Jama'a sun fara tashi tsaye don kare kansu daga ƴan bindiga - Dikko Radda

Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda

Asalin hoton, Umar Dikko Radda

Bayanan hoto, Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya ce kawo yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu kan kiraye-kirayen da suke yi wa jama’ar jiharsa na tashi tsaye wajen kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya ce kawo yanzu akwai garuruwa da dama a jiharsa da ‘yan bindigar basa marmarin shiga, saboda matakan kare kai da mazaunansu suka ɗauka.

Hakan kuma ya ce ba wai suna kira ga al’umma su tashi su ɗauki makami ba ne, sai dai don su kare kansu, saboda jam’an tsaron da ake da su a Najeriya ba za su iya kare ‘yan Najeriya ba saboda sun yi kaɗan.

Dikko Raddan ya ce Abun da muka ce da mutane shi ne su bamu matasansu mu basu horo, mu basu abubuwa da zasu iya bayar da tsaro ga kawunansu, kafin jami’an tsaro su kawo musu dauki” inji shi.

Sai dai wasu na ganin cewar a duk lokacin da gwamantoci suka fara kiran jama’a su fara kare kansu, tamkar sun gaza ne.

Sai dai gwamna Raɗɗa ya ce ko kaɗan ba haka lamarin yake a wajensu ba, illa ma abun da suke ta fada tuntuntuni shine cewar jam’ain tsaron Najeriya sun yi kadan wajen bayar da tsaron da ya kamata ga al’umma, shi yasa suka kafa rundunar tsaro ta Katsina Community Watch, don taimaka wa jami’an tsaron da ke jihar.

A wasu lokutan kuma akan zargi jami’an wannan rundunar tsaro ta Katsina Community Watch da gwamna Raɗɗan ke cewar sun kafa da cin zarafi ko wuce gona da iri a yayin da suke aiki.

Raɗɗan ya ce “Mu dai a Katsina mun shirya ƙa’idoji, kuma akwai tsarin doka da muka shimfiɗa kan yadda za su tafi da aikinsu, dukkan abu da ake yi a kan doka ake yinsa. Amma dama rahoton cin zarafi ba a kan jam’anmu kadai aka fara shi ba, an yi wa sojoji, an yi wa yan sandan kuma abin da za mu lura shi da shi shi ne ai jama’a ake yi wa aikin” inji shi.

Haka kuma ya ce “Duk sanda muka samu ƙorafi muna bincikawa, yanzu haka akwai jami'inmu da muka kama kan wani laifi da ya ake zargin ya aikata, yana can zai fuskanci shari’a duk inda muka kama muna daukar mataki amma duk inda ba mu samu ba kin ga zargi ne kawai, ya kamata a sani abun nan da ake yi na yaƙar yan ta’adda shi ma yana yaƙarka” inji gwmanan jihar ta Katsina.

Matsalar rashin tsaro dai ta yi matuƙar ƙamari a yankin arewa maso yammacin Najeriya kuma duk da nasarorin da jami'an tsaro suke cewa suna samu wurin kawar da manyan ƴan bindiga har yanzu mazauna wannan yankin ba su kasance cikin kwanciyar hankali ba sakamakon hare-haren da ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa a yankunansu.