Me ya sa ake ragargaje Man United a Premier amma take ƙoƙari a Europa League?

Harry Magiure

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Harry Magiure na cikin 'yanwasan da ke haskawa tawagar Man United ta gasar Europa League
Lokacin karatu: Minti 1

Ganin iriin halin da Manchester United ta shiga a gasar Premier League ta bana, za a iya munana mata zaton cewa ba za ta yi nasara ba a wasa na biyu da za ta buga da Athletic Bilbao a yammacin Alhamis.

Amma kuma idan aka zo gasar zakarun Turai, lamarin ya sha bamban.

Ita kaɗai ce ƙungiyar da ba ta yi rashin nasara ba cikin dukkan waɗanda ke buga gasar zakarun Turai uku a bana - a Champions League, da Europa League, da kuma Conference League.

Kazalika, United ɗin ce ta fi kowacce cin ƙwallaye a raga, inda ta zira 31 a kakar wasa ta bana a Europa.

Tsohon ɗanwasan Ingila da Manchester City Nedum kuma mai sharhin wasa a BBC, Nedum Onuoha, ya bayyana dalilan da suka sa Man United take sauyawa idan ta je gasar zakarun Turai ta Europa League a bana.

A kakar wasa ta 2002-03 (32) da ta 2020-21 (34) ne kawai ta ci fiye da haka a kaka ɗaya a wata babbar gasar Turai.

"Ba na ganin cewa Man United na sauya salo a wasannin zakarun Turai - kawai dai yanayin ƙungiyoyin da suke fuskanta ne. A Premier League, ƙungiyoyi sun gama sanin Man United ciki da waje.

"Dalili shi ne sukan haɗu sau biyu duk shekara. Sun san abin da za su tarar game da 'yanwasan United ɗin da kuma filin wasanta.

"A gasar zakarun Turai kuma, akasari wannan ne karon farko da suke zuwa filin wasa na Old Trafford da kuma karawa da United. Ba su san yadda ya kamata su tunkare su ba.

"Shi ya sa idan kulob ya ciyo ƙwallo uku a waje, abu ne mai wuya a ce bai yi nasara ba idan aka zo gidansa. Sun san cewa za su yi ƙoƙari a kan Bilbao.

"Tun da dai ba a kammala wasan ba, ba zai yiwu a ce Man United ta ci ba saboda wani abu zai iya faruwa."