Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Binciken BBC ya gano masu ingiza zargin 'kisan Kiristoci' a Najeriya, shin gaskiya ne?
- Marubuci, Olaronke Alo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
- Marubuci, Chiamaka Enendu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Global Disinformation Unit
- Marubuci, Ijeoma Ndukwe
- Aiko rahoto daga, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 9
Barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi ta kai wa Najeriya hari domin dakatar da abun da ya kira kashe Kristoci a Najeriya ba hakanan ta faru ba.
Watanni da dama kenan da masu fafutuka da ƴan siyasa a Washington ke zargin cewa masu iƙirarin jihadi suna harin Kiristoci a Najeriya.
Sai dai BBC ba ta iya tabbatar da wasu hujjojin da aka dogara da su na iƙirarin ba.
Amma BBC ta gano cewa wasu alkaluman da ake amfani da su wajen tabbatar da wannan zargi suna da wahalar tabbatarwa da rashin tabbas.
A watan Satumba, shahararren mai gabatar da shiri Bill Maher ya kira abin da ke faruwa da "kisan ƙare dangi". Ya ce Boko Haram sun kashe fiye da mutane 100,000 tun 2009, sun kuma kona majami'u 18,000.
Alkaluma irin waɗannan sun yaɗu sosai a shafukan sada zumunta.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta yi watsi da iƙirarin tana mai bayyana shi da jirkita gaskiyar abun da ke faruwa.
Ba ta musanta cewa akwai tashin hankali a ƙasar ba, amma ta ce:
"'Yan ta'adda suna kai hari kan duk wanda ya ƙi bin mummunar aƙidarsu kama daga kan Musulmi ko Kiristoci ko wadanda ma ba su da addini."
Wasu ƙungiyoyi da ke bibiyar rikicin siyasa a Najeriya suna cewa adadin Kiristocin da aka kashe bai kai yadda ake fadi ba, kuma mafi yawan wadanda ƙungiyoyin masu iƙirarin ke kashewa Musulmi ne.
Masanin tsaro, Christian Ani ya ce duk da cewa Kiristoci na cikin waɗanda ake kai wa hari, ba za a ce su kadai ne ake hari kai tsaye ba. Ana kai hare-haren ne domin haifar da tsoro a cikin al'umma gaba daya.
Haka kuma Najeriya tana fama da matsalolin tsaro daban-daban a fadin kasar, ba kawai ta'addanci daga masu iƙirarin jihadi ba. Wadannan matsalolin suna da dalilai daban-daban, don haka bai kamata a rikita su wuri ɗaya ba.
Najeriya na da mutane kusan miliyan 220, rabinsu Musulmai, rabinsu Kiristoci. Amma Musulmi sun fi yawa a Arewa, inda mafi yawan hare-hare ke faruwa.
Me ƴan siyasan Amurka ke cewa?
Sanatan Texas mai tashe, Ted Cruz, ya dade yana yin yakin neman goyon baya kan wannan batu.
A ranar 7 ga Oktoban 2025 ya rubuta a X cewa "tun 2009, sama da Kiristoci 50,000 aka kashe a Najeriya, kuma an lalata majami'u sama da 18,000 da kuma makarantun Kirista 2,000".
A cikin wani saƙon imel da aka aika wa BBC, ofishin Sanata Cruz ya bayyana cewa shi ba zai kira wannan lamari da"kisan ƙare dangi ba." kamar yadda Maher ya faɗa, amma zai kira shi da "Musguna wa Kiristoci".
Sai dai Cruz ya zargi jami'an Najeriya da "watsi ko ma taimakawa wajen kisan Kiristoci da masu iƙirarin jihadi ke yi". Trump ma ya goyi bayan wannan magana, yana kiran Najeriya da "ƙasa mai wulaƙanta mutane", yana cewa gwamnati "ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci".
Gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargi, tana cewa tana iya ƙoƙarinta wajen yakar masu iƙirarin jihadi. Wasu jami'an ma sun ce suna maraba da taimakon Amurka wajen yaƙar 'yan tada zaune tsaye, matuƙar ba za a yi shi ba tare da Najeriya ba.
Gwamnatin Najeriya da ta daɗe tana fafatawa da ƙungiyoyin ƴan ta'adda da masu iƙirarin jihadi inda kusan duk mako ana samun labarin sabon hari ko sace mutane.
Boko Haram – wadda ta yi fice bayan sace 'yan matan Chibok – tana aiki tun 2009, amma yawancin hare-harenta a arewa maso gabas ne, yankin da Musulmai suka fi yawa.
Wasu kungiyoyi masu iƙirarin jihadi kamar ISWAP ma sun bayyana, sun fi kai hare-harensu a arewa maso gabas.
Adadin mutanen Kirista da wasu a Amurka ke cewa an kashe na da ban tsoro, amma tabbatar da ko wadannan alƙaluman gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne ba abu ne da ya kamata a duba.
Daga ina suka samu alƙalumansu?
Dangane da majiyar alƙaluman da ake amfani da shi, a cikin wani shirin podcast a watan Satumba, Cruz ya ce sun yi amfani da rahoton shekarar 2023 na International Society for Civil Liberties and Rule of Law (InterSociety) – wata ƙungiya mai zaman kanta wadda ke sa ido kan take hakkin ɗan'adam a Najeriya.
Ofishinsa ma ya tura wa BBC waɗansu adireshin na rubutu da suka tattauna batun wanda InterSociety ce ta fitar da bayanan.
Maher bai amsa buƙatar BBC kan inda ya samo alƙalumansa ba, amma ganin alƙaluman na kama da na Cruz, zai iya yiwuwa ya dogara ne kan bayanan InterSociety.
Ga bayanai da za su iya shafar manufofin Amurka kan Najeriya, aikin InterSociety bai fayyacacce ba ne.
A rahoton da suka fitar a watan Agusta, wanda ya haɗa bincike na baya-bayan nan da sabbin alƙaluma na 2025, an ce kungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya sun kashe fiye da Kiristoci 100,000 a cikin shekaru 16 tun daga 2009.
Rahoton ya kuma nuna cewa Musulmai 60,000 ma sun mutu a wannan lokacin.
InterSociety ba ta bayar da jerin tushen bayanai daki-daki ba, wanda hakan ke sanya tabbatar da adadin mutanen da suka ce sun mutu ya yi wahala.
A martani ga wannan sukan, ƙungiyar ta ce, "ku sani ba zai yiwu su sake dukkan rahotanninsu tun daga 2010 ba. Hanyarmu mai sauƙi ita ce ɗaukar ƙididdigar taƙaitaccen bayanan baya, mu haɗa da sabbin bayanan da muka gano domin mu haɗa sabon rahotonmu."
Amma majiyar bayanan da ƙungiyar InterSociety ke ambatawa a rahotanninta ba ya nuna ainihin ƙididdigar da suka wallafa.
Ya batun waɗanda aka kashe a shekarar 2025?
Idan aka duba mutuwar mutane a wannan shekara kaɗai, InterSociety ta ƙididdige cewa daga watan Janairu zuwa Agusta an kashe Kiristoci sama da 7,000.
Wannan adadin shi ma ya yaɗu sosai a kafafen sada zumunta, ciki har da wakilin Jam'iyyar Republican, Riley M Moore, wanda ya yi magana kan wannan batu a Majalisar Wakilai.
InterSociety ta haɗa jerin rahotanni guda 70 daga kafofin watsa labarai a matsayin wasu daga cikin majiyar bincikensu kan hare-hare da aka kai wa Kiristoci a 2025.
Amma a kusan rabin waɗannan lokuta, kafofin yaɗa labarai ba su ambaci addinin waɗanda abin ya shafa ba.
Alalmisali, InterSociety ta kawo rahoton Al Jazeera kan wani harin da aka kai a arewa maso gabas na Najeriya, tana cewa bisa ga rahoton "Boko Haram sun sace aƙalla manoma 40, mafi yawansu Kiristoci ne a Damboa, Jihar Borno."
Amma rahoton Al Jazeera bai ambaci cewa waɗanda abin ya shafa Kiristoci ne suka fi yawa ba kamar yadda InterSociety ta faɗa..
InterSociety ta faɗa wa BBC cewa suna yin ƙarin bincike don gano asalin waɗanda abin ya shafa, amma ba su bayyana yadda suka yi hakan ba, amma sun ambaci saninsu kan al'ummomi da kuma amfani da "rahotannin kafofin watsa labaran Kirista."
Idan aka haɗa adadin Kiristocin da aka ce an kashe a waɗannan rahotanni guda 70 da aka haɗa, adadin bai kai 7,000 ba kamar yadda InterSociety ta ambata.
BBC ta tattara alƙaluman mace-macen daga rahotannin 70 da aka haɗa kuma ta gano cewa adadin waɗanda aka kashe 3,000 ne ba 7,000 ba inda ta ƙara da cewa kamar an ruwaito wasu hare-haren fiye da sau ɗaya.
Don bayyana wannan bambanci alƙaluma da aka samu, InterSociety ta ce ta haɗa da yawan mutanen da take gani sun mutu a hannun masu garkuwa da kuma bayanan shaidun gani da ido waɗanda ba za ta iya fitar da bayanansu ga bainar jama'a ba.
Wa ke da alhakin kashe-kashen?
A cikin jerin wadanda ake zargi da kai hare-hare akwai ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi kamar su Boko Haram da makiyaya ƴan ƙabilar Fulani.
Fulani makiyaya yawancinsu Musulmai ne da ke zaune a fadin Yammacin Afirka, kuma mafi yawansu suna samun abin dogaro a rayuwarsu ne daga kiwon dabbobi.
Sai dai, saka Fulani makiyaya a cikin jerin masu kai hare-hare da InterSociety ta yi, inda suke kiran su "masu iƙirarin jihad" a duk rahotanninsu, ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya kan yadda za a rarraba irin waɗannan kashe-kashen.
Duk da cewa Fulani makiyaya galibinsu Musulmai ne, masana da dama a fannin sun musanta cewa wannan rikici na addini ne. Sun ce mafi yawancin rikicin na faruwa ne sakamakon kan buƙatar neman wurin kiwo.
Fulani makiyaya sun taɓa shiga rikici da al'ummomin Musulmai da Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya.
Masani kan harkar tsaro, Mista Ani, ya ce: "Kiran Fulani makiyaya masu iƙirarin Jihadi– wannan magana ce mai tsauri da nisa. kwata-kwata bai da alaƙa da addini. Yawanci ayyukan ƴan daba ne da masu aikata laifi kawai."
Confidence McHarry, babban masani a fannin tsaro a cibiyar SBM Intelligence da ke mai da hankali kan Afirka, ya ce rikicin ya kan faru ne saboda matsalolin ƙabilanci da gasa kan albarkatu.
"Yana iya kasancewa rikici na kabila ne – suna neman mamaye ƙasa, suna neman faɗaɗa yankuna, amma yadda suke tilasta wa al'ummomi su tsere kuma suna kai hare-hare a wuraren ibada, hakan ne ke sanya abubuwan su zama kamar rikicin addini ne."
Haka kuma, InterSociety ta ambaci abin da ake kira a Najeriya "'yan bindiga," inda mafi yawansu Fulani ne daga arewa maso yamma, waɗanda ke satar mutane da kuma kashe Musulmai da Kiristoci.
Su wane ne ke ƙarfafa batun?
Batun barazanar da Kiristocin Najeriya ke fuskanta ya daɗe ana tattauna shi tsakanin 'yan siyasa a Amurka da kuma ƙungiyoyin Kirista na duniya.
A cikin shekarun baya, wannan batu ya taɓa tasowa a Amurka ta hannun ƙungiyar IPOB – ƙungiyar da ke rajin kafa ƙasar Biafra a kudu-maso-gabas da yawanci Kiristoci ne.
Sojojin Najeriya sun zargi Intersociety da alaƙa da IPOB, amma wata ƙungiya mai zaman kanta ta musanta kowace irin alaƙa.
Wata ƙungiyar IPOB ta taka muhimmiyar rawa wajen yaɗa labarin "kisan ƙare dangi kan Kiristoci" a Majalisar Dokokin Amurka.
Gwamnatin Biafra da ke gudun hijira a ƙasashen Waje (BRGIE) ta bayyana wannan a matsayin "shiri ne na musamman sosai", inda ta ce sun ɗauki kamfanonin yaɗa labarai aiki kuma sun gana da jami'an Amurka, ciki har da Cruz.
Sai dai Sanata Cruz ya ƙi cewa uffan kan lamarin.
Me sauran masu bincike ke cewa?
Adadin Kiristocin da aka kashe da InterSociety ta bayar ya ninka fiye da rahotannin wasu majiyoyi game da yawan Kiristocin da aka kashe a Najeriya.
Acled, wata ƙungiya da ke sa ido a tashe-tashen hankula a Yammacin Afirka, ta bayar da adadi daban inda za a iya duba bayanan majiyoyin da ta wallafa cikin sauƙi.
Babban mai bincikenta, Ladd Stewart, bai yi magana kai tsaye kan rahotannin InterSociety ba, amma ya shaida wa BBC cewa adadin Kiristocin da aka kashe 100,000, wanda aka yaɗa a kafafen yaɗa labarai ya haɗa da dukkan rikicin siyasa a Najeriya, don haka ba gaskiya ba ne a ce wannan adadi ne na Kiristocin da aka kashe tun 2009.
Acled ta gano cewa fararen hula ƙasa da 53,000 aka kashe waɗanda Musulmai da Kiristoci ne a rikicin siyasa tun 2009.
Idan aka duba daga shekarar 2020 zuwa Satumba 2025, Acled ta ce kusan mutum 21,000 ne aka kashe ta hanyar garkuwa da su da hare-hare da cin zarafi ta hanyar lalata da amfani da bama-bamai.
Ta gano lamura 384 da aka kai hari musamman kan Kiristoci daga 2020 zuwa Satumba 2025, inda ta ce mutum 317 ne suka mutu, wanda ke nuna suna da ƙaramin kaso daga cikin waɗanda aka kashe.
Acled ta dogaro ne da kafafen yaɗa labarai na cikin gida da kafafen sada zumunta domin samun bayanai inda za a iya tabbatar da rahotanni da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, da kuma abokan aiki na cikin gida.
Ina Trump ya samo alƙalumansa?
A wani saƙo da Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Juma'ar da ta gabata, ya ambaci adadin Kiristocin 3,100 aka kashe.
Wani jami'in Fadar White House ya ce yayi amfani da rahoton da ƙungiyar Open Doors ta bayar game da Kiristocin da suka mutu cikin watanni 12 daga Oktoba 2023.
Open Doors wata ƙungiya ce da ke binciken yadda ake musgunawa Kiristoci a duniya.
A cikin rahotonta, ta ce yayin da Kiristoci 3,100 suka mutu, Musulmai 2,320 ne aka kashe a wannan lokacin.
Open Doors ta kuma haɗa abin da take kira "Ƙungiyoyin Ta'addanci na Fulani" a cikin jerin masu aikata laifi, inda ta ce sun yi sanadiyar kusan kashi ɗaya bisa uku na Kiristocin da aka kashe cikin watannin 12.
Frans Veerman, babban mai bincike a Open Doors, ya ce: "Abin da muke gani yanzu shi ne har yanzu ana kai wa Kiristoci hari, hakazalika harin da ake kai wa Musulmai ma na ƙaruwa."
Masana sun ce an samu hare-hare da yawa da aka kai kan masallatai da al'ummomin Musulmai a arewa maso yamma na ƙasar.
Mr. McHarry ya ce: "Za a iya cewa wannan wani ɓangare ne na rashin tsaro gaba ɗaya. Dalilin da ya sa ba a ɗauka cewa wannan rikici ne na addini ba shi ne; waɗanda ke kai hare-haren kan Musulmai ma wasunsu Musulmai ne."