Abu uku Najeriya za ta yi ta ga ƙarshen 'yan fashin daji cikin ɗan lokaci - Radda
Gwamnatin Najeriya na iya kawo ƙarshen hare-haren 'yan fashin daji cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, matuƙar ta tashi tsaye ta aiwatar da wasu muhimman abubuwa guda uku.
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da rikicin 'yan fashin daji, masu kai hare-hare a kan babura tare da satar mutane don neman kuɗin, ne ya bayyana haka lokacin wata zantawa ta musamman da BBC.
Ya ce matuƙar aka shigar da mutanen da rikice-rikicen ya fi shafa, sannan aka ƙara ɗaukar ɗumbin jami'an tsaro kamar sojoji da 'yan sanda aiki, ba shakka nesa ta zo kusa ga wannan rikici.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kuma ce akwai buƙatar samar da ƙarin kayan aiki ga hukumomin tsaro musamman ma dai sojoji ta yadda za su iya tunkarar ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama da shi.
"Yanzu in ka kalli duka hwaɗin Najeriya, da ɗan sanda da sibi defes da soja, har yanzu ba su kai miliyan ɗaya ba a ƙasar da muke da ya fi mutum miliyan 200.
"Ka ce su za su kare wannan ƙasar, ina ga kamar ba a hau hanyar da ta kamata a hau ba," in ji Gwamna Dikko Raɗɗa.
Ku kalli bidiyon a sama don ganin cikakkiyar wannan hira.



