'Dalilin da ya sa muka rufe makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar Katsina'

Asalin hoton, Katsina State Government
Gwamnatin jihar Katsina a arewacin Najeriya ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun koyar da kiwon lafiya masu zaman kansu nan take a faɗin jihar.
A cewar gwamnatin, an ɗauki matakin ne sakamakon yadda aka samu wasu makarantun da yawa marasa rajista, kuma suke da ayar tambaya game da yadda suke gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan Lafiya Musa Adamu Funtua ya faɗa wa BBC cewa sun gano makarantun da yawa da ba su cika ƙa'ida ba.
"Kwamati zai duba ya ga waɗanda suka cika ƙa'ida da waɗanda ba su cika ba tun daga wajen buɗe su," in ji shi.
A baya-bayan nan, an samu ƙaruwar makarantun horar da ungozomomi da ma'aikatan jinya masu zaman kansu a jihohin Najeriya da dama, duk da cewa suna da tsada sosai.
Hakan na faruwa ne yayin da na gwamnati ba su iya ɗibar ko rabin ɗaliban da ke fita daga sakandare duk shekara.
A watan Yulin 2022 ma gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya 26 da ba su da ta ce ba su da lasisi, tana mai cewa wasu daga cikin makarantun ba su da mazauni na dindindin.
Sauran zarge-zargen da gwamnatin Kanon ta yi sun ƙunshi koyar da wasu kwasa-kwasai da suka saɓa da manhajar kiwon lafiya, tare da tatsar ɗalibai da iyayensu maƙudan kuɗaɗe na babu gaira-babu-dalili.
'Matakan da muke ɗauka a Katsina'
Tun da farko mai bai wa gwamnan Katsina shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya faɗa wa manema labarai ranar Litinin cewa makarantun za su ci gaba da zama a rufe har sai an kammala bincike.
Ya kuma nemi shugabannin makarantun da su gabatar da takardun da suka dace domin tantancewa tsakanin ranakun Alhamis zuwa Juma'a.
BBC ta tambayi kwamishinan lafiya ta yadda za su tabbatar hakan bai shafi karatun ɗaliban da suka yi rajista a makarantund da suka cika ƙa'ida ba, sai ya ce:
"Ba zan so in faɗi adadin kwanaki ba, amma dai ina ba ka tabbacin aikin nan an fara shi kuma ba zai tsaya ba," a cewar Musa Adamu.
Ya ƙara da cewa: "Koke ne ya yi yawa ta yadda abin ya zama kamar ruwan dare. Ba wai hana su aiki aka yi baki ɗaya ba, kawai dai so ake su bi ƙa'ida."
Gwamnan Katsina Dikko Radda ya kafa kwamitin tantance makarantun ƙarƙashin jagorancin Umar Mammada.











