Ina De Bruyne zai koma idan ya bar Man City?

Asalin hoton, Getty Images
Rayuwar Kevin de Bruyne ta kusan shekara 10 a Manchester City na dab da kawo wa ƙarshe - to mece ce makomar ɗanwasan?
Ɗanwasan na Belgium mai shekara 33 a watan Afrilu ya sanar cewa zai tafi idan an kammala wasa
Zai tafi a matsayin ɗaya daga cikin ƴanwasa mafi shahara da aka taɓa gani a gasar Premier, inda ya ci kofi 16 tun da City ta ɗauko shi daga Wolfsburg a 2015.
Sai idan zai ƙara tsawaita kwangilar shi ta ɗan ƙaramin lokaci domin gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, amma ga alama wasa huɗu ta rage masa a Manchester City.
Ina ɗanwasan na tsakiya zai koma? zai tafi Amurka ne ko Saudiyya ko Turai ko kuma ritaya zai yi, BBC ta diba zaɓin da yake da shi.
Amurka
Ƙungiyoyin Amurka a gasar MLS zaɓi ne ga ɗanwasan na Belgium a wannan lokacin.
San Diego da Inter Miami na cikin ƙungiyoyin da suka nuna sha'awar ɗanwasan.
Zai iya haɗuwa da Lionel Messi da Luis Suarez a Inter Miami ta David Beckham
Sai dai kuma rahotanni sun ce wakilan De Bruyne za su gana da jami'an Chicago Fire ta Amurka.
Saudiyya
Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Sadio Mane - na cikin fitattun ƴanwasan da ke taka leda a ƙungiyoyin Saudiyya.
Daraktan wasanni na lig ɗin Saudiyya Michael Emenalo shi ya kawo De Bruyne a Chelsea a 2012, kodayake haskawa tara kawai ya yi a ƙungiyar
Wakilan De Bruyne a baya sun tattauna da ƙungiyoyin Saudiyya, don haka akwai yiyuwar zai iya tafiya Saudiyya.
Sai dai ana ganin zai fi son zuwa Amurka ko kuma ci gaba da zama a Turai maimakon Gabas Ta Tsakiya saboda iyalinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Zai iya amai ya lashe a Man City
De Bruyne na da farin jini a Manchester City musamman daga magoya bayan ƙungiyar .
Ya ƙara samun ƙauna a Etihas sakamakon ƙwallon da ya ci a ragar Wolves a ranar 2 ga Mayu.
"Na nuna zan iya ci gaba da taka leda a nan."
"Abokan wasa da dama sun yi min magana, sun nuna rashin jin dadinsu cewa zan tafi, amma haka rayuwa ta gada," in ji De Bruyne.
Kocin Manchester City Pep Guardiola da daraktan wasannin ƙungiyar ne suka ba De Bruyne damar tafiya, don haka akwai yiyuwar su sauya tunani.
De Bruyne na cikin waɗanda suka fi karbar albashi a Premier kuma da wahala City ta ƙara masa albashi domin neman ya tsaya.
Ritaya
Wasu masu sharhi na ganin De Bruyne zai iya yin ritaya idan ƙwangilar shi ta kawo ƙarshe a City.
Ɗanwasan shekarunsa 33 kuma duk da City ta ki sabunta kwangilar shi duk da akwai damar ya ci gaba da taka leda, hakan alama ce da ke nuna shekarunsa sun ja.
Zai iya kuma komawa taka leda a lig din da ba zai wahala ba inda kuma babu wani kalubale sosai domin neman zuwa gasar cin kofin duniya.











