Majalisar dokokin Amurka ta fitar da rahoto kan zargin 'kisan Kiristoci' a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 5

Majalisar dokokin Amurka ta tsoma baki kan zargin da ake yi na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya umarci kwamitin majalisar wakilan ƙasar kan kasafin kudi ya yi bincike kan zargin kisan Kiristocin a Najeriya.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban na Amurka ya yi barzanar far wa Najeriya bayan ya bayyana ƙasar a matsayin 'abin kunya', inda ya ce Amurka za ta 'kawar da ƴan ta'adda' a ƙasar.

Kafin ganawar da ƴan majalisar wakilan Amurkar suka yi, wata tawagar gwamnatin Najeriya ta ziyarci Amurka domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan batun, da kuma hanyar magance matsalar tsaro a ƙasar.

A lokacin ziyarar, tawagar ta musanta duk wani zargin kisan kiyashi kan kiristoci a Najeriya.

Haka nan kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin aiki tare kan matsalar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.

Tawagar za ta yi aiki ne domin magance matsalar tsaro da Najeriya ke fama da ita, duk da dai har yanzu Amurkar ba ta fitar da tata tawagar ba.

'Da gangan ake yin kisan'

Brian Mast, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilan Amurka kan harkokin ƙetare ya ce hare-haren da ake kaiwa a Najeriya, ana yi ne da gangan kan wasu mutane.

Mast ya ce ba rikici ne kawai tsakanin al'umma ba.

"Wannan ba rikici ne kawai tsakanin al'umma' ko 'na neman abin duniya ba,' kamar yadda wasu ke cewa. Wannan wani mataki ne na kawar da mutane sanadiyyar addininsu."

Mast ya ce "walau Boko Haram, ko Iswap ko Fulani makiyaya masu tsattsauran ra'ayi', manufarsu ita ce kawar da kiristoci daga yankunansu.

Ɗan majalisar ya ce ya goyi bayan matakin Shugaba Trump na ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta.

"Dole ne mu buƙaci gwamnatin Najeriya ta ƙwace makamai daga hannun ƙungiyoyi, ta mayar da mutanen da aka tarwatsa zuwa gidajensu sannan ta hukunta masu laifi."

'Duniya ba za ta kawar da ido ba'

Ɗan majalisar Amurka Riley Moore mai rajin tabbatar da ƴancin addini, ya ce Kiristoci na fuskantar matsala ne saboda addininsu.

"Ƴan'uwanmu Kiristoci na fuskantar cin zarafi kuma ana kashe su a Najeriya kawai saboda sun yi imani da Yesu almasihu mai ceto."

Moore ya ce a sanadiyyar abin da ke faruwa ne ya sanya Shugaba Trump ya ba shi umarnin duba "wannan mummunan abu da ke faruwa da Kiristoci a Najeriya.'

"Duniya ba za ta kawar da idonta ba game da cuzguna wa Kiristoci a Najeriya," in ji shi.

Sai dai wani binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa alƙaluman da mutane irin su Riley Moore ke amfani da su wajen zarge-zargensu ba su da ƙwari.

'Dole ne a dakatar da kashe-kashe'

Vicky Hartzler ta hukumar tabbatar da ƴancin addini a ƙasashen duniya ta Amurka ta ce wajibi ne a dakatar da kashe-kashen da ke faruwa a Najeriya.

Hartzler ta yi iƙirarin cewa ƴancin gudanar da addini na fuskantar barazana kuma wajibi ne a kawo ƙarshen hakan.

"A ƴan kwanakin da suka gabata, ranar 22 ga watan Nuwamba an sace yara 303 da malamai 12 daga makarantar St Mary, ta mabiya katolika a jihar Neja.

"Ko ma wace ƙungiya ce ke aikata hakan, dole ne a sani cewa: ana take hakkin yin addini sosai," in ji ta.

Haka nan ta ambaci abin da ya faru a jihar Kwara, inda ƴan bindiga suka sace masu ibada. Ta ce ba za a ce ba a kashe Musulmai ba, amma yawancin waɗanda ake kashewa Kiristoci ne.

"Abin ya yi muni, ya ƙazanta, kuma Kirista ne suka fi shan wahala. To amma ko ma mene ne addinin waɗanda abin ke rutsawa da su, wajibi ne a dakatar da kashe-kashen, kuma dole gwamnati ta ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki domin hana ci gaba da wannan kashe-kashe.

Sai dai alƙaluma daga

Shawarwarin da ƴan majalisar suka bayar

Ƴan majalisar na murka sun bayar da wasu shawarwarin da za su taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu.

Hartzler ta bayyana matakin kamar haka:

  • Gwamnatin Amurka za ta yi aiki kai-tsaye da gwamnatin Najeriya domin bunƙasa yin komai a fayyace, tare da taimakawa wajen horas da ƴansanda da kuma yin sulhu.
  • Gwamnatin Amurka za ta nanata wa gwamnatin Najeriya buƙatar ɗaukar mataki cikin hanzari a duk lokacin da aka samu buƙatar hakan, domin tabbatar da cewa an mayar da hanakali wajen rage rikici tsakanin al'umma.
  • Gwamnatin Amurka za ta ci gaba da aiki da ta Najeriya domin samar da ƙwarewar da ake buƙata da tallafi wajen horaswa kan yadda za a magance matsalar ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya domin samar da ci gaba.

Su wane ne ƴan bindigar da ke addabar Najeriya?

Matsalar da ta fara a wajen shekarar 2011, kuma ta ci gaba da ƙazancewa tun wajen 2014, ƴan bindiga sun watsu a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sokoto da Neja da kuma Kebbi, a arewa maso yammacin Najeriya.

Ƴan bindigar na gudanar da ayyukansu ne a dazukan da babu alamar gwamnati a yankin, inda suke satar shanu, da fashi da makami, da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da fyaɗe da yi wa al'umma fashin kaya da kuma kashe-kashe.

A wasu wuraren sukan ƙaƙaba wa mazauna haraji.

Abin da ke iza wutar ta'asar da suke tafkawa shi ne safarar ƙananan makamai a yankin, musamman daga yankin Sahel mai maƙwaftaka.

Maƙasudin ayyukan ƴan bindiga shi ne domin su azurta kansu, ba domin siyasa ko aƙida ba. Suna ayyukansu ne ba tare da wani tsayayyen shugabanci guda ɗaya ba, amma suna da wasu da suka yi ƙaurin suna a cikinsu.

Daga cikin irin wadannan jagororin daba da suka yi ƙaurin suna akwai Dogo Gide da Ado Aleru, wadanda ke gudanar da ayyukansu a yankin jihar Zamfara.

Akwai kuma Bello Turji, wanda hare-harensa suka karaɗe yankunan Zamfara da Sokoto.

Gwamnati ta ayyana ayyukan ƴan bindiga a matsayin na ta'addanci a watan Janairun 2022, wanda hakan ya sanya su sahu daya da mayaƙan Boko Haram da Iswap da ke yaki a arewa maso gabas, kusa da tafkin Chadi.

A shekarun baya-bayan nan an samu rahotannin ƴan bindiga suna hada kai da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi ko kuma amfani da irin kalamansu.

Gwamnatin Najeriya na amfani ne da ƙarfin soji wajen yaƙi da gungun na ƴan bindiga, inda ta samar da sansanonin soji a yankin, tana ƙaddamar da farmaki ta ƙasa da sama, tana kama wasu daga cikinsu.

Ayyukan sojojin sun tarwatsa wasu daga cikin gungun ƴan bindigar, inda wasu suka watsu zuwa yamma, zuwa jihar Kwara, wasu kuma kudu zuwa jihar Kogi yayin da wasu suka yi wasu yankunan.

Gwamnatocin jihohi kan tallafa wa ayyukan sojoji, amma kuma wasu daga cikinsu sun yi sulhu da ƴan bindigar domin samun sauƙin matsalar wadda ta kashe dubban mutane da tarwatsa wasu dubban.