Wane ne ke da alhakin kashe-kashe da ake ganin ya fi muni a yaƙin Sudan?

Asalin hoton, X
- Marubuci, Mohammed Mohammed Osman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- Lokacin karatu: Minti 4
Gargaɗi: Wannan rubutun na tattare da wasu bayanai masu tayar da hankali.
Da wani manomi mai shekara 40 Ali Ibrahim yake bayyana lamarin, ya ce rikicin ya fara da yammacin ranar 5 ga Yuni, inda suka fara jin harbe-harbe.
"Ba mu taɓa ganin irin waɗannan harbe-harben ba tun muna ƙananan yara. Sai da aka kwashe sa'a huɗu ana jefa bama-bama, inda aka tarwatsa gidaje, yara da mata suna ta koke-koke, ga dattawa da ba za su iya guduwa ba."
Aƙalla fararen hula 100 aka kashe a ranar a ƙauyen Wad al-Nourah, kamar yadda ƙididdigar ƴan sa kai ya nuna.
Ali ya ce mutanen ƙauyensu ba su makamai: "Mu manoma ne kawai ba mu taɓa riƙe makamai ba. Ba mu da maƙiya a iya saninmu."

Asalin hoton, X
BBC ta samu jin ta bakin waɗanda suka tsira da dama, inda suka zargi dakarun RSF da harin ta hanyar amfani da miyagun makamai.
Adadin waɗanda aka kashe shi ne mafi yawan da aka kashe fararen hula a cikin ƙanƙanin lokaci tun bayan ɓarkewar yaƙin tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF a Afrilun 2023.

BBC ta samu zantawa da wasu da suka tsira da raunuka da suke jinya a asibitin gwamnati na Al Managil, inda suka bayyana wasu hotuna da bidiyoyi.
Asibitin yana da nesan kilomita 80 ne daga ƙauyen, sannan waɗanda suka tsiran sai da suka ɗauki sa'o'i kafin suka isa asibitin. Kamar yadda ƴan ƙauyen suka bayyana, dakarun na RSF sun yi yunƙurin hana fita daga ƙauyen barin harin, sannan sun sace musu ababen hawansu.

Wayewar gari da hari
Bayan awanni ana jefa musu bama-bamai da kuma wahalar birne gawarwakin waɗanda suka mutu da kuma kai waɗanda suka ji rauni asibiti, ƴan ƙauyen sun sake shiga ruɗu inda a washegari suka wayi gari da wani harin daga dakarun RSF, kamar yadda Nisreen, wata matar aure ta bayyana wa BBC a asibiti.
"Sun shigo gidanmu, suka min duka da ƴanuwana, sannan suka tambaye mu ina zinarenmu? ƙanwata ta ruɗe ta ce mahaifiyarmu ta ba su zinaren - wanda ya kai darajar biliyoyin fan na Sudan." (Dalar Amurka 1 na daidai da fan 2600 na Sudan.)
Bayanan Nisreen ya yi daidai da na sauran waɗanda suka tsira, inda dukkansu suka tabbatar da cewa dakarun RSF ne "suka kawo mana hari a ƙauyenmu, suka shiga gidajenmu, suka kashe fararen hula, sannan suka mana sata ciki har da zinare da kayayyakin abinci."
'Sun kashe min ɗan uwa'
Hamad Suleiman wani tireda mai shekara 42 ya ce dakarun RSF sun shiga gidansu suka fara harbe-harbe.
"Na je gidan ɗan uwana na same su a can, nan suka kashe ƴanuwa biyu, sannan wani ya samu rauni, yanzu muna tare da shi a nan asibiti."
"Sai na tambaye su me ya sa suka kashe shi, sai suka ce wai ai sun yi kalmar shahada, sai suka harbe ni a hannu suka tafi... amma sun sace mana motoci."

'Al Mustanfaron'
BBC ta tuntuɓi dakarun RSF domin jin ta bakinsu a game bayanan waɗanda suka tsira ɗin da zarginsu da kai harin da kashe-kashe da sace-sace, amma ba mu samu wata amsa ba har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.
Kakakin dakarun RSF, Al-Fateh Quraishe ya fitar da wani bidiyo a shafin X washegarin harin, inda ya ƙaryata hannun dakarun a kashe fararen hula.
Ya ce dakarun sun fafata da sojojin Sudan ne da masu leƙen asirinsu waɗanda ake kira 'Al Mustanfaron'.
Wajen ƙauyen
Sashen bin diddigi na BBC ya yi nazarin bidiyoyin da RSF suka fitar, wanda suka ce suna nuna hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da Al Mustanfaron ke amfani da su Wad al-Nourah. Sai dai nazarin bidiyoyin ya nuna cewa wuraren da suka bayyana ba a cikin ƙauyen suke ba.
Haka kuma bidiyoyin sun nuna yadda dakarun na RSF suka kusta cikin ƙauyen ɗauke da miyagun makamai suna harbe-harbe.
Wad al-Nourah kamar sauran ɗaruruwan ƙauyuka ne da suke jihar Gezira. Yawancin ƴan ƙauyen manoma ne sai kuma kasuwar da suke ci.
Dakarun RSF sun mamaye jihar Gezira a Kudancin Khartoum ne a watan Disamban 2023, kuma ana zarginsu da cin zarafin fararen hula - wanda suka daɗe ƙaryata.
Tun bayan da RSF suke karɓe iko da yankin a Disamban bara, ƙauyuka da dama suna fama da matsalolin hare-hare.
Buƙatar a gudanar da bincike

A cewar rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya, yaƙin Sudan ya kashe sama da mutum 14,000, sannan ya raba kusan mutum miliyan biyu da gidajensu tun bayan watan Afrilun bara.
Koodinetan ayyukan jin ƙai na MDD a Sudan, Clementine Nkweta-Salami ya yi kira da a gudanar da bincike domin gano asalin abin da ya faru a ƙauyen na Wad al-Nourah.
Ƴan ƙauyen, waɗanda suka rasa gomman ƴanuwansu suna fata za a kafa kwamitin bincike, sannan za a hukunta waɗanda aka samu da laifi.
Akwai ƙarin rahoto daga Abdelrahman Abutaleb da Richard Irvine-Brown






