Yadda amon wuta daga rana ke barazanar haifar da katsewar lantarki a duniya

Na'urar ɗaukar hoton NASA ta nuna wannan hoton na tururin rana.

Asalin hoton, NASA/SDO

Lokacin karatu: Minti 4

Rana takan shiga wani yanayi na yawaitar tunzuri inda takan yi amon wuta, wanda a bana ya kai ƙololuwa, kamar yada hotunan da hukumar lura da sararin samaniya ta Amurka (NASA) ta fitar suka nuna.

A cikin wannan mawuyacin yanayi, iska kan ɗauki tururin zuwa duniyar bil'adama.

Kuma irin wannan yanayi yakan shafi fannonin fasaha da ƙere-ƙere da ke nan doron duniya, har ma yana haddasa katsewar lantarki, amma ba ya da illa kai tsaye ga lafiyar ɗan'adam.

Mene ne amon wutan rana?

Hoton yadda duniyar rana ta ke.

Asalin hoton, Getty Images

Samun haɗari a duniyar rana ba baƙon al'amari ba ne. Yana faruwa ne a yayin da rana ke fitar da tururinta da ke tashi kamar wuta kuma wanda ke ɗauke da sinadarai daban-daban masu watsuwa a sararin samaniya.

Tururin mai ɗauke da sinadaran lantarki kan yi tafiya mai nisa cikin ƙanƙanin lokaci kamar walkiya, domin yakan ɗauki tsawon mintuna takwas ne kacal ya iso duniyar bil’adama.

Tururin rana yana isa duniyar mutane a cikin yanayi mabambanci.

Ƙarfin tururin da rana ke fitarwa yana fitar da hasken wuta mai launi daban-daban.

Wata mota a tsaye yayin da tururin rana ke faruwa a Hamadar Siberian na yankin Krasnoyarsk a ƙasar Rasha a ranar 2 ga watan Janairu.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

Bayanan hoto, Hoton yaddatururinn rana ke canza launin sararin samaniya.

Wane tasiri tururin rana ke da shi ga duniya?

Hukumar NASA ta ce tururin rana yana da tasiri ga ɓangaren sadarwar rediyo da hasken lantarki da kuma yadda ake aikewa da saƙonni ta intanet.

A shekarar 2017, an samu manyan-manyan tururin rana guda biyu da suka haddasa cikas ga na'urorin da ke gano wurare irin su GPS.

Yayin da a watan Febrairun 2011 kuma an samu wani tururin rana mai ƙarfin gaske da ya kawo cikas ga sadarwar rediyo a ƙasar Chana.

Turaron ɗan'adam na cikin sararin falaƙai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da irin aikin da rana ke yi tana iya haifar da illa ga ɓanagaren sadarwa

A can shekarun baya a shekarar 1989 ma an samu wani tururin rana da ya haddasa ɗaukewar lantarki wadda ta jefa miliyoyin mazauna lardin Quebec na ƙasar Canada a cikin duhu har na tsawon sa'a 9.

Yayin da a shaekarar 1859 wani tururin shi ma da ya auku a lokacin ya haifar da wani hadarin da ya shafi bangaren sufurin jiragen ƙasa na Victoria.

Wannan lamari ne da har yanzu ana iya samun sa kuma yana da matuƙar haɗari, kamar yadda wani bincike ya nuna. Jami'ar Lanchester da ke Birtaniya ta gargaɗi hukumar da ke lura da sufuri jiragen ƙasar da ta shirya wa aukuwar hadarin da ke ɗauke da tururin rana da zai iya haifar da tangarɗa duk kuwa da cewa ba a cika samun irin haka na faruwa ba.

Ko ana yawan samun aukuwar tururin rana?

Sunspots.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu alamomi masu bayyana baƙi-baƙi a jikin rana na nuna yuwar ƙaruwar tururin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rana dai an halicce ta ne da wasu nau'in iskar gas mai motsi, wada ke samar da ƙarfin fizgar magaɗishu.

Ƙarfin fizgar kan rinƙa juyawa, abin da ake kira juyawar rana. Wannan kan haifar da sararin jikin na rana ya yi tumbuɗin da zai iya kawo hadarin tururin ranar.

Duk bayan shekara 11 ko fiye ƙarfin fizgar maganaɗisu da ke kudanci da arewacin jikin ranar kan riƙa yi yana sauyawa daga wannan wuri zuwa wancan.

A cewar ƙungiyar ƙwararru waɗanda suka haɗa da na hukumar Nasa da Hukumar da ke lura da yanayin teku ta Amurka (NOAA), sun ce yanayin na yanzu da ke jujjuyawa da ake kira Solar Cycle 25, ya soma ne a watan Disamban 2019 .

Nasa da NOOA sun ce a yanzu rana ta riga ta kai ƙolin lokacin wannan jujjuyawa ta rana a bara.

A daidai ɓangarorin waɗannan baƙaƙen sassan da ke cikin rana akan samu fashewa mai ƙarfi, waɗanda kan yi duhu sosai kasancewar sun yi sanyi fiye da zagayensa. Galibin su sun mamaye sararin da ya kai girman duniyar ƙasa ta ɗan'adam ko ma fiye.

Hadarin da ke haifar da tururin rana da kan kai ƙolinsa a duk bayan shekara 11 da takan kammala zagayawa.