Gagarumar girgizar ƙasar Rasha da ke haifar da tsunami a sassan duniya

Tsunami waves flood an area after a powerful magnitude 8.8 earthquake struck off Russia's far eastern Kamchatka Peninsula, in Severo-Kurilsk, Sakhalin Region, Russia, July 30, 2025.

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Tom Bennett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Wata gagarumar girgizar ƙasa mai nauyin maki 8.8 a ma'auni ta faɗa kan gaɓar ƙasar Rasha mai nisa, inda ta haifar da barazanar faruwar tusnami a faɗin yankin Pacific.

Girgizar ƙasar wadda ta faru a kusa da Lardin Kamchatka da ke Rasha da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Laraba, na ɗaya daga cikin girgizar ƙasa mafiya girma da aka taba samu.

Kimanin mutum miliyan biyu ne aka umarta su bar muhallansu a Japan da Rasha da Hawaii - sai dai an sassauta gargaɗin.

An kuma yi irin wannan gargaɗi a China da Philippines da Indonesia da New Zealand har ma da Peru da Mexico.

Taswirar yankunan da girgizar ƙasar da kuma tsunami suka shafa
Bayanan hoto, Taswirar yankunan da girgizar ƙasar da kuma tsunami suka shafa

Wace ɓarna girgizar ƙasar da tsunami suka haifar?

Bidiyon da aka gani sun nuna manyan igayar ruwa na ratsa gine-gine a birnin Severo-Kurilsk na Rasha. Hukumomi sun ce igiyar ruwa mai tsawon mita huɗu ta mamaye tashar ruwar yankin da kuma wani wurin sarrafa kifi, haka nan igiyar ruwan ta yi awon-gaba da jiragen ruwa.

Haka nan lamarin ya lalata cibiyar samar da lantarki ta yankin Sakhlin na Rasha. Har yanzu ba a tabbatar da iyakar ɓarnar da lamarin ya haifar ba.

Hukumomin yankin Sakhalin a Rasha sun janye gargaɗin da suka bayar na faruwar tsunami.

A Japan kimanin mutum miliyan 1.9 ne aka umarta su bar yankunansu sannan hukumomi sun buƙace su su koma wurare masu tudu. Igiyoyin ruwa na farko-farko da suka isa gaɓar ƙasar ba sa da ƙarfi sosai, sai dai hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta ce igiyar za ta iya kaiwa tsawon mita uku.

A Hawaii, hukumomi sun yi gargadin samun igiyoyin ruwa masu tsawon ƙafa 10, sai dai daga baya an sassauta gargaɗin da aka yi.

Bayanan bidiyo, Kalli yadda igiyar ruwa ke toroko bayan faruwar girgizar ƙasa

Wace ɓarna girgizar ƙasar za ta haifar?

Ya zuwa yanzu ɓarnar da aka gani ba ta kai wadda aka yi tsammani ba - duk dai dai cewa igiyoyin ruwa na ci gaba da faɗaɗa a tekun Pacific.

"Ko a yanzu, masana kimiyya na sake yin nazari kan hasashen da suka yi a farko," in ji Chris Goldfinger, farfesan kimiyyar muhallin teku a Jami'ar Jihar Oregon.

"Kowace ƙasa, kowace tashar ruwa da kuma duk wata gaɓa za ta fuskanci tasirin girgizar, wasu za su fuskanci tasiri mai muni, wasu kuma mai sauƙi-sauƙi."

Ya ce "zai ɗauki tsawon "sa'o'i takwas zuwa tara" kafin tsunami daga Kamchatka ta kai gaɓar ƙasar Amurka.

Mene ne tsawon lokacin?

Girgizar ƙasar ta faru ne da kimanin ƙarfe 11:25 na safiyar Laraba, agogon cikin gida.

Igiyar ruwa ta fada kan gaɓar nahiyar Amurka ta Arewa da kimanin ƙarfe 12:20 na tsakar dare, agogon cikin gida.

"Yadda abin yake shi ne, igiyar ruwar tsunami tana gudu ne kwatankwacin irin na jirgin," in ji Helen Janiszewski, ƙaramar malamar jami'a a Jami'ar Hawaii.

"Idan ka yi tunanin yadda jirgi zai tashi daga wani wuri zuwa wani, to haka ambaliyar tsunami ke gudu daga inda abin ya faru," in ji ta.

Girgizar ƙasa masu muni da aka samu a tarihi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar kula da yanayin ƙasa ta Amurka ta ce girgizar ƙasar ta faru ne a kusa da doron ƙasa - inda ta faru a kimanin zurfin kilomita 20.7, kuma asalin inda abin ya faru na da nisan kilomita 119 ta kudu maso gabashin yankin Petropavlovsk-Kamchatsky.

Da farko an auna maki 8.0 na girgizar sai dai daga baya an gano cewa ta zarce haka. Kuma an samu wasu ƙanana-ƙananan motsin ƙasa daga baya.

Yanzu an haƙiƙance cewa ita ce girgizar ƙasa ta shida mafi ƙarfi da aka taɓa samu a doron ƙasa, inda suke da ƙarfi iri ɗaya da girgizar ƙasar da aka samu a shekara ta 2010 a Biobio da ke Chile da ta shekarar 1906 a Esmeraldas da ke Ecuador.

Girgizar ƙasa ta biyar mafi ƙarfi a tarihin duniya, ita ma ta faru ne a Kamchatka Krai da ke Rasha a 1952. Ita ce girgizar ƙasa ta farko a duniya da aka samu wadda ta kai ƙarfin maki 9.

Idan za a yi kwatanta, girgizar ƙasa da guguwar tsunami da aka samu a shekarar 2004 a tekun Indian Ocean - wadda ta kashe mutuane 227,000 - tana da maki 9.2 zuwa 9.3.

Ta faru ne a wani wuri da ke da nisan kilomita 160 daga kan gaɓar yankin Sumatra na ƙasar Indonesia - wurin da ke da yawan al'umma.

Yankin Kamchatka na Rasha ba ya da cunkoson al'umma.

A world map displaying the ten largest earthquakes recorded since 1900, marked with red circles and numbered from 1 to 10. The earthquakes are listed below the image with their respective magnitudes, locations, and years: 1) Magnitude 9.5 in Biobío, Chile, 1960; 2) Magnitude 9.2 in Alaska, US, 1964; 3) Magnitude 9.1 in Tōhoku, Japan, 2011; 4) Magnitude 9.1 in Sumatra, Indonesia, 2004; 5) Magnitude 9 in Kamchatka, Russia, 1952; 6) Magnitude 8.8 in Kamchatka, Russia, 2025; 7) Magnitude 8.8 in Biobío, Chile, 2010; 8) Magnitude 8.8 in Esmeraldas, Ecuador, 1906; 9) Magnitude 8.7 in Alaska, US, 1965; 10) Magnitude 8.6 in Sumatra, Indonesia, 2012
Bayanan hoto, Girgizar ƙasa mafiya muni a tarihin duniya