Abin da muka sani kan tiyatar da aka yi wa ɗan wasan Najeriya Taiwo Awoniyi

Taiwo Awoniyi

Asalin hoton, X/@NFFC

Lokacin karatu: Minti 4

An yi wa ɗan wasan gaba na ƙungiyar Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi allurar bacci mai nauyi domin taimaka masa farfaɗowa daga tiyatar da aka yi masa a cikinsa, kamar yadda bayanai suka tabbatar.

Ɗan wasan ɗan asalin Najeriya, an garzaya da shi asibiti ne domin fuskantar tiyata a ranar Litinin, bayan ya samu mummunan rauni a cikinsa a wasan da aka tashi canjaras, 2-2; tsakanin ƙungiyarsa da Leicester a gasar Premier ta Ingila.

Alamu sun nuna cewa rayuwar ɗan wasan mai shekara 27 ba ta cikin haɗari, sai dai bayanai na nuna cewa allurar baccin mai nauyi da aka yi masa za ta taimaka ne wajen tsagaita ayyukan zuciya da jikinsa wanda hakan zai taimaka wajen hanzarta samun sauƙi.

Awoniyi ya ci karo ne da ƙarfen raga sa'ilin da yake ƙoƙarin cin ƙwallo mintuna kaɗan gabanin tashi daga wasa a karawar tasu da Leicester.

Likitoci sun kwashe tsawon mintuna suna kula da shi kafin barin sa ya ci gaba da wasa.

Awoniyi ya ci gaba da wasa duk da raɗaɗin da yake ciki, kamar yadda aka gani baro-ɓaro, kasancewar a lokacin Forest ta ƙarar da yawan ƴan wasa da za ta iya canzawa a karawar.

Sai a ranar Litinin ne aka ƙara tabbatar da munin raunin da Awoniyi ya samu bayan da likitocin ƙungiyarsa suka ƙara duba shi, inda daga nan ne aka garzaya da shi asibiti domin yi masa tiyata.

Ɗan Najeriya Taiwo Awoniyi mai wasa a ƙungiyar Nottingham Forest da kuma ɗan wasan Leicester City ɗan asalin ƙasar Argentinian, Facundo Buonanotte lokacin da suka yi karo a jikin sandar ƙarfen raga a karawar da aka tashi 2-2 tsakanin Liecester da Nottingham ranar Lahadi a gasar Firimiyar Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan Najeriya Taiwo Awoniyi mai wasa a ƙungiyar Nottingham Forest da kuma ɗan wasan Leicester City ɗan asalin ƙasar Argentinian, Facundo Buonanotte lokacin da suka yi karo a jikin sandar ƙarfen raga a karawar da aka tashi 2-2 tsakanin Liecester da Nottingham ranar Lahadi a gasar Firimiyar Ingila

A ranar Talata, ƙungiyar ta Nottingham Forest ta fitar da sanarwa inda ta ce "Awoniyi na samun sauƙi".

Sai dai an ga yadda aka samu wata ƴar rashin jituwa tsakanin mamallakin ƙungiyar Evangelos Marinakis da mai horas da ita Nuno Espirito Santo a cikin filin wasa jim kaɗan bayan kammala wasan a ranar Lahadi.

Bayan sukar abin da mamallakin ƙungiyar ya yi, Forest ta ce lamarin ya faru ne kasancewar Marinaki bai ji daɗin yadda Awoniyi ya ci gaba da wasa ba duk kuwa da raunin da ya samu.

Sanarwar ƙungiyar ta ce "Evangelo Marinakis bai ɗauki Nottingham a matsayin ƙungiyar ƙwallon ƙafa kawai ba, ya ɗauke ta a amatsayin wani ɓangare na iyalinsa - kuma yana ƙoƙarin ganin kowa ya yi amanna da hakan.

"Wannan ne ya sanya bai ji daɗin abin da ya faru ba a filin wasa na Leicester City a ranar Lahadi.

"Matakin da ya ɗauka ya kasance na nuna tsantsar kulawa da tallafa wa ɗaya daga cikin waɗanda ya ɗauka a matsayin nasa."

Wane ne Taiwo Awoniyi?

Taiwo Awoniyi (Hagu) tare da Joe Aribo a lokacin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka a 2021 a ƙasar Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Taiwo Awoniyi (Hagu) tare da Joe Aribo a lokacin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka a 2021 a ƙasar Kamaru

Taiwo Awoniyi ɗan asalin Najeriya ne wanda ke taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nottingham Forest da ke Birtaniya.

Awoniyi ya tafi Nottingham ne a watan Yunin 2022 daga ƙungiyar Union Berlin da ke Jamus.

Dan wasan mai shekara 27 ya fara wasan ƙwallon ƙafa ka'in da na'in ne a ƙaungiyar Liverpool a shekara ta 2015 kafin ya tafi wasu ƙungiyoyi a Jamus da Holland da kuma Belgium a matsayin aro.

Ɗan wasan na gaba ya taka wa Najeriya a gasanni daban-daban a matakai daban-daban kafin buga wa ƙasar a babbar ƙungiyarta ta Super Eagles.

Yana daga cikin tawagar Najeriya da ta yi nasara kan Libya a wasan neman gurbin gasar kofin nahiyar Afirka ta 2025.

Ɗan wasan na da aure da ɗa ɗaya.