Wata katuwar huda a rumfar samaniya ta rufe

Asalin hoton, CAMS
Wata makekiyar huda wadda ba taba sanin da ita ba, a kafar da ke tare tarin gurbatatun sinadarai da ke sauka sararin duniya daga rana, da ake kira "ozone layer," a Arewacin wurin da duniya (north pole) ke juyawa a duk cikin sa'a 24 ta toshe bayan kimanin wata daya da ganota.
A karshen watan Maris ne, masana kimiyya a hukumar da ke bibiyar sararin samaniya (CAMS) suka gano abin da suka kira wawakekiyar tazarar da ba a san da ita a sararin samaniya ba, da ke sarke a yankin da ke fama da kankara.
A nan kusa zai bude ya zama wani wawakeken rami da ba su taba bibiya ba a bangaren arewaci.
Girmansa ya kai kasar Greenland, da yake kadawa ta saman dandaryar inda kankara ta mamaye.
Amma zuwa 23 ga watan Afirilu, an samu labarai masu dadi: "A shekarar nan ta 2020 wannan ramin da ba a sani ba da ke arewaci na shigifar ramin za ta zo karshe," kamar yadda CAMS ta wallafa a tiwita.
Me yasa aka damu da maganar Shigifa?

Asalin hoton, Getty Images
Ita shigifar dai na kare duniya daga sinadaran da rana ke fitarwa masu cutarwa.
Mafi yawa shigifar duniya na boye a can saman samaniya a kololuwar sama.
Layin da ke da tsayin kilomita 10 zuwa 40 tsakanin saman kasa, turakan shigifar sama na daya daga cikin manyan garkuwar da ke kange duniya daga zafin hasken rana.
Wawakeken rami irin wannan shinge zai yi tasirin kan yadda kankarar ke narkewa, al'amarin da ke da karfin tsananta wa garkuwar jikin halittu, tattare da Karin hadarin kamuwa da cutar dajin fata da yanar idon mutane.
Halittu da mutane daban ne.
Ratar da ke wannan wannan garkuwar na tasiri kan yawan kankarar da ke narkewa, da ke kara matsin lamba ga rayuwar dan Adam, da tsarin garkuwar jikin dan adam da karin hadarin kamuwa da kansar fata da kuma yanayin ganin dan Adam.
Sannan akwai karamar tazarar da ke shigifar samaniya da ke saman yanki mai kankara. Wannan ne karon farko da za ka iya magana kan ramin shigifar da ke tsakiyar kankara", kamar yadda CAMS ta fada.
Ta yaya wananan ramin yake fitowa yake komawa?

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ta ce karuwar ramukan cikin gaggawa ya samu ne sakamakon sauyin yanayin da duniya ba ta saba da shi ba a yankin kankara.
Yayin da iska mai karfi ta kada zuwa saman kankara na tsawon kwanaki a jere, sai ta samar da abin da masana kimiyya suka kira "sanyayyar iska mai kadawa" - wani karfi ne da ke kada kansa, tare da samar da rami a bakin shigifar.
Amma yanzu tazarar ta rufe, masana kimiyya sun ce za ta kara budewa a gaba amma idan yanayi ya samu.
"Wannan ramin shigifar da ke yankin kankara ba shi da wata alaka da cutar korona da ta janyo dokar hana fita, amma sanyayyar iska ta dogon lokaci ce ke haifar da ita," a cewar CAMS.
*"Wannan ramin shigifar alama ce ta wata babbar matsalar raguwar kwarin shigifar samaniyan, da kuma rufewar da zagayen duniya na shekara-shekara ke janyowa, baya daukar dogon lokaci wajen warkewa.
''Amma akwai kyakkyawan fatan cewa, cewa shigifar na warkewa daga wannan matsala, amma ba cikin gaggawa ba, " kamar yadda ta kara da cewa.
Ramin shigifar da ke nahiyar Antarctica har yanzu a bude yake

Asalin hoton, Getty Images
Samun ramukan a yankin arewaci abu ne da ba kasafai yake faruwa ba, amma an yi ta samun budewar ramukan duk shekara a yankin Antarctica sama da shekara 35.
Duk da cewa girman ramukan na bambanta a kowacce shekara, sai dai babu alamun zai ragu a nan kusa.
Ana dan samun murmurewa kadan-kadan tun bayan haramta amfani da sinadaran carbon da chlorine da fluorine da hydrogen a 1996.
Duka wadannan sinadarai ne da ake amfani da su wajen hada magungunan feshi da katifu da kuma iskar gas.
A cewar Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya, ramin shigifar da ke yankin nahiyar Antarctic ya ragu da kaso daya cikin uku duk bayan shekara 10 tun daga shekarar 2000.
A halin yanzu, mafi kankantar labarin da aka samu kan shigifar tun shekarar 2019 ne, amma Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya ta yi hasashen ramin ba zai cike ba duka har sai kusan nan da shekara ta 2050.











