Bulaguro hudu da Buhari ya yi lokacin da kasar take cikin alhini
Ahmad Tijjani Bawage
BBC Hausa

Asalin hoton, Buhari Sallau
A ranar Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya tafi kasar Laberiya don taya ta murnar cika shekara 175 da samun ƴancin kanta.
Tafiyar shugaban na zuwa ne kwana biyu da sakin wani bidiyo da ya nuna ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna na zane su da bulala tare kuma da azabtar da su.
Akwai lokuta da dama da shugaban kasar ke yin bulaguro a daidai lokacin da kasar ke cikin wani alhini, musamman halin tabarbarewar tsaro da kasar ke fama da shi, wanda mutane ke bayyana cewa yana nuna halin ko-in-kula ga yanayin da ƙasar ke ciki.
A wannan maƙala ta musamman, BBC Hausa ta duba wasu tafiye-tafiye huɗu da shugaban ya yi a lokacin da kasar ke cikin alhani.

Asalin hoton, Buhari Sallau
Disamban 2021 – Tafiyarsa Legas bayan kashe mutum 23 a harin Sabon Birni
A watan Disamban 2021, Shugaba Buhari ya tafi Legas domin ƙaddamar da littafi, a daidai lokacin da 'yan bindiga suka ƙona wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-ɓauna a wani yanki na jihar Sokoto.
Fasinjojin sun fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar domin yin ƙaura zuwa wasu yankunan Najeriya, saboda ta'azzarar hare-haren 'yan bindiga a yankin nasu.
‘Yan Najeriya dai sun yi ta sukar shugaban a kan rashin soke tafiyar ganin irin rayukan da aka ƙona.
Sai dai shugaban ya yi wa iyalan waɗanda aka kashe jaje, inda ya ce harin na nuna irin ƙaimin da ya kamata gwamnatinsa ta ƙara kan maganin ‘yan bindiga.
Zabar tafiya zuwa Legas maimakon jihar ta Sokoto a lokacin da abin ya faru da shugaban ya yi, ya kuma fusata wasu manya a jihar kamar su tsohon gwamna Attahiru Bafarawa.
Bafarawan ya bayyana gazawar shugaban tare kuma da cewa bai damu da rayukan mutanen da suka zaɓe shi ba, saɓanin alkawarin da ya yi musu a lokacin yaƙin neman zaɓe.
Maris 2022 – Zuwa kallon wasan Najeriya da Ghana kwana biyu da harin jirgin ƙasan Abuja -Kaduna
A ranar 28 ga watan Maris ɗin 2022 ne masu tayar da ƙayar baya suka kai wa jirgin ƙasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna hari da daddare.
Sai dai ana cikin wannan hali, kwatsam washe gari sai aka ga Buhari ya tafi kallon ƙwallon ƙafa da kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta yi da takwararta ta Black Stars of Ghana a Abuja babban birnin kasar.
Bayan nan, fadar shugaban ta fitar da saƙo inda take Allah-wadai da harin da aka kai kan jirgin kasar na Abuja-Kaduna, inda shugaban ya bayar da umarnin ƙarfafa matakan tsaro a kan hanyar jirgin kasan da kuma gyara taragon jirgin da aka lalata.
Sai dai bayan nan, ‘yan kasar sun yi kiraye-kiraye na ganin an samu sauyi a ɓangaren tsaro da kuma sukar shugaban da cewa ya gaza.
Yulin 2022 - Tafiyarsa Senegal bayan harin gidan yarin Kuje da kuma hari kan tawagarsa
Kwana guda bayan kai waɗannan hare-hare, yayin kuma da ƴan Najeriya ke nuna alhininsu kan abubuwan da ke faruwa a kasar, kwatsam sai fadar shugaban kasar ta fitar da wata sanarwa cewa Shugaba Buharin zai tafi zuwa Senegal.
Harin da aka kai gidan yarin Kuje ya janyo tserewar fursunoni da dama, inda ake zargi cikin waɗanda suka tseren har da mayaƙan kungiyar ‘yan tayar da kayar baya na Boko-Haram.
A gefe ɗaya kuma, wasu ‘yan bindigar sun kai hari kan ayarin motocin shugaban ɗauke da manyan masu yi masa hidima da suke kan hanyarsu ta zuwa garinsa Daura.
Yulin 2022 – Ziyara zuwa Laberiya kwana biyu da sakin bidiyon fasinjojin jirgin ƙasa mai tayar da hankali
A ranar Asabar 23 ga watan Yulin 2022 ne, ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar Abuja-Kaduna suka fitar da wani bidiyo mai tayar da hankali, inda aka ga suna dukan fasinjojin.
Kwana biyu bayan sakin bidiyon, sai fadar shugaban ƙasar ta fitar da sanarwar cewa, tafiyar na nuna muhimmancin da ke da akwai na tsaro da zaman lafiyar Laberiya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.
Mutane da dama dai na sukar shugaban da cewa yana barin matsaloli da kasarsa ke fama da su sannan yana saka baki a al’amuran wasu kasashen, har ma da yin alkawarin taimaka musu bayan kasa yin kataɓus a ƙasarsa.
'Bai damu da kasar ba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A nasu bangaren kungiyoyin kare hakkin dan adam na kallon tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari yake yi a yayin da ake tsaka da wani mawuyacin hali a matsayin wata alama ta rashin damuwa da kasar da ma 'yan kasar.
Malam Auwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar Transparency International da ke rajin tabbatar da mulki na gari, ya shaida wa BBC cewa "ni a ganina Shugaba Buhari bai damu da Najeriya da halin da take ciki ba.
"Abin da na ya sa fadi haka shi ne, yawancin shugabannin kasashen duniya kan koma kasashensu yayin da wani abin takaici ko bala'i ya same ta a duk inda suke.
"Amma shi sau da dama yana ma tafiyarsa zuwa wasu kasashen a yayin da kasarsa ke cikin mawuyacin hali. Wannan ya faru a lokuta da dama," in ji shi.
Ya kara da cewa shugaban na Najeriya ba shi da masu ba shi shawara na gari, shi ya sa yake yin abin da ya ga dama.
"Kuma a halin da ake ciki sai dai kawai mu yi addu'ar ya gama mulki ya tafi, domin abin da ka kwashe shekara bakwai ba ka yi ba, babu yadda za ka sauya a 'yan watannin da suka rage masa."
Wane martani fadar shugaban Najeriyar ta mayar?
BBC ta tuntuɓi mai magana da yawun shugaban Najeriyar Malam Garba Shehu, wanda ya ce duk masu zargin ba su san irin nauyin da yake kan shugaban ƙasar ba ne, musamman dangane da matsalolin da suka shafi yammacin Afirka.
Ya ce bai kamata Najeriya ta dinga kawar da kai daga kan al'amuran da suka shafi maƙwabtanta musamman waɗanda suka taimaka mata a baya ba.
"Gaba ake ji, idan wata fitina ta ɓullo babu mai iya ɗaukar nauyin kawo zaman lafiya a yammacin Afirkar idan ba Najeriyar ba.
"Wannan abin yi wa kai ne," in ji Malam Garba.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ya nanata cewa ya kamata mutane su gode wa Allah domin matsalar tsaron da ake ciki a ƙasar a yanzu ba ta kai ta baya ba.
Sharhi
Bayanai sun nuna cewa a 2022 kadai, shugaba Muhammadu Buhari, ya kai ziyara zuwa akalla kasashe 10 .
A mafi yawan lokuta, ‘yan kasar na nuna ɓacin ransu kan irin tafiye-tafiye da shugaban yake yawan yi da kuma ɗumbin kudade da ake kashewa a tafiye-tafiyen wadanda ma mutanen ke cewa ‘taron shan shayi’ ne, saboda babu alfanu da za su kawowa kasar.
Sai dai tafiye-tafiyen da shugaban ke yi sun ragu bayan zuwan annobar korona, amma a yanzu, bayan soke takunkamai da aka saka a lokacin annobar, shugaban ya koma yin bulaguron da ya saba yi.











