Man United na son Kolo, Juventus za ta soke kwantaragin Pogba

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Manchester United na shirin daukar Randal Kolo Muani, Real Madrid na zawarcin William Saliba na Arsenal, yayin da Chelsea ke ci gaba da zawarcin Victor Osimhen.

Manchester United ta shirya tayin fan miliyan 58.6 kan dan wasan Paris St-Germain dan kasar Faransa Randal Kolo Muani mai shekaru 25. (Fichajes)

Real Madrid na son siyan dan wasan bayan Arsenal da Faransa William Saliba a matsayin "babban fifiko" a shekarar 2025, inda tuni Los Blancos ta tuntubi dan wasan mai shekaru 23. (Le 10 Sport - a Faransanci), waje

Galatasaray za ta yi kokarin mayar da dan wasan Najeriya Victor Osimhen da yaje kungiyar aro daga Napoli a matsayin dan was anta na dindindin, yayin da Chelsea ke ci gaba da zawarcinsa. Sai dai farashin dan wasan mai shekaru 25 zai kai fam miliyan 68 a watan Janairu ko kuma fam miliyan 63 a bazara mai zuwa. (Corriere dello Sport)

Manchester City na tunanin daukar golan Porto Diogo Costa, mai shekara 25, don maye gurbin Ederson, amma dan wasan na Portugal zai kai fam miliyan 63. (Caught Offside)

Manchester United ta sanya dan wasan baya na Chelsea Ben Chilwell, mai shekara 27, a matsayin wanda ta fi bukata a watan Janairu. (Teamtalk)

Dan wasan tsakiya na kasar Sipaniya Martin Zubimendi ya sake nanata bukatarsa ta ci gaba da zama a Real Sociedad duk da rade-radin da ake ta yi na cewa Manchester City na zawarcinsa. (Mirror)

Crystal Palace za ta kara zawarcin dan wasan gaban Hammarby dan kasar Ivory Coast Bazoumana Toure, mai shekara 18, wanda suma Manchester United da Celtic ke zawarcinsa. (Give me sport)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Har yanzu Arsenal za ta yi zawarcin dan wasan gaba a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu, duk da dan was an gabanta na Jamus Kai Havertz y afara da kafar dama. (Football Insider)

Dan wasan bayan Liverpool Virgil van Dijk, mai shekara 33, na daf da sabunta kwantiraginsa bayan da kulob din ya tabbatar da ci gaba da zaman dan wasan Faransa Ibrahima Konate mai shekara 25. (Teamtalk)

Arsenal da Tottenham da Newcastle United duk suna zawarcin matashin dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Jacob Ramsey, mai shekara 23. (Give me sport)

Newcastle na iya sayar da dan wasan gaban Ingila Callum Wilson, mai shekara 32, a watan Janairu domin saukaka yunkurin siyan sabon dan wasan gaba. (Football Insider)

Marseille na ci gaba da tattaunawa don siyan dan wasan tsakiyar Faransa Paul Pogba, mai shekara 31, wanda zai iya sake buga wasa daga watan Maris bayan dakatarwar da aka yi masa na tsawon shekaru hudu kan laifin kara kuzari zuwa watanni 18. (Madubi), waje

Za a soke kwantaragin Pogba a Juventus bayan dakatarwar da aka yi masa. (Fabrizio Romano)