaci, shi yasa muke ganin an bar lamarin ne haka kara zube''.
''Tun da aka sace 'yan uwanmu ba bu wanda ya tuntube mu, ba a ce mana komai ba, ba mu san halin da 'yan uwanmu ke ciki ba, abubuwan da muke ganin na faruwa na da matukar tayar da hankali'' in ji shi.
Ya kara da cewa abun da suka sa a gaba a kudin da suke tarawa a yanzu shi ne ganin sun kubutar da 'yan uwansu.
Amma idan har kudin da suke tarawa ya kai yadda watakila 'yan bindigar za su bukata, za su biya don ganin sun ceto dukkan mutanen da suka rage a hannunsu.
Wasu iyali mai mutum shida
Ko a Instagram, an ga yadda a kwanakin nan wasu mutane ke ta yin shelar yadda za a haa kuaen da za a ceto wani iyali, miji da mata da yaransu huɗu.
Su ma waɗannan iyalai an sace su ne a cikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da aka kai wa hari a watan Maris.
Kuma a ƙalla kamar yadda masu nemar musu taimakon suka ce, maharan na neman naira miliyan 100 kan kowane mutum ɗaya.
Hakan na nufin ana buƙatar naira miliyan 600 don ceto wannan iyali.
Sai dai babu tabbas kan ko masu taya iyalin neman taimakon danginsu ne ko kuwa ƴan ƙasa ne da ke neman su ga an kuɓutar da su kawai.
Yadda matsalar ta zama ruwan dare
Yanzu dai kusan a iya cewa yawancin 'yan Najeriya sun saba da labaran satar mutane, don kuwa ba a shafe kwana guda ba tare da ka ji an sace mutane a wasu wuraren ba, musamman arewa maso yammacin kasar, inda matsalar ta fi kamari.
Mahukunta na cewa suna iya bakin kokarinsu wajen shawo kan matsalar, amma mutane da dama na ganin cewa har yanzu gafara sa kawai ake ji ba tare da an ga ko da kaho ba.
Masharhanta na yawan kalubalantar gwamnati a kan yadda take hana mutane biyan fansa ba tare da ta samar da wani kwakkwaran shiri na kubutar da 'yan uwansu ba idan aka sace su ba.










