'Sojojin Sudan na azabtar da fararen hula'

Wani soja ya na tafiya shi kaɗai a kan wata gada. Akwai motocin da suka ƙone da kuma ɓaraguzan gine-gine a warwatse a kan gadar.

Asalin hoton, Avaaz via Getty Images

Bayanan hoto, Birnin Khartoum ya zama tamkar kufai a lokacin da sojoji suka sake ƙwace iko da shi a watan Maris
    • Marubuci, Wedaeli Chibelushi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Marubuci, Will Ross
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Wata fitacciyar ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama a Sudan ta zargi sojoji da sauran jami'an tsaron ƙasar da azabtar da mutane har lahira da kuma gudanar da wuraren da suka kira "zaurukan kisa".

Ƙungiyar mai suna ''Emergency Lawyers group'' ta ce ta tattara bayanan kamen da aka yi wa ɗaruruwan mutane a Khartoum babban birnin ƙasar. Ta ce a cikin lamuran da suka fi "muni", su ne inda aka gano gawawwakin wasu wadanda aka kama inda bincike ya kuma nuna cewa an azabtar da su.

Sojojin Sudan sun ƙwato birnin daga hannun dakarun RSF a cikin watan Maris, ƙungiyar da suka kwashe shekara biyu suna gwabza ƙazamin yaƙin basasa da ita, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Rundunar sojin ƙasar dai ba ta ce uffan ba a lokacin da BBC ta nemi jin ta bakinta.

Yayin da yaƙin ke ci gaba da gudana ƙungiyar ta ''Emergency Lawyers group'' ta tattara bayanan ayyukan cin zarafi daga ɓangaren sojoji da kuma na RSF.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a dandalin sada zumunta na X, ƙungiyar ta ce ta lura da yadda ''ayyukan cin zarafi ke ƙara muni''.

Ƙungiyar ta yi zargin cewa an kama wasu fursunonin inda aka kai su waɗansu manyan wuraren da aka keɓe domin tsare mutane.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, "Sun fuskanci abubuwan da suka shafi ci gaba da tsare su cikin mummunan yanayi da kuma shari'o'in da hukumomin tsaro ke yi waɗanda ba su wani kwatankwacin adalci, ko kuma waɗanda ake sakowa cikin halin rashin lafiya," in ji sanarwar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"A cikin lamuran da suka fi muni, akwai gawarwakin waɗanda aka kashe ko kuma aka bayyana su a matsayin sun mutu sakamakon azabtarwa."

An saba amfani da azabtarwa a lokacin mulkin danniya na shugaba Omar al-Bashir.

A tsawon yaƙin da har yanzu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, an gano cewa ita ma rundunar RSF ta cin zarafin fursunoni inda har ta kai ga kashe wasu daga cikinsu.

Wata tawaga mai zaman kanta ta a Sudan ta bayyana a cikin watan Maris cewa dukkanin ɓangarorin biyu na da alhakin "yawaita kama mutane da tare da wani dalili ba da azabtar da su da kuma musgunawa waɗannan fursunonin".

Ta ce da RSF da sojoji sun yi amfani da "fyade da sauran nau'ikan cin zarafi masu nasaba da jima'i da kama mutane da tsare su ba bisa ƙa'ida ba, da kuma azabtarwa da musgunawa".

Yaƙin da aka gwabzawa ya haifar da ɗaya daga cikin rikicin jin-kai mafi a duniya - an tilastawa mutane miliyan 12 barin gidajensu da kuma ayyana matsananciyar yunwa a sassan ƙasar.

A makon da ya gabata ƙungiyar likitocin nan ta 'Doctors Without Borders ' (MSF) ta ce yaƙin ya haifar da ɓarkewar cutar kwalara mafi muni da ƙasar ta fuskanta cikin shekaru da dama.

An samu kusan mutane 100,000 da suka kamu da cutar inda hakan kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2,470 a cikin shekarar da ta gabata.