PSG na kan gaba a son Salah, Utd za ta taya Akturkoglu

 Mohamed Salah

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Paris St-Germain na kan gaba a ƙungiyoyin da ke fafutukar ɗaukar Mohamed Salah, kuma ƙungiyar za ta yi ƙoƙarin lasa wa ɗan wasan na Masar mai shekara 32, wanda kwantiraginsa zai ƙare a Anfield a ƙarshen kakar nan, zuma a baki ta hanyar ba shi kwantiragin shekara uku. (Sun)

Ita kuwa Liverpool tana son sayen ɗan wasan gaba na Borussia Dortmund Karim Adeyemi a matsayin wanda zai gaji Salah, kuma a shirye take ta taya ɗan wasan na Jamus mai shekara 22 fam miliyan 41. (Bild)

Manchester United na shirin taya ɗan wasan gaba na gefe na Benfica, Kerem Akturkoglu, ɗan Turkiyya mai shekara 25 a kan kusan fam miliyan 34. (Fichajes )

Wataƙila Newcastle United ta sake komawa zawarcin babban ɗan bayan Ingila Marc Guehi a watan Janairu, da kyautata zaton Crystal Palace za ta sayar mata da ɗan wasan mai shekara 24. (Mail)

Har yanzu Chelsea na son ɗan wasan gaba na Kolombiya Jhon Duran, to amma kuma Aston Villa na son kuɗin da ya zarta fam miliyan 80 a kan matashin ɗan wasan mai shekara 20 wanda tauraruwarsa ke haskawa a yanzu. (Teamtalk)

Barcelona da Juventus na sa ido a kan halin da ɗan wasan gaba na gefe na Argentina, Alejandro Garnacho, mai shekara 20, ke ciki, wanda kuma aka yi amanna Manchester United ta yi masa kuɗi fam miliyan 50. (Sun)

Ana ganin kociyan Fenerbahce Jose Mourinho zai kasance cikin waɗanda za su iya maye gurbin Sean Dyche a matsayin kociyan Everton idan Dan Friedkin ya kammala sayen ƙungiyar. (Football Insider)

Ɗan bayan Chelsea da Ingila, Ben Chilwall, mai shekara 27 shi ne ɗan wasan da Atletico Madrid take son saye a yanzu. (Teamtalk)

Newcastle United na daga cikin ƙungiyoyin da ke kan gaba wajen son sayen ɗan gaban Kanada Jonathan David, mai shekara 24 daga Lille. (GiveMeSport)

Ɗan gaban Norway Erling Haaland, mai shekara 24, na shirin sanya hannu a sabon kwantiragi da Manchester City amma kuma yana son a ƙara da damar sayar da shi ga duk ƙungiyar da za ta biya fam miliyan 100 a kanshi. (Teamtalk)

Daman kuma Barcelona na sanya burin sayen Haaland ɗin a bazarar 2025 babban abin da ta sanya a gaba a cinikayyarta. (SPORT)

Sir Jim Ratcliffe zai halarci wasan Premier da Manchester United za ta yi a gidan Aston Villa ranar Lahadi yayin raɗe-raɗi a kan makomar kociyan ƙungiyar Erik ten Hag ke ta ƙaruwa (Mirror)