Shin zaman kaɗaici na da amfani gare ka?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Andre Biernath
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 7
An bayyana kaɗaici a matsayin wata barazana da ke da illa ga lafiya wadda haɗarinta ya kai kwatankwacin shan sigari kara 15 a rana.
Amma kuma a wani gefen, mukan iya samun ɗaruruwan sakonni a kan wayoyinmu a duk rana. Irin waɗannan sakonnin kan yi wa mutum yawa har ya sanya shi jin yana buƙatar ya samu salama.
Shin, za a iya samun daidaito kuwa? BBC ta tambayi masana kiwon lafiya kan ra'ayoyinsu.
Akwai bambanci tsakanin zaɓin keɓe kai da kaɗaici?
Duk da dai wannan ba sabuwar matsala ba ce, kaɗaici ya zame wa miliyoyin mutane matsala lokacin da aka shafe tsawon lokaci a kulle a gida saboda annobar Korona. Ya bar mutane da dama maƙale a gida su kaɗai.
Kaɗaici wani ''yanayi ne mara daɗi da mutum ke samun kansa a ciki a lokacin da baya samun shiga ko mua'amala da mutane kamar yadda yake so,'' inji Andrea wigfield, shugabar cibiyar nazari kan kaɗaici ta jam'iar Sheffield Hallam da ke Birtaniya.
Masana na ganin cewa hakan na faruwa ne idan ka ji mu'amalarka da mutane ta yi ƙasa da yadda kake so. Ko kuma idan kana kwatanta alaƙar da kake da ita da mutane, da kuma waɗanda abokanka ke da su da mutane - za ka iya jin rashin gamsuwa cewa naka abotan ko mu'amalar ba ta da ƙarfi.
A yayin da wanda ya keɓe kansa zai iya shiga kaɗaici da sauri, hakazalika da gaske ne za ka iya jin kaɗaici ko a cikin gwamman mutane ne.
Jin cewa kamar ba ka dace a wani wuri ba, ko kuma alaƙar da kake da ita ba ta da ƙarfi, hakan zai iya kaika ga jin wannan yanayi na kaɗaici cikin sauri, a cewar Wigfield.
Duk da dai wasu harsuna suna amfani da kalmomin a matsayin abu ɗaya, zaɓin keɓewa daga mu'amala da mutane a haƙiƙance, wani yanayi ne kamar na wucin gadi da zai iya kawo wa mutum wani yanayi na nutsuwa.
Zaɓin keɓewa daga mu'amala da mutane zai iya zama wani lokaci da kake kai ɗaya kuma ba ka mu'amala da kowa a shafukan sada zumunta, in ji Thuy-Vy, farfesa a fannin ilimin halayyar ɗanadam a jami'ar Durham da ke Birtaniya.

Asalin hoton, Getty Images
Me kaɗaici yake yi wa jikinka?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kaɗaici abu ne mara kyau ga lafiya, wani sabon bincike da aka gudanar a jam'iar Cambridge ya bayyana alaƙar kaɗaici da barazanar iya kamuwa da ciwon zuciya, shanyewar ɓarin jiki, ciwon sukari da kuma saukin kamuwa da wasu cutukan.
Wigfield ya kara da cewa ana ƙara samun hujjoji da ke nuna kaɗaici na iya kai wa ga ciwon mantuwa, da ciwon tsananin damuwa da fargaba da kuma shafar ɗabi'a bakiɗaya.
Zuwa yanzu ba a gane alaƙar hakan ba. Likitoci na ganin cewa alaƙar ka iya zama saboda ƙaruwar gajiya da jiki ke yi da kuma ƙarancin saita tunani saboda kaɗaici, wanda hakan ke ta'azzara yanayin lafiyar kwakwalwa.
Hukumar lafiya ta duniya ta yi ƙiyasin cewa babban mutum ɗaya cikin mutane huɗu na fuskantar kaɗaici, kuma kashi 5 zuwa 15 na masu tasowa na fama da kaɗaici.
Baya ga shekaru, wasu rukuni na mutane na da ƙaruwar barazanar zama cikin kaɗaici, kamar baƙin haure da ƙabilu marasa rinjaye, da masu neman mafaka da masu sauya jinsi, da masu kula da marasa lafiya da kuma mutane masu wasu ciwukan na daban.

Asalin hoton, Getty Images
Ta yaya za ka shawo kan kaɗaici?
A shekarun baya bayan nan, gwamnatoci da dama sun ƙaddamar da shirye-shiryen magance matsalar kaɗaici.
Bincike ya nuna cewa yin ayyukan sa kai na iya zama wani mataki na kariya. A hong Kong, wani gwaji da aka yi kan mutane 375 masu aikin sa kai ya nuna cewa amfani da lokacin da ba ka komai don yin wani abu da ka yarda da shi na iya yaye kaɗaici, musamman kan manya.
Ƙasashen Autraliya da Netherlands kuwa sun ɗauki wani mataki na daban ta hanyar ƙarfafa rayuwa tare tsakanin manya da ƙanana. Ana ƙarfafawa tsofaffi da matasa yin rayuwa tare a wuri ɗaya kamar rukunin gidaje ko wasu cibiyoyin alumma.
Akwai kuma ƙaruwar wani mataki da likitoci ke ɗauka a Birtaniya kan mutanen da ake zargin suna fama da matsanancin kaɗaici wanda za a ƙulla alaƙa tsakaninsu da wasu mutane maimakon a rubuta musu magani.
Holan Liang, likitar ƙwaƙwalwa ta yara da matasa, ta yi bayani daga mahangar alumma, inda ta ce samar da alumma da ke da juriya da ke haɗa kai wanda kowa yana da gurbi da kuma manufa zai taimaka matuƙa.
''Bibiyar juna da kyautatawa da taimakawa mutane na taimakawa wajen rage kaɗaici,'' in ji Liang, wadda ita ta wallafa littafin A Sense of Belonging.
Ga kowani mutum kuwa, masana sun shaidawa BBC cewa ya kamata kowa ya sanya ido kan abin da ke samar musu da biyan buƙata da kuma ingancin alaƙar su da mutane da abotansu.
Masana sun kuma ce a sanya ido kan alamun da ke nuna kaɗaici, kamar yawan bacin rai da kuma ƙarancin buƙatar mau'amala da mutane ko fita daga gida.
Alamomin gargaɗi sun haɗa da rashin jin son wata alaƙa da mutane ko wurare da ke kewaye da mutum.

Asalin hoton, Getty Images
Ana kyarar wanda ya zaɓi ya keɓe kansa?
Farfesa Nguyen ta bayyana muhimmmancin cewa mutum a matsayinsa na ɗanadam, yana dogara ne da alaƙa da mutane wadda akwai wasu tsare-tsare da yakamata a bi domin rayuwa
A kan hakan ne ''mu kan fi mayar da hankali ne kawai kan mu'amala da kuma kasancewa tare. Saboda haka ana kyarar wanda ya buƙaci ya ɗan keɓe kanshi daga mu'amala da mutane,'' in ji ta. Sai dai '' ɗaya daga cikin tasirin keɓewa shi ne samun kwanciyar hankali nan take.''
Wani bincike a jami'ar Reading da ke Birtaniya ya nuna cewa keɓe kai na da alfanu.
Masu bincike sun bibiyi wasu manyan mutane 178 na tsawon kwanaki 21. A cikin wannan lokaci, waɗanda ake bibiyar an buƙace su suyi rubutu tare da amsa wasu tambayoyi domin a auna gajiyarsu da samun gamsuwa a rayuwarsu da cin gashin kansu da kuma kaɗaicinsu.
Binciken ya bayyana cewa shafe sa'oi cikin kaɗaici na da alaƙa da ƙaruwar jin raguwar gajiya, ƴancin yin zaɓi da kuma kasancewa yadda kake so, wanda a cewar masu rubutun, na nuna tasirin kwantar da hankali da keɓe kai ke da shi.
Sai dai a ranakun da suka shafe sa'oi masu tsawo su kaɗai, waɗanda akayi binciken kansu sun nuna cewa sun ji yanayin kaɗaici ko kuma rashin samun gamsuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda za ka samar wa kanka lokuta masu ma'ana
Alamu sun nuna cewa zaɓin keɓewa daga mu'amala da mutane na samar da wani yanayi na daidaita halin da mutum ke ji, kamar jin ƴanci da cin gashin kai. Don haka wani abu ne da zai iya amfani a yanayin da muke fuskantar matuƙar gajiya ko kuma a ranakun da muke jin abubuwa sun cakuɗe sunyi mana yawa.
Saboda haka, zaɓin keɓewa na iya taimakawa samun lafiyar kwakwalwa da juriya. Sai dai kuma kasancewa cikin kaɗaici kan iya zama abin damuwa ga wasu mutane.
Farfesa Nguyen ta bayar da shawarar gina lokacin kasancewa kai kaɗai zuwa wani abu da zai zama kana yin shi kullun.
'' A duk lokacin da mutane suka tambaye ni yadda za su ribaci zaɓin keɓewa daga mu'amala da mutane, abu ɗaya da nake yawan basu shawara kai shi ne ku fara a hankali, kamar minti 15 duk rana,'' in ji ta.
A cikin wannan ƙanƙanin lokacin, za ka iya fahimtar yadda kake ji da abin da kake son yi. Kuma yayin da ranakun ke wucewa, sai ka fara ƙara lokacin, minti bayan minti.
'' Wasu lokutan mutane kan so su fara da rage lokacin da suke shafewa a kan wayoyinsu ko a cikin shafukan sada zumunta na tsawon kwanaki. Hakan zai iya samar da rashin jin daɗi kuma ba zaka so ka ƙara yi nan gaba ba,'' in ji ta.
Amma akwai iyaka?
Alƙaluma daga jam'iar Reading sun nuna cewa mutane sun fi jin kaɗaici da rashin samun gamsuwa a ranakun da suka shafe ƙarin sa'oi a keɓe.
A wurin Nguyen, samun daidaito ba da sa'oi ake gwada shi ba, ya kamata a kalle shi ne ta fuskar ingancinsa.
Ta bayyana cewa wasu binciken sun nuna jin kaɗaici na somawa ne idan muka kasance mu kaɗai na kashi 75 cikin ɗari na sa'oin da muke a farke.
Sai dai ta ce a tunaninta '' hakan ya dogara ne ga kowane mutum da yadda yake ji a kullum''.
To mene ya kamata ayi a waɗannan lokuta?
Masana sun bayar da shawarar samun abubuwan da za su tsima ka amma kuma za su samar maka da hutu da nutsuwa.
Daga cikin abubuwan da ke dai-dai da lokacin zaɓin zama a kaɗaici sun haɗa da karatu da aikin lambu da tafiya cikin abubuwa kamar su tsirrai da gaɓar teku ko sauraron waƙoƙi ko girki ko kuma ƙirƙire-ƙirƙire.











