Yadda maganin ƙarfin maza ya sauya yadda ake kallon al'adar saduwa

Maganin Viagra

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Ana ganin gano maganin ƙarfin maza na Viagra a matsayin wani muhimmin abu a tarihin rayuwar jima'i, sai dai wani abun mamaki shi ne an gano maganin ne kwatsam - yayin da ake gwajin magungunan wata cuta, wadda take buƙata ta daban.

An fara sayar da Viagra ne a shekarar 1998, kuma nan take ya zama maganin da aka fi saya a duniya.

Wannan magani wanda wani kamfanin magunguna a Amurka ya gano bagata-tan, ya zama maganin da ya fi kawo musu ɗimbin kuɗi a yanzu.

A watanni uku na farko kaɗai, an yi kiyasin cewa Amurkawa sun kashe dala miliyan 400 wajen sayan maganin don magance matsalar rashin ƙarfin maza.

Shahararren ɗan kwallon duniya, ɗan ƙasar Brazil Pele - bai zama wanda kamfanin maganin ta saka a jikin kwalinta ba duk da shahararsa.

Fafaroma wanda ya kasance jagoran ƴan addinin Kirista a faɗin duniya, shi ma ya nuna goyon bayansa ga Viagra.

South Wales a Birtaniya

Asalin hoton, Getty Images

Ƙoƙarin ma'aikata ne ya samar da maganin

Gwajin magani.

Asalin hoton, BBC / TWO RIVERS MEDIA

Bayanan hoto, Ɗaya daga cikin waɗanda suka shiga gwajin sabon maganin Adrus Price.

Tarihin maganin na ƙarfin maza (Viagra) yana da alaƙa mai ƙarfi da garin masana'antu na Margate da ke kudancin Wales, a Birtaniya.

Yawancin maza a garin suna yi aiki ne a kamfanin ƙarafa. Amma an kai wani lokaci da aka tilastawa ma'aikatan barin kamfanin - sun koma neman aiki a wasu wurare.

Wasu daga cikin waɗannan mutane da ba su da aiki, sun shiga aikin taimako a wata cibiyar bincike.

A cibiyar ce ake gwaje-gwaje kam magunguna da za a samar.

Da farko, babu wani daga cikinsu da ya yi tunanin cewa binciken da za su yi za zama tarihi.

Kusan shekaru 30 bayan nan, sun gano cewa binciken da suka yi na gwajin magani, ya warkas da miliyoyin maza da ke fama da rashin ƙarfin mazakuta.

A farkon shekarun 1990, kamfanin magunguna na Pfizer ya kasance yana gwajin wani sinadari mai suna Sildenafil UK 90,480.

Burin yin haka shi ne yin amfani da sinadarin domin samar da maganin hawan jini da ciwon zuciya.

Shi ya sa kamfanin ya gudanar da bincike a cibiyoyin bincike, inda suka ɗauki mutane kalilan domin gwajin maganin.

Babban sauyi

Maganin Viagra

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kai wani lokaci da waɗanda suka shiga gwajin, suka ki mayar da maganin.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An yi gwajin maganin kan mutane da ke fama da matsalar rashin ƙarfin maza a asibitin Southmead a Bristol, da ke Ingila.

An sake gudanar da gwaji a shekarar 1994 a birnin Swansea, da ke Birtaniya - inda aka gwada shi kan masu cutar suga da cutukan zuciya waɗanda suka yi ƙorafin fama da rashin kuzari da ƙarfin maza.

"Pfizer ya ce a gudanar da binciken kan maza da ke mu'amala da mata," a cewar David Price, shugaban tawagar gwajin.

Hakan na nufin maza da ke mu'amala da jinsin mata kaɗai (ba masu mu'mala da duka jinsuna ba).

"Mun gwada maganin kan mutane da dama. Sun kasance waɗanda ke aiki da kuma suka yi aure waɗanda suka fito daga birnin Swansea.

"An nuna wa mutanen bidiyon batsa yayin gwajin," in ji shi.

An saka wata na'ura cikin al'aurar mazan da ke cikin gwajin domin bin diddigin tasirin maganin. Likitoci sun tabbatarwa mutanen cewa babu wata matsala gare su.

Har ila yau, irin wannan gwaji da aka yi a Bristol ya samu nasara.

Pfizer ya gano cewa maganin 'babban sauyi ne' wandazai kawo sauyi mai ma'ana a ɓangaren.

Abin da ya sa aka fitar da maganin kasuwa

An samu nasarar gwajin maganin na Viagra abin da ya sa kamfanin Pfizer ya yanke shawarar fitar da shi kasuwa da wuri.

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da maganin a cikin wata shida.

Daga nan sashen kasuwanci na Pfizer ya fara tunanin yadda zai tallata sabon maganin yadda ya kamata.

Ƙwararru sun yi shakkun cewa ko jama'a za su yi na'am da maganin ko kuma ya zama 'bala'i'.

Pfizer ya nuna damuwa kan fitar da maganin 'ƙarfin maza' zuwa ƙasashe masu ra'ayin riƙau a lokacin.

Sun yi amfani da martanin mutane a lokacin gwajin a cikin sakonsu na tallata maganin.

Jennifer Dobler, tsohuwar babbar jami'ar kasuwanci a Pfizer, ta ce "Mun samu bayani biyu daga binciken, na farko kan yadda rashin ƙarfin maza ke shafar rayuwar mutum. Na biyu, yadda yake shafarsu lokacin jima'i.

"Batutuwan sun yi tasiri a gare ni."

A 1998, bayan tallata maganin ga jama'a yadda ya kamata, sai aka fitar da Viagra zuwa kasuwannin Amurka da Birtaniya. Viagra ya fara shiga kasuwa ne karkashin sunan 'Blue Pill'.

Maganin Viagra

Asalin hoton, PFIZER

Bayanan hoto, Tallan maganin Viagra a 2006

Maganin da aka fi saurin saya a duniya

mm

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Viagra shi ne magani na farko a tarihi da aka amince da shi don maganin matsalar rashin ƙarfin maza.

Viagra shi ne magani na farko a tarihi da aka amince da shi don maganin matsalar rashin ƙarfin maza.

Ya zama maganin da aka fi saurin saya a tarihin duniya, inda a shekara ake iya sayar da maganin da ya kai na dala biliyan 2 a shekarar 2008, kuma na farko da aka taɓa samun haka.

Ader na cikin mutanen da suka taimaka wajen samar da Viagra. Miliyoyin mutane sun ci alfanu saboda waɗannan mutane.

Sai dai bai san cewa maganin zai zama sananne haka ba.

"Na kaɗu lokacin da samu labarinsa," in ji Ader. "Viagra babban magani ne. Ina cike da farin ciki cewa an samar da shi a birnin mu."

David Brown, wanda yana cikin mutanen da suka samar da maganin, ya ce in ba don mutanen South Wales ba, da Viagra bai zo duniya ba.

"Sun kafa tarihi. Zai iya sun shiga gwajin ne domin samun kuɗi, amma ƙoƙarinsu ya janyo sauyi mai ma'ana a rayukan mutane. Ya kamata su ji daɗi kan haka," in ji shi.

Ta yaya Viagra ke aiki?

Raguwar ƙarfin namiji na ɗaya daga cikin maza matsala ce da ta daɗe wadda ke addabar mutane a faɗin duniya.

A tarihi, an fara ambato wannan matsala ce tun a zamanin rubuce-rubucen Masar na zamanin da na shekarun 2000.

Sai dai samar maganin Viagra ya samar da mafita ga wannan matsala.

Maganin na ƙara ƙarfin tafiyar jini zuwa gaban namiji da kuma fitar da wani sinadari a kwakwalwa.

A cewar hukumar kula da inshorar lafiya ta Birtaniya, matsalar rashin ƙarfin namiji abu ne da ake yawan samu a tsakanin maza masu shekara 40 ya yi sama.

A cewar wasu bincike, kusan rabin mutane masu shekara 40 zuwa 70 na fama da matsalar. Maza miliyan huɗu ne ke da matsalar a Birtaniya kaɗai.

Har ila yau, wani bincike da aka yi a 2025, ya nuna cewa yawan maza da ke fama da matsalar rashin ƙarfin jima'i zai kai miliyan 322.