Arsenal da Man City na farautar Wirtz, Lampard na son zama kocin Ingila

Florian Wirtz

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal da Bayern Munich da Manchester City da kuma Real Madrid na rige-rigen saye ɗan wasan Jamus mai buga tsakiya Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kaka ta gaba, yayinda ƙungiyarsa ta Bundesliga ke neman yuro miliyan 150 a kan matashin mai shekara 21. (Bild - in German)

Kocin Newcastle United Eddie Howe da kuma tsohon koci a Chelsea Graham Potter sun kasance a kan gaba a takarar maye gurbin Erik ten Hag da zarar ya bar Manchester United, yayinda tsohon kocin Ingila, Gareth Southgate da kocin Inter Milan Simone Inzaghi kowanne suma na kan layi. (Teamtalk)

Amma rahotanni na nuna cewa tsohon kocin Juventus, Massimiliano Allegri ya fi kwanciya a zuciyar Sir Alex Ferguson domin ci gaba da tafiyar da Manchester United. (Express)

Kocin Southampton Russell Martin na sake tsunduma cikin barazanar rasa aikinsa saboda rashin taɓuka abin kirki tun farkon kaka.(Mirror)

Tsohon kocin Chelsea, Frank Lampard ya nuna kwaɗayinsa kan aikin horar da tawagar Ingila, da yanzu haka ke karkashin mukaddashin koci Lee Carsley. (Football London)

Ɗan wasan tsakiya a Real Sociedad da Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 25, ya ce ba shi da nadama kan watsi da tafiya Liverpool a kakar da ta gabata. (Mirror)

Mai buga gefe a Borussia Dortmund Karim Adeyemi ɗan shekara 22 ya kasance wanda Liverpool ke zawarci. Matashin mai taka leda a Jamus, ƙungiyar na son ya maye gurbin ɗan wasan gaba Mohamed Salah a sabuwar kaka. (Sun)

Everton ba ta nuna damuwa kan cinikin 'yan wasan watan Janairu ba, da Liverpool ke neman rabata da Jarrad Branthwaite mai shekara 22. (Liverpool Echo)

Everton na iya sake gwada sa'arta kan ɗan wasan Paraguay Miguel Almiron, mai shekara 30, da watakil ya bar Newcastle United a Janairu. (Teamtalk)

Manchester United na iya tsawaita zaman ɗan wasanta mai shekara 31 da karin shekara guda, Harry Maguire. A bana kwantiraginsa ke karewa kuma bata son ya bar kungiyar a kyauta. (Football Insider)