Me ya rage wa Barcelona wajen lashe gasar La Liga ta bana?

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Bayan da Barcelona ta yi nasarar doke Real Madrid 4-3 ranar Lahadi a El Clasico a Estadio Olimpic, yanzu tana neman maki biyu ta lashe kofin La Liga na bana.

Barcelona ta ci gaba da zama ta ɗaya a teburin kakar bana da maki 82, yayin da Real Madrid mai maki 75 take biye da ita - kenan da tazarar maki bakwai tsakani.

Koci, Hansi Flick, wanda ya ɗauki Spanish Super Cup da Copa del Rey a kakarsa ta farko a Barcelona, na fatan haɗa maki biyu a sauran wasa ukun da suka rage a La Liga.

Damar farko da Barcelona ta samu

Ranar Laraba, Real Madrid za ta kara da Mallorca a Santiago Bernabeu, kuma da zarar ta kasa samun maki uku a ranar, Barcelona za ta lashe La Liga na bana na 28 jimilla na farko a wajen Flick

Idan kuma Real Madrid ta doke Mallorca, Barcelona za ta buga wasan hamayya da Espanyol, wadda da zarar ta ci karawar za ta lashe kofin na La Liga..

Idan har Barcelona ta ɗauki La Liga a Espanyol, zai zama karo na biyu da ta lashe kofin a gidan abokiyar hamayya bayan cin 4-2 a 2022/23.

Sai dai idan Barcelona ba ta samu damar ɗaukar kofin a Espanyol ba, za ta jira ranar Lahadi a karawar mako na 37 da za ta yi a gida da Villareal ranar 18 ga watan Mayu.

Idan haka ma bai faru ba, watakila Barcelona ta lashe kofin La Liga a filin wasa na San Mammes a karawa da Athletic Bilbao ranar Lahadi 25 ga watan Mayu.

Barcelona ta rasa kofin Champions League a kakar nan, bayan da Inter Milan ta fitar da ita a zagayen daf da karshe.

Wasa ukun da suka rage wa Barcelona a La Liga:

Spanish La Liga ranar Alhamis 15 ga watan Mayu

  • Espanyol da Barcelona

Spanish La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Mayu

  • Barcelona da Villarreal

Spanish La Liga ranar Lahadi 25 ga watan Mayu

  • Ath Bilbao da Barcelona