Yadda aka kashe mutane fiye da 6,000 cikin kwana 3 a Sudan

Mutane da ke yin ƙaura daga birnin fled el-Fasher sun bi layin karɓar abinci.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Mutane da ke yin ƙaura daga birnin fled el-Fasher sun bi layin karɓar abinci.
    • Marubuci, Natasha Booty
    • Marubuci, Richard Kagoe
  • Lokacin karatu: Minti 3

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce an kashe mutane aƙalla 6,000 cikin kwana uku kacal, lokacin da mayaƙan RSF suka ƙwace iko a birnin el-Fasher na Sudan a shekarar da ta gabata.

Wani mutum da ya shaida yadda mayaƙan suka buɗe wuta kan mutane dubu ɗaya da ke neman mafaka a ginin wata jami'a a watan Oktoba, ya ce "yanayi ne muka gani kamar a cikin fim,"

Rahoton ya tattara bayanai kan kisan mutane da yawa da azabtar da mutane da sace wasu da kuma cin zarafin fararen hula ta hanyar lalata. Ya kuma jadadda cewa dukkan su laifukan yaƙi ne.

RSF ba ta yi tsokaci ba game da rahoton, amma a baya ta musanta irin wannan zargi.

Kimanin shekaru uku kenan ana gwabza yaƙi tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan RSF a Sudan. Yaƙin basasan ya kashe dubban mutane kuma ya tilasatawa wasu fiye da miliyan 13 yin ƙaura.

An riƙa amfani da salon cin zarafi ta hanyar lalata ga maza da mata da kuma ƙananan yara, a matsayin salon jefa tsoro a zukatan jama'a.

Daga mayaƙan RSF har dakarun Sudan, babu wanda ya tsira daga zargin aikata munanan laifukan yaƙi.

Amurka da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Right Watch sun yarda cewa mayaƙan RSF da ƙawayen su sun aikata kisan gilla kan ƙabilar Massalit da ke yammacin Darfur, da kuma sauran yankunan da Larabawa ke zaune, amma sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce lamarin ya zarce hakan.

El-Fasher, wani babban birni a Darfur ya faɗa yanayi na tsananin yaƙi har na tsawon watanni 18. Kuma a nan ne aka aikata munanan laifukan yaƙi ga jama'a.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutane fiye da 140 ne suka bayar da labarin ko dai yadda abin ya shafe su kai tsaye ko kuma yadda ya shafi wasu kuma ya faru a kan idon su, lokacin da ofishin kare haƙƙin ɗan Adam na Majlisar Dinkin Duniya ya tuntuɓe su a ƙarshe shekarar 2025.

Majlisar Dinkin Duniya ta ce a cikin kwanaki uku na farko da fara yaƙin a birnin el-Fasher, ''mutane aƙalla 4,400 aka kashe'' a cikin birnin, kuma an kashe wasu ''fiye da 1,600 a kan hanyar su ta guduwa daga birnin''.

"Babu shakka haƙiƙanin mutanen da aka kshe a yayin faɗan na da yawan gaske,'' in ji rahoton.

Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta Majlisar Dinkin Duniya Volker Türk, ya sake kira ga dukkan ɓangarorin biyu su kawo ƙarshen aika-aikan da mayaƙan su ke aikatawa.

Ƙasashen duniya na ci gaba da matsin lamba kan masu goyon bayan rikicin tare da kiran tsagaita wuta.

Haɗaɗɗiyar Dular Larabawa ta musanta zargin da ake ta yaɗawa cewa tana tallafawa mayaƙan RSF da makamai.

A makon da ya gabata, Birtaniya ta ɗauki matakin ladabtarwa kan wasu muhimman mutane shida da ta ke zarginsu da hannu kan ruruta rikicin Sudan, cikin su harda babban kwamandan rundunar sojin Sudan da kuma na RSF, da kuma baƙi ƴan ƙasar waje waɗanda ake zargi da ɗaukar sojoji haya ƴan Colombia.

Ƴan majalisar Birtaniya sun yi tsokaci a kai, inda bayan iƙirarin Majalisar Dinkin Duniya ana sayen kayan yaƙi daga Birtaniya, kuma daga ƙarshe a bai wa mayaƙan RSF.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya Yvette Cooper ƙasarsa na da tsauraran matakai kafin fitar makamai zuwa ƙasashen waje.

A woman looking at her mobile phone and the graphic BBC News Africa

Asalin hoton, Getty Images/BBC

Go to BBCAfrica.com for more news from the African continent.

Follow us on Twitter @BBCAfrica, on Facebook at BBC Africa or on Instagram at bbcafrica