An kara bai wa Fernandes jan kati a wasan Porto a Europa

Bruno Fernandes

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 2

Porto da Manchester United sun tashi 3-3 a wasa na bibiyu a gasar zakarun Turai ta Europa League da suka buga ranar Alhamis a Portugal.

United ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Marcus Rashford, sannan Højlund ya kara na biyu a raga.

Daga nan ne Porto ta zare ɗaya ta hannun Pepe, sannan Samu Omorodion ya farke na biyu, sai kuma ya ci na uku.

Daga baya ne United ta farke na uku ta hannun Harry Maguire daf da za a tashi daga karawar da suka yi.

Koda yake an bai wa ƙyaftin ɗin United, Bruno Fernandes jan kati, wanda aka kora a wasan Tottenham a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Daga baya United ta shigar da kara kan jan katin Fernandes, wadda ta yi nasara aka soke, kenan zai buga wasan Premier na gaba da United za ta je Villa Park.

Wannan shi ne wasa na tara da aka buga tsakanin ƙungiyoyin biyu, inda Porto ta yi nasara biyu da canjaras huɗu da canjaras uku da suka yi.

Wasan da aka buga tsakanin Porto da Manchester United:

2024/25

Europa League Alhamis 3 ga watan Oktoba

  • Porto 3 - 3 Man Utd

2008/2009

Champions League Laraba 15 ga watan Afirilu 2009

  • Porto 0 - 1 Man Utd

Champions League Talata 7ga watan Afirilu 2009

  • Man Utd 2 - 2 Porto

2003/2004

Champions League Talata 9 ga watan Maris 2004

  • Man Utd 1 - 1 Porto

Champions League Laraba 25 ga watan Fabrairu 2004

  • Porto 2 - 1 Man Utd

1996/1997

Champions League Laraba 19 ga watan Maris 1997

  • Porto 0 - 0 Man Utd

Champions League Laraba 5 ga watan Maris 1997

  • Man Utd 4 - 0 Porto

1977/1978

Euro Cup Winners Cup Laraba 2 ga watan Nuwamba1977

  • Man Utd 5 - 2 Porto

Euro Cup Winners Cup Laraba 19 ga watan Oktoba 1977

  • Porto 4 - 0 Man Utd

Manchester United za ta je gidan Aston Villa ranar 6 ga watan Oktoba a Premier League daga nan ta kara da Brentford a Old Trafford ranar 19 ga watan Oktoba.