'Na yi fatan kada na haifi jaririna'

Asalin hoton, AFP/Getty Images
- Marubuci, باربرا بليت آشر
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, مراسلة بي بي سي لشؤون أفريقيا
- Lokacin karatu: Minti 5
A watan Mayun da ya gabata ne Amira ta yi wata tafiya mai cike da hatsari zuwa ɗaya daga cikin wuraren da yaƙi ya yi ƙamari a Sudan.
A yanzu haka mayaƙan RSF sun ƙwace iko da garin da take zaune, Nahud da ke jihar Yammacin Kordofan.
Hanyar cike take da hatsari, amma ta rasa wani zaɓi face binta, a lokacin tana da cikin wata bakwai.
"Babu asibitoci masu yawa babu ɗakunan shan magani, na ji fagabar cewa ba zan samu motar da a ta ɗauke ni daga garinmu ba, idan har na jima a cikinsa. Tafiyar ta zo min bagatatan, cikin wahala ga kashe kuɗi ," Amira said.
Yaƙi tsakanin dakarun Sudan da mayaƙan RSF ya yi sanadin rayukan fararen hula masu yawa. A yanzu yakin ya koma kudancin yankin Kordofan, inda Amira ta tsallake.
BBC ba ta yi amfani da sunanta na ainihi ba saboda kareta.
A lokacin da take kan hanyarta ta guduwa, Amira ta naɗi sautin wasu abubuwa da suka faru, wanda ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama na Avaaz ya kunna wa BBC.
Mun kuma tuntuɓeta ta waya yayin da take Kampala, babban birnin Uganda, inda take jiran haihuwa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bulaguron Amira cike yake da wahalhalu tun daga farko.
Amira ta ce mayaƙan RSF da ƙawayensu ne ke iko da duka hanyoyin zirga-zirga.
A lokacin da ta shiga babbar mota ita da mijinta domin fita daga Nahud, sai faɗa ya ɓarke tsakanin wani matashi - da ya ɗauki shatar mota wa iyalansa - da kuma wani dieba wanda mayaƙin RSF ne da ya riƙa loda fasinjoji cikin motar.
"Nan take direban ya zaro bindigarsa, inda ya yi barazanar harbin matashin da ya ɗauki shatar motar,'' a cewar Amira.
Ta ƙara da cewa nan take aka riƙa bai wa direban haƙuri ciki har da sauran mayaƙan RSF ɗin da ke wurin.
"Kakar matashin da mahaifiyarsa suka riƙa kuka , durƙushe a kasa suna roƙon wannan direban kada ya harbi yaron. Mu fasinjoji mun shiga tashin hankali saboda fargaba,'' in ji Amira.
"Ina jin cewa ya yi tunanin cewa idan ya yi harbi, to zai harbi mutane da dama, saboda yana cikin maye bayan shan wiwi.''
Daga ƙarshe direban ya haƙura bai yi harbin ba, amma matashin bai samu shiga motar ba, don haka ya ci gaba da zama a Nahud.
Babbar motar da su Amira ke cii da sauran gomman fasinjoji ta samu barin Nahud, tare da kama wata mummunar hanya mai cike da ramuwa, yayin da take maƙare da jakankunan mutane da fasinjoji kimanin 70 zuwa 80, ciki har da tsofaffi da masu shayarwa da masu juna biyu, duk a yunƙurin tseratar da kansu da kuma yaransu.
"A tsarace nake har muka isa inda za mu je," a cewar Amira. "Na yi ta addu'ar kada naƙuda ta kamani, tare da fatan komai ya zama daidai.

Asalin hoton, Amira
Daga ƙarshe matafiyan sun isa Al-Fula, babban birnin jihar Kordofan ta Yamma. Amma Amira ba ta so ta cigaba da zama a wurin, domin sojoji na tunƙarar yankin.
"Ban san me zai faru ba idan sojojin suka isa Al-Fula, musamman idan sojojin suka fara kai farmaki kan mutanen da suka fito daga wasu ƙabilu da ake tunanin suna da alaƙa da RSF, kamar ƙabilun Baggara da Rizeigat,'' kamar yadda Amira ta bayayna cikin sautin da ta naɗa.
Amira ta ci gaba da cewa, "Mijina a ɗan ɗaya daga cikin waɗannan ƙabilun ne, kodayake ba shi da alaƙa da RSF. Ma'aikacin gwamnati ne, wanda ya karanci fannin shari'a, amma hakan ba zai kuɓutar da shi ba, a yanzu ana far wa mutane kawai saboda ƙabilanci''.
Ana zargin sojojin Sudan da dakarun sa-kai da ke kawance da su da cin zarafin fararen hula da suke zargi da haɗa baƙi da dakarun RSF a yankunan da suke iko da su, a wani abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin "rahotanni kisan gilla masu inganci.
A baya dai sojojin Sudan sun yi Allah wadai da cin zarafi da wasu sojojin ƙasar suka aikata, lokacin da ake zarginsu da take hakkin ɗan'adam.
Babban jagoran sojin ƙasar, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya kafa wani kwamiti a farkon wannan shekarar domin binciken cin zarafi da aka yi a lokacin da sojoji suka mamaye tsakiyar Sudan.
Kordofan, wanda ya ƙunshi jihohi uku, ya zama cibiyar filin daga. Yankin na da matuƙar muhimmanci a yaƙin Sudan, domin yana ɗauke da manyan rijiyoyin mai, kuma shi ne muhimmin yanki game da hanyoyin sufuri.
Bayan barin Al-Fula, Amira ta kwashe kwana uku tana tafiya a motoci daban-daban, har lokacin da ta isa kan iyakar Sudan ta Kudu wuri mai aminci.
"Direbobin RSF na aiki yadda suka ga dama," in ji ta.
"Su ke zaɓar wanda zai hau musu mota, da inda zai zauna, da abin d za su biya. Babu takamaikan kuɗin mota, dole ku biya duk abin da suke yanke. Mutanen na da makamai saboda ba tashin hankali suke gudu ba.''
Ta ƙara da cewa akan tsayar da motar duk bayan kamar miti 20 a shigayen binciken abababen hawa da RSF suka kafa, tare da tilasta musu biyan kuɗi ga dkarun da ke kan shingayen.
Duk kuwa da cewa fasinjojin na tare da mayaƙan na RSF waɗanda suka riga suka biya kuɗi.
Abinci na da matuƙar tsada, ga ƙarancin ruwan sha.

Asalin hoton, Amira
A ƙauyen Al-Hujayrat, matafiya sun sami sadarwar intanet ta hanyar na'urar Starlink mallakar rundunar RSF, duk kuwa da cewa yin hakan na da hatsari.
Amira ta ce "da zarar ka shiga intanet, to fa sai ka yi kaffa-kaffa." "Idan membobin RSF sun ji kuna kallon bidiyon sojoji, kuna kunna sautin waƙar soja, ko ambaton RSF a hankali yayin tattaunawa, za su kama ku."
Titunan ba su da kyau sosai, kuma ababen hawa sun yi matuƙar lalacewa. Sau uku motar da Amira ke ciki na tsayawa a hanya.
Lokacin da Amira ta shiga mummunan tashin hankali shi ne lokacin da tayar motarta ta fashe a lokacin da suka shiga dajin ƙirya, inda fasinjojin suka maƙale ba tare da ruwan sha ba. Direbobin da ke wucewa sun ƙi tsayawa su taimake shu.
"Wallahi na ji kamar ba zan iya zuwa wani wuri ba, cewa zan mutu a can," in ji Amira.
"Na riga na saduda, bargo kawai nake da shi, na ɗauka na kwanta a ƙasa," "Ran nan na ji kamar zan mutu a wurin."
Amma hakan bai yiwuwa, daga karshe Amira da mijinta suka samu shiga wata karamar mota dauke da kayan lambu.

Asalin hoton, Amira
Washegari, suka isa Abyei a kan iyaka, amma tafiyar ta samu jinkiri saboda ruwan sama da ambaliya.
A wannan lokacin suna cikin wata motar da ke ɗauke da gangunan mai, motar ta ci gaba da tsayawa.
"Motar ta ci gaba da nutsewa cikin laka," in ji Amira.
"Tafafinmu sun jiƙe, haka ma jakunkunanmu, ƙura da zafi sun yi mana yawa''.
"Muna cikin sanyi muna addu'ar Allah ya kaimu."
Daga ƙarshe ma'auratan sun isa Juba, babban birnin Sudan ta Kudu, mai tazarar kilomita 1,300 kudu da Nahud, kuma daga nan ne suka shiga motar bas zuwa babban birnin Uganda.
Yanzu da na samu lafiya, kwanciyar hankali na da daci.










