Me ya sa mutane da dama ke rububin zuwa Duniyar Wata a 2022?

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar nan ta 2022, kasashe, kamfanoni da kungiyoyi za su yi ta rige-rigen tafiya duniyar wata. Tuni shirin Artemis na Hukumar Kula da Sararin Samaniya mai zaman kanta ta Amurka NASA ta fara shirin tabbatar da an samu mutane da dama a can duniyar watan zuwa shekarar 2025. Wadanne abubuwa ne suke faruwa a can duniyar a bana, kuma mene ne burin masu niyyar zuwan?
Bana za a yi ta gogoriyon zuwa duniyar wata, bayan a bara ba samu ko mutum daya da ya sauka a duniyar ba.
Hukumar NASA za ta kaddamar da shirinta na Artemis, sannan za ta dauki nauyin masu burin zuwa domin kai kayayyakin aiki da sauran abubuwan da masu binciken sararin samaniya za su bukata domin gudanar da bincikensu a nan gaba.
Kasashen India da Japan da Rasha da Koriya ta Kudu da Hadaddiyar Daular Larabawa ma za su kaddamar da shirinsu na zuwa duniyar watan a bana, haka ma akwai kamfanoni da dama da suke da burin haka duk a banan.
Duk tafiye-tafiyen nan za a yi su ne da jiragen da babu matuka, kuma su ne za su zama kamar sharar fage domin tabbatar da kasancewar mutane a duniyar wata a nan da kasa da shekara 10.
Duk da cewa ba shi ba ne babban burinsu-assasa tashar sauka da tashin jirage a duniyar watan yana cikin shirye-shiryen tafiya har zuwa duniyar Mars.
Dokta Zoë Leinhardt, masanin sararin samaniya ne a Jami'ar Bristol da yake da tunanin cewa a bana za a samu wani cigaba na rige-rigen zuwa duniyar wata har da wasu kasashen da ba su damu da bangaren ba a baya.
Kasashe da dama da suke da burin zuwa duniyar watan, za su je ne domin gudanar da bincike, amma wasu suna da wata babbar manufar.
"Wasu matafiyan suna da dadadden burin zuwa duniyar watan domin tabbatar da shirinsu da kuma gwada sababbin fasaharsu da kuma wasu hadakan gwiwa da suka shiga," inji Dokta Leinhardt.
To wadanne shirye-shiryen tafiya ne a kasa, kuma mene ne manufofin kowanne daga cikinsu:
Wasu labaran masu alaƙa
Nasa Artemis-1tafiyarsu da babban burinsu
Hukumar Nasa na da wani babban buri na ganin an samu mutane da dama a duniyar wata zuwa nan da shekarar 2025.
A watan Maris mai zuwa, za a kaddamar da shirin Artemis-1, wanda shi ne somin-tabin shirye-shirye manya masu zuwa.
Za a yi tafiyan ne ba tare da matuki a jirgin ba, illa kawai 'yar tsana da za a sa a kujerar kwamandan jirgin mai suna "Moonikin". Wannan wata 'yar tsana ce da aka sanya wa sunan Arturo Campos, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen dawo da Apollo 13 duniyar nan bayan tafiyarsa duniyar wata a baya.
Aikin Campos shi ne gwada kayan tafiya sararin samaniya da masu binciken na Artemis za su saka a lokacin kaddamar da shirin, da sauran shirye-shiryen tafiyar.
Rokar Hukumar Nasa na Space Launch System (SLS), wanda shi ne roka mafi gudu a duniya ne zai fara tafiya, inda zai tafi da jirgi kirar Orion zuwa duniyar watan domin gwaji da tabbatar da lafiyar fasinjojin jirgin.
Nasa za ta mayar da hankali kan mashingin zafi na jirgin Orion din a lokacin tafiyar mai tsananin gudu a lokacin da yake dawowa duniya a kusa 2,760 a ma'aunin Celsius.
Haka kuma, a bana din dai wasu bangarori na shirin na Artemis za a samu cigaba matuka.

Asalin hoton, Getty Images
Capstone: Cislunar Autonomous
Tsarin amfani da Positioning System Technology Operations and Navigations- shi ne babban burin shirin Artemis.
Nasa za ta kaddamar da ƴar karamin na'aurar daukar hoto ta CubeStat, da jirgin tafiya sararin samaniya na Capstone duka a watan Maris na bana, domin gwada layin hasken da ke zagaye tsakanin duniyar wata da duniyar da muke ciki.
Burin shi ne a tabbatar da lafiyar masu binciken a nan gaba.
'Babban burin shi ne zuwa duniyar Mars'
Bayanan da za a samu bayan wannan gwajin zai taimaka wajen tabbatar da tsarin da aka yi na shirin Artemis- cigaban da Nasa suka bayyana a matsayin, "layukan haske da ke zagaya duniyar wata sun ba da taimakon da ake bukata domin dawowar mutane lafiyar."
Idan komai ya tafi inda aka tsara, a shekarar 2025 ce Artemis-3 zai zama tafiya zuwa duniyar wata na farko tun bayan na Apollo 17 da aka yi a shekarar 1972.
Kuma tafiyar ana sa ran a samu mace ta farko ciki, da kuma wanda ba Bature ba na farko a ciki.
Dokta Hannah Sargeant, masaniyar kimiyyar duniyoyi a Jami'ar Central Florida, ta ce mayar da hankali kan duniyar watan, yana cikin wani babban buri da ake da shi a gaba. Cigaban da ake samu kuma yana cikin wani sharar fage domin binciken sararin samaniya sosai a nan gaba.
"Amfani da mutum-mutumi wajen tafiya zuwa duniyar wata yana daga cikin tsare-tsaren gaba-gaba zuwa tashoshin sararin samaniya, sannan kuma daga can a tafi duniyar Mars," inji ta.
Tafiye-tafiyen India da Japan da UAE
Wasu kasashen da kamfanoni suma suna da shirin tafiya zuwa duniyar wata a bana.
Wasu daga cikinsu za su gudanar da bincike ne, wasu kuma za su kai kayayyakin aiki da sauransu.
Shekara biyu bayan wata tafiya da aka shirya zuwa duniyar wata ba ta yiwu ba, yanzu haka Kungiyar Binciken Sararin Samaniya na India, (ISRO), ta fara shirye-shiryen sake tafiya a wani shirinta na 'Chandrayaan-3'.
Za a kaddamar da jirgin tafiya sararin samaniya mai dauke da motar tafiya a duniyar wata a karshen rubu'i na uku na bana.
Japan na da shirye-shirye manya guda biyu a duniyar sama a bana.
Hukumar Sararin Samaniya ta Japan (JAXA) tana shirin kaddamar da jirgin tafiya sararin samaniyan a watan Afrilun bana mai suna SLIM (Smart Lander for Investigating the Moon), wanda zai samar da fasahar sauka a duniyar sama a daidai yadda aka tsara, sannan ya gano alamomin rayuwa ta hanyar amfani da fasahar gane fuska. Sannan kuma za a tafi da kayayykin daukar hoto na X-Ray Imagining and Spectroscopy Mission (XRISM) da sauransu.
Sannan kuma wani kamfanin binciken sararin samaniya na Japan mai suna ispace shi ma zai tura motar tafiyavduniyar saman a sumuni na biyu na banan. Shirin Mission 1 (M1) yana cikin tsare-tsaren Hukumar JAXA na bana na 'Hakuto-R,' wanda za a yi amfani da mutum-mutumi guda biyu wajen aikin.
Hukumar JAXA ce ta kirkiri daya-wanda karamin mutum-mutumi ne na roba mai taya biyu da ke kamar mota mai taya hudu da za ta zauko yanayin sararin duniyar wata. Dayan motar da kamfanin na Japan za su yi amfani da ita kuma ita ce Rashid da suka dauko daga Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shirin Luna 25 na Rasha da, Pathfinder Lunar Orbiter na Koriya ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Shirin Rasha na bana shi ne Luna 25.
Shi ne zai zama karo na farko da Rasha za ta tafi duniyar wata a shekara 45, sannan ta shirya zama kasa ta farko za ta sauka a yankin Kudancin duniyar ta wata.
Wannan ne yankin da Hukumar NASA ta tanada domin jiragen tafiya duniyar wata masu dauke da fasinjoji.
Hukumar Sararin Samaniya ta Rasha, Roscosmos ta shirya kaddamar da shirin ne a Yulin bana, ita kuma Hukumar Sararin Samaniya ta Koriya ta Kudu, the Korea Aerospace Research Institute za ta kaddamar da shirinta na Pathfinder Lunar Orbiter (KPLO) na tafiya duniyar watan a karshen watan Agusta na bana.
KPLO zai bincika yanayin duniyar watan ne, sannan ya samar da bayanan da ake bukata domin masu tafiyar a nan gaba.
Mutum-mutumin tafiya na kasuwanci
Kamfanoni masu zaman kansu ma na rububin tafiya duniyar watan.
A karkashin wani shirin Nasa na Commercial Lunar Payload Service (CLPS), kamfanoni za su yi hada-hadar tafiyar da matafiya zuwa duniyar wata.
Kamfanin Intuitive Machine na Houston yana shirin amfani da mutum-mutumi mai kafa shida mai suna Nova-C domin tafiya duniyar watan a farko-farkon bana.
Daga baya kuma kamfanin Astrobotic Technology da ke Pennsylvania zai gabatar da na sa a tsakiyar shekarar ta bana.
Shirin kamfanin na Peregrine Mission 1 zai dauki wasu kayayyakin bincike ciki har da mota kirar akwati mai kafa hudu.
Mene ne makasudin wadannan tafiye-tafiye?
Dokta Sargeant ta ce da yawansu za su je binciken yanayin sararin samaniyar ne, da zummar samar bayanan da za su taimaka wajen tabbatar da lafiyar matafiya da kayayyakin aikinsu daga fadawa wani hadari kamar kura ko iska mai karfi.
Hakanan kuma tafiye-tafiyen zai ba masu binciken damar gwada sababbin kayayyakin aikinsu da kuma gwada hanyoyin da za su samu ababen bukata kamar ruwa.
"Muna so mu tabbatar wadannan injunan za su yi aiki kafin mu fara tura mutane, wadanda za su ta'allaka ne da ababen bukata da su samar a can," inji Dokta Sargeant. "Ke nan wadannan ababen bukatar ne za a yi amfani da su wajen samar da mai da ake bukata domin cigaban tafiyar zuwa duniyar Mars.
"Haka kuma duniyar watan za ta zama kamar wajen gwada fasahohi da nan gaba za a yi amfani su wajen tafiya duniyar Mars da ake kira Red Planet. Ya fi kusa da dawo gida da za a iya yi a kwana uku, sama tafiya duniyar ta Mars da zai ci akalla wata shida."











