Jami'an tsaro sun yi nasarar kashe ƴanbindiga a jihar Katsina

KATSINA STATE GOVERNOR

Asalin hoton, UMAR DIKKO RADDA/FACEBOOK

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Katsina dake arewacin Najeriya ta ce rundunar haɗin gwiwa ta jami'an tsaro a jihar ta yi nasarar kashe ƴanbindiga 18 a yankin ƙaramar hukumar Dutsinma, yayin da ɓarayin dajin suka afkawa wasu ƙauyuka.

Gwamnatin ta ce an samu wannan nasarar ne a Jiya asabar, bayan samamen da jami'an tsaro suka kai, sakamakon bayanan sirri da suka samu a kan ayyukan ƴan bindigar.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida na jihar Katsina, Dr Nasir Muazu, ya ce an kuma samu nasarar anso shanu da sauran dabbobi wadanda ke ƙarƙashin kulawar gwamnati, "an kuma samu bindiga AK47 harsashi 11."

Dr Nasiru Muazu dai ya ce an samu sauƙin matsalar tsaro wasu ƙananan hukumomi idan aka kwatanta da inda aka baro.

Ko a kwanakin baya a cikin wata tattaunawa da gwamnan jihar ta Katsina,Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya yi da BBC ya ce kwalliya ta fara biyan kudin sabulu kan kiraye-kirayen da suke yi wa jama'ar jiharsa na tashi tsaye wajen kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga.

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya ce kawo akwai garuruwa da dama a jiharsa da 'yan bindigar basa marmarin shiga, saboda matakan kare kai da mazaunansu suka ɗauka.

Hakan kuma ya ce ba wai suna kira ga al'umma su tashi su ɗauki makami ba ne, sai dai don su kare kansu, saboda jam'an tsaron da ake da su a Najeriya ba za su iya kare 'yan Najeriya ba saboda sun yi kaɗan.

Gwamnan ya yi bayanin cewa Ya yi sabbin dabarun da gwamnati ta ɓullo da su sun taimaka sosai wajen kawar da masu bai wa ƴan bindigar bayanan sirri, waɗanda da ma can masana a fannin tsaro ke cewa su ne babbar illa a yaƙi da masu garkuwa da mutane.

Gwamnan ya ce an kama mutane da dama masu bayar da bayanan sirri ga ƴan bindigar kuma bincike ya tabbatar cewa suna da hannu dumu-dumu a wannan ɗanyen aiki.

Ko a baya-baya nan an riƙa gani wasu bidiyo na wasu mutane da ke iƙirarin suna bayar da bayanai ga ƴanbindiga a lokacin da jami'an sa kai na gwamnatin jihar ke tattaunawa da su.

Matsalar rashin tsaro dai ta yi matuƙar ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya kuma duk da nasarorin da jami'an tsaro suke cewa suna samu wurin kawar da manyan ƴan bindiga har yanzu mazauna wannan yankin ba su kasance cikin kwanciyar hankali ba sakamakon hare-haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa a yankunan