Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda hare-haren Amurka suka kasance a Sokoto da Kwara
Tun bayan wallafawar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi a shafinsa na Truth Social cewa sun kai hari kan ƴan kungiyar IS a Najeriya, ƴan ƙasar ke ta yin tambayoyi dangane da haƙiƙanin abin da ya faru.
BBC ta bi diddigi inda ta haɗa bayanai daga wuraren da abin ya faru da kuma wasu majiyoyi na gwamnati da waɗanda wasu jaridun ƙasar suka rawaito amma waɗanda suka tabbata.
Bayanai sun nuna cewa an kai harin ne a ƙananan hukumomin Tangaza da Tambuwal da ke Sokoto, arewa maso yammaci da Offa da ke Kwara a arewa ta tsakiyar Najeriya.
Makami mai linzami daga Ghana
Bayan harin na yammacin ranar Alhamis, Ma'aikatar tsaron Amurka ta wallafa wani taƙaitaccen bidiyo da yake nuni da yadda aka harba makami mai linzami daga wani jirgin yaƙi.
Majiyoyin tsaro sun nuna cewa an harba wani jirgi mara matuƙi da ke ɗauke da makami mai linzami daga wani jirgin yaƙin Amurka da ke sansanin sojin Amurkar a Ghana zuwa wani yanki na jihar Sokoto, inda bayanan sirri suka nuna ƴan ƙungiyar IS na cin karensu babu babbaka.
'Harin ya fatattaki Lakurawa'
Bayanai daga Sokoto sun nuna cewa hare-haren sun sauka a wurare daban-daban a ƙananan hukumomin Tambuwal da Tangaza duka a jihar Sokoto.
A Tangaza, shugaban ƙaramar hukumar ta Tangaza Isa Saleh Bashir, ya shaida wa BBC cewa "tabbas an kai hare-hare cikin daji kuma sansanonin ƴan ta'adda ne. Daga cikin wuraren da aka kai wa hare-haren sun haɗa da wani ƙauye da ake kira Tandami.
"Ba mu samu labarin adadin mutanen da suka mutu ba amma dai tabbas an jikkata su. Rahotanni na nuna cewa an ga jami'an tsaron jamhuriyar Nijar da ke sintiri sun ce sun ga Lakurawa na tserewa daga yankin," in ji shugaban ƙaramar hukumar.
'Harin Jabo ya jikkata mutane'
To sai dai kuma harin da aka kai garin Jabo da ke ƙaramar hukumar Tambuwal ya sauka ne a wani fili da ke bayan wani asibiti da ke ƙauyen na Jabo.
"Inda wannan abin ya faɗi bai fi mita 500 daga asbitin Jabo. Ba don Allah ya kiyaye ba ma da kan asibitin zai faɗa," in ji ɗanmajalisar dokoki da ke wakiltar ƙaramar hukumar Tambuwal wanda kuma ɗan Jabo ne.
Wani mazaunin garin na Jabo wanda ya shaida yadda harin ya kasance ya faɗa wa BBC cewa harin bai shafi kowa ba.
"Ina kwance a tsakar gida sai na ji ƙara sai na ga wani abu ya fito daga jirgi sai kuma na ji rugugum alamar ya faɗa ƙasa. Nan na shaida wa maiɗakina cewa abin nan fa ya faɗi ƙasa. Sai na fita na tsaya a ƙofar gida tare da abokai. Lallai mun ga ya faɗa sarari kuma bai shafi kowa ba. Gonakin albasa ya faɗa."
Sai dai kuma wani matashi mai suna Hassan Garba ya ce harin ya jikkata wasu mutane sakamakon tartsatsin wuta da ya haifar.
An kai ƙarin sojoji yankin
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa majiyar tsaro daga soji ta tabbatar mata cewa jim kaɗan bayan harin na Amurka, tuni rundunar sojoji ta aike da jami'an tsaro yankunan da ke zagaye da wurin da aka kai harin.
Ƙananan hukumomin da aka kai ƙarin sojojin sun hada da Gudu da Tangaza da Binji da manufar daƙile yiwuwar sake haɗuwar ƴan ta'adda da harin na ranar Alhamis ya tarwatsa.
Sai dai mazauna yankin da abin ya faru sun ce ba su ga jami'an tsaro ba kuma su ba su da masaniyar cewa a yankin akwai ƴan ta'adda.
"Mu nan yankin namu lafiya muke zaune. Ba mu taɓa sanin akwai wata matsalar tsaro a wannan yankin namu ba. Mu ma mun yi mamaki."
Harin Offa ya faɗa kusa da masallacin Idi da otal biyu
Majiyoyi da suka haɗa da na gwamnatin jihar Kwara sun tabbatar da cewa an kai harin a cikin garin Offa, inda a ƴan kwanaki wasu ƴan bindiga suka kai hari a coci wanda ya yi sanadiyya rasa ran mutum biyu sannan suka yi awon gaba da dama.
Hotuna da BBC ta samu daga mazauna garin sun nuna yadda makamin ya faɗa kan gidajen al'umma a garin Offa inda ya rugurguza katangun wasu tsirarun gine-gine.
Wani jami'in gwamnati ya ce al'amarin ya faru a wurare da dama a cikin garin na Offa da suka hada da kusa da filin Idi da wasu otal guda biyu da suka hada da Offa Central hotel da Solid Worth Hotel
Ƙarin hare-hare
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya nuna cewa akwai yiwuwar kai ƙarin hare-hare kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X cewa "Ƙari na nan tafe..."
Mista Pete dai bai faɗi ina ne kuma Amurkar za ta kai ƙarin hare-hare ba.
Sai dai a baya-bayan nan sunan Arewacin Najeriya ya yi ƙauri wajen "kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista" da Trump ya yi.