ISS: Abu 30 kan tashar kimiyya ta ƙasashen duniya da ke ƙololuwar sararin samaniya

Asalin hoton, Reuters
Shin kun san cewa akwai wata tasha ta kimiyya ta musammman ta wasu ƙasashen duniya da ke can ƙololuwar sararin samaniya?
Idan ba ku sani ba, to wannan maƙala za ta warware muku bakin zaren, don sanin yadda ita ma wannan tasha take zagaya duniya kamar yadda duniya ke zagaya rana.
A shekarar 1998 aka ƙaddamar da tashar, kuma tun lokacin 'ƴan sama jannati ke zama a cikinta.
Wuri ne mai muhimmanci, wanda masana ke gudanar da gwaje-gwaje da bincike da za su taimaka wa wasu masanan da za su biyo bayansu zuwa wasu duniyoyi kamar Mars da Duniyar Wata.

Asalin hoton, CARLOS CLARIVAN/SCIENCE PHOTO LIBRARY
1. Tashar na zaga duniyarmu ne sau ɗaya cikin kowane minti 90, kuma tana tafiyar kilomita takwas cikin ko wace daƙiƙa
2. A cikin sa'a 24 kawai, tashar na zaga duniya sau 16, yadda ta kan ci karo da fitowa da faduwar rana sau 16
3. Tsawon tashar ya kai ƙafa 357 - wato ya kai faɗin filin ƙwallon ƙafa.
4. Baya ga duniyar wata, tashar ta ISS ce ta biyu a haske a sararin samaniyar duniyarmu cikin kowane dare - ba ka bukatar amfani da na'urar telescope mai hangen nesa idan kana son ganin tashar yayin da ta ke wucewa ta saman garin da ka ke
5. Ƙasashe 16 ne suka haɗa kai wajen gina tashar ta ISS: Amurka da Rasha da Kanada da Japan da Belgium da Brazil da Denmark da Faransa da Jamus da Italiya da Hollan da Norway da Spaniy ada Sweden da Switzerland da kuma Birtaniya.
6. An gina tahar da ɗaruruwan bangarori manya da ƙanana, wannan tashar ce abu mafi girma da ɗan Adam ya taɓa ginawa - wanda ake iya rayuwa a ciki - wanda kuma aka kai sararin samaniyarmu aka ajiye
7. Baya ga wannan tashar, akwai wasu tashohin da wasu ƙasashen suka gina a sararin samaniya: Akwai tashar MIR ta Rasha da Skylab ta Amurka da kuma Tiangong ta China.
8. Rasha ta daina amfani da tasharta ta MIR, ita ma tashar Skylab ta Amurka ba ta aiki domin a shekarar 1973 zuwa 1974 ne Amurkar ta aika da tashar sararin samaniya na tsawon mako 24, amma ta rikito zuwa doron duniya bayan wannan lokacin
9. Tashar ISS ta fi ta MIR girma sau huɗu, kana ta fi na Skylab da na Tiangong girma sau biyar
10. A ɓangaren tsada, tashar sararin samaniya ta ISS ce abu mafi tsada da ɗan Adam ya taba ginawa. An ƙiyasta cewa an kashe dala biliyan 120 wajen haɗa wannan tashar kawo yanzu.

Labarai masu alaƙa


Asalin hoton, Reuters
11. Akwai makewayi guda biyu a tashar!
12. Akwai kuma ɗakin motsa jiki ɗaya da ɗakunan barci guda shida da kuma wata taga da za a iya kallon kowace kusurwar sararin samaniya daga cikin tashar
13. Jirage ko rokoki masu shawage a ƙololuwar samaniya shida na iya ziyartar tashar a lokaci guda kuma su yada zango a lokaci guda
14. Tilas ƴan sama jannati su riƙa motsa jiki na sa'a biyu a cikin kowane yini domin hana tsokar jikinsu saki yayin da suke cikin tashar
15. Fiye da na'urori masu ƙwaƙwalwa wato komfuta 50 ne ke kulawa da dukkan ayyukan da ake yi a tashar
16. An haɗa kaya masu amfani da latironi a tashar da wayoyin da tsawonsu ya kai kilomita 12
17. Mutum 230 daga ƙasashe 18 na duniya sun ziyarci tashar ta "International Space Station"
18. An gudanar da tattaki a wajen tashar har sau 205 tun watan Disambar 1998
19. Watakila a tashar ta ISS ce kawai za ka iya jin warin sararin samaniya. Wani ɗan sama jannati da ya taba zama a tashar ya bayyana yadda ya ji wani wanri mai kama da na "karfe gami da na wata iskar gas" a daidai wani mashigi tsakanin rokokin da ke yada zango a tashar, wurin da ake daidaita ƙarfin iskar da ke tsakanin na cikin tashar da wanda ke cikin rokokin da ke isa wurin

Asalin hoton, Reuters
20. Tashar ta ISS na da nauyin kilogram 420,000 - wanda ya kai nauyin motoci 320
21. Ta na da nisan kilomita 250 ne daga doron ƙasa - rokan da tashi daga duniyarmu na iya isa can cikin sa'a shida, amma akwai rokokin da ka iya isa tashar cikin sa'a huɗu
22. Ƴar sama jannati Peggy Whitson ta kafa tarihi bayan da ta shafe kwana 665 tana zama da aiki a tashar zuwa 2 ga watan Satumbar 2017
23. Yan sama jananti na cin abinci sau uku a tashar, amma babu kujeru a ɗakin cin abincin.
24. Idan suna son cin abinci, sai su sami wani wuri su rike saboda rashin nauyin da ke cikin tashar. Dukkan abinci da abin sha da su ke bukata an riga an hada su daga nan duniya a cikin wasu ledoji da kwangwanaye na musamman. Buɗewa kawai suke yi su ci. Saboda yanayin wurin, ba a bukatar firji na sanyaya abinci ko abin sha
25. Iskar da ake shaƙa a cikin tashar ana samunta ne ta hanyar kimiyya mai suna "electrolysis", wanda wata na'ura ke samarwa a cikin tashar

Ƙarin labaran da za ku so

26. Yayin da tashar ke zagaya duniya, ta kan bi ta saman yankunan da kimanin kashi 90 cikin 100 na mutane ke rayuwa.
27. Yan sama jannati na ɗaukan miliyoyin hotunan doron duniyarmu. Ana iya ganin hotunan a nan: https://eol.jsc.nasa.gov
28. A kusan cikin ko wane yini, tashar na tafiya mai nisa wadda ta kai zuwa da dawowa daga duniyarmu zuwa Wata
29. Akwai wata na'ura mai tsimi da tanadin ruwa na kimanin kashi 65 cikin 100 a tashar ta ISS wadda ke rage asarar ruwan da ake kai wa can daga duniyarmu
30. Tawagar da ke ISS kan zauna a can iya tsawon wata shida sai a sauya wasu su tafi. Mutum ɗaya ne da ya taɓa daɗewa mafi tsawo a can, wato Valeri Polyakov ɗan sama jannati Rasha, wanda ya yi wata 14.











