Yaƙin Sudan: "jikin ɗana ya cika da tabon raunuka"

Ahmed Abdul Rahman kwance a kan bargo tare da bandeji a jikinsa.
    • Marubuci, Barbara Plett Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ahmed Abdul Rahman yana iya jin ƙarar bam daga inda yake kwance a cikin wasu tantuna da aka kafa a birnin el-Fasher na Sudan.

Wannan yaro ɗan shekara 13 ya sami rauni sosai daga harin bam na baya-bayan nan. "Ina jin zafi a kaina da ƙafafuna," in ji shi.

Tsawon watanni 17 kenan da dakarun RSF suka mamaye birnin el-Fasher, birnin da ke tsakiyar yankin Darfur, kuma yanzu suna dannawa zuwa kusa da wasu mahimman wuraren soja a birnin.

Rikici ya ɓarke ne a Sudan tun a shekarar 2023 sakamakon taƙaddama tsakanin manyan kwamandojin RSF da sojojin Sudan.

Bayan rasa iko da birnin Khartoum, dakarun na RSF sun ƙara ƙaimi wajen ƙwace el-Fasher, wanda shi ne wuri nsa ƙarshe a yammacin Darfur da ke hannun sojojin ƙasar.

Yanƙin da sojoji ke riƙe da shi yanzu ya rage wani ƙaramin yanki kusa da filin jirgin sama.

Kowace rana cike take da wahala ga dubban fararen hula da suka maƙale cikin birnin.

Samun sahihan labarai ya yi wuya saboda rikicin da ke faruwa, amma BBC ta yi aiki tare da ƴanjarida masu zaman kansu a cikin el-Fasher don gano yadda rayuwa ke tafiya.

Mahaifiyar Ahmed, Islam Abdullah, ta ce: "Jikinsa cike yake da raunukan bindiga.

Babu tabbas go zai ci gaba da ruyuwa duba da halin da yake ciki saboda asibitoci na fuskantar hare-hare kuma kayan aiki na ƙarewa, samun kulawar lafiya ta yi wuya."

A kusa da shi, akwai wata yarinya Hamida Adam Ali, ita ma ba ta iya motsawa saboda raunin da ke ƙafarta.

Sai da ta kwana a titi na tsawon kwanaki biyar bayan harin bam ɗin da ya raunatata, kafin aka kai ta sansanin 'yan gudun hijira.

"Ban san ko mijina ya mutu ko yana raye ba," in ji ta. "ƴaƴanba kodayaushe suna kuka saboda yunwa''.

Wani lokaci suna samun abinci, wani lokaci kuma suna kwanciya ba tare da cin abinci ba.

Kafata tana ruɓewa kuma tana wari. Ni dai kawai ina kwance ne, ban da komai."

Hamida Adam Ali
Bayanan hoto, Hamida Adam Ali da ƴaƴanta sun tsira daga mutuwa, amma ba ta san makomar mijinta ba.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƴan makonnin nan, dakarun RSF sun samu ci gaba sosai.

Sun fitar da hotuna da bidiyo da ke nuna mayaƙansu a wani wuri da BBC ta tabbatar cewa shi ne hedkwatar rundunar sojojin da ke kula da tankokin yaƙi.

Akwai wasu sansanoni kusa da wannan wuri ciki har da wani sansanin sojojin ƙasa, da sojojin Sudan har yanzu ke ƙarewa.

A kwanakin baya, sojoji sun saki bidiyo suna murna da isowar kayan agaji masu muhimmanci da ake kawo su ta jiragen sama.

Amma kuma a cikin jaridu da ke ɗauke da labaran waɗannan yaƙe-yaƙe, mayaƙan RSF ɗin suna murnar abin da suke nunawa a matsayin nasara a el-Fasher.

Samun cikakken iko da birnin zai ba su babbar fa'ida a cikin yaƙin basasar da aka daɗe ana fama da shi ba, musamman bayan koma bayan da suka fuskanta a farkon wannan shekara.

Wannan zai sauƙaƙa musu samun damar zuwa Libya da kuma ƙarfafa ikonsu kan iyakar yammacin Sudan daga Kudancin Sudan zuwa wasu sassan Masar, in ji wata masaniyar Sudan, Kholood Khair, ga BBC.

Ta ce: "RSF za su iya kawo mai daga kudancin Libya da makamai ma daga kudancin Libya, kuma za su iya tsare hanyoyin su daga iyaka har zuwa Darfur. Daga el-Fasher, RSF za su iya kai hare-hare zuwa yankunan Kordofan da kuma babban birnin ƙasar, Khartoum. Wannan zai ba su ƙarfi sosai a fannin soji."

Ƙungiyoyin makamai na gida da aka sani da dakarun haɗin gwiwa, waɗanda ke tare da sojojin gwamnati, ma suna da abubuwa da yawa a za su rasa.

Ci gaban RSF yana samun ƙarfin gwiwa ne daga amfani da jaragen yaƙi marasa matuƙa da fasaha sosai, waɗanda ake cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ce ta samar musu, kodayake ta musanta wannan iƙirarin

Hotunan da BBC ta tabbatar suna nuna yadda aka harba jiragen yaƙi marasa matuƙa a wani wuri kusa da sansanin soja.

Sansanin ƴan gudun hijira
Bayanan hoto, An tilasta wa miliyoyin mutane tserewa daga gidajensu saboda yaƙin basasa a Sudan.

A watan da ya gabata, fiye da mutum 75 ne suka mutu a harin da aka kai a masallaci yayin da masallata ke sallar asuba, wanda ake zargin RSF ne suka kai harin, duk da cewa ba su ɗauki alhakin kai harin a fili ba.

Masu ceto ba su samu gawawwakin kowa ba.

Samah Abdullah Hussein ta ce an binne ɗanta Samir a kabarin bai ɗaya yayin da kuma yayansa rauni ya samu.

"An buge shi da ƙarfi a kai abin da ya bashi rauni mai zurfi, kwakwalwarsa ta fashe daga bugun." in ji ta, tana goge hawaye.

"Dayan ɗan nawa kuma ya ji rauni a kai da hannu, ni kuma an buge ni a kafata ta dama."

Dubban mutane sun tsere daga el-Fasher a shekarar da ta gabata, yayin da waɗanda suka tsira suka ce mutane na fuskantar hari da sace-sace da kisa a hanyarsu ta gudu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi kan samun ƙarin munanan yanayi idan har RSF suka ƙwace birnin gaba ɗaya.

Jami'an tsaro suna ƙaryata cewa suna kai hari kan ƙabilu da ba Larabawa, irin su al'ummar Zaghawa duk da hujjojin laifukan yaƙi da Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka gabatar.

Suna ƙoƙarin aika saƙo daban tare da sabbin bidiyo da ke nuna suna gaisawa da taimaka wa waɗanda suka tsere.

Wani ɗan gudun hijira ya ce ganin bidiyon ya girgiza shi, saboda ya gane mutane da yawa ciki har da danginsa. "Abin ya girgiza ni sosai, har sai na samu labarin cewa sun tsira," in ji shi.

Mutane da yawa suna tsoron abin da makonni masu zuwa za su kawo, yayin da waɗanda suka maƙale a birnin ke jiran tsira ko kai musu ɗauki.