Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun waƙoƙin Hausa da suka ja hankali a 2025
Kamar yadda aka saba, a wannan shekarar ma, kamar sauran shekarun baya, fasihan mawaƙan Hausa sun nishaɗantar da mutane ta hanyar baje-kolin waƙoƙinsu masu cike da hikima da saƙonni.
An fitar da waƙoƙi da dama da suka danganci siyasa da soyayya da na fina-finai da na nishaɗi, da ma waƙoƙin jan hankali.
Kamar yadda BBC ta saba a duk shekara, a bana ma mun zaƙulo muku wasu waƙoƙi da suka ja hankalin masu bibiyar waƙoƙin a wannan shekarar ta 2025 da ake ban-kwana da ita.
Sai dai a cikin jerin, ba a yi la'akari da waƙoƙin siyasa ba, inda aka fi mayar da hankali kan waƙoƙin soyayya da nishaɗi da ma na jan hankali daga waƙoƙin da mawaƙan arewa suka fitar.
Duk da cewa an fitar da ɗaruruwan waƙoƙi da suka ja hankali a wannan bigiren, inda akwai waɗanda suka ja hankali a wasu ɓangarorin daban, mun rairayo wasu domin tariya tare da tayar da tsumar ma'abota waƙoƙin Hausa.
Duk da cew akwai hanyoyin tantance waƙoƙin da aka saurara, mun yi amfani da yanayin kallon da aka yi a YouTube, duk da cewa akwai waƙoƙi da yawa da suka yi tashe, amma ba a kalla sosai a YouTube ba.
Gangar so: Shamsiyya Sadi
Waƙar 'Gangar So' na cikin waƙoƙin da suka ja hankali a wannan shekarar ta 2025 musamman a kafofin sada zumunta da wuraren bukukuwa, inda masoya suke tsakuro wasu daga baitocin waƙar suna haɗawa da hotunan masoyansu.
Mawaƙiya Shamsiyya Sadi ce ta rera waƙar, sannan jaruma Mommy Gombe ta hau bidiyon.
Daga cikin baitocin da aka amfani da salo na musamman wajen aika saƙon soyayya akwai:
Da salo kake gun tausayawa
To sai ga kuma kulawa,
Ka nai mani aikin yabawa,
Habibi kai duniya ne.
An fitar da bidiyon waƙar ne a ranar 16 ga watan Agusta, kuma zuwa lokacin tattara wannan labarin an kalla waƙar sama da dubu 340 a YouTube.
Sai dai waƙar ta daɗe tana tashe a kafofin sadarwa, kasancewar mawaƙiyar ta fitar da waƙar kafin ta ɗauki bidiyonta.
Ba su so - DJAB
Waƙar 'Ba su so" na cikin sababbin waƙoƙin da fitaccen mawaƙi Hausa mai amfani da salon zamani, musamman gambara, Haruna Abdullahi wanda aka fi sani DJ Ab ya fitar a shekarar 2025.
A ranar 6 ga watan Disamba ne Ab ya saki waƙar a YouTube, inda a cikin kwanakin kaɗan aka kalle ta sama da sau dubu 40.
Waƙa ce da aka nuna azanci da aika saƙon habaici cikin wani irin salo da hikima na musamman.
Daga cikin baitocin da mawaƙin ya aiksa saƙo cikin sauƙi akwai:
In dai ni ne
...za su gaji
In dai ni ne
...za su bari
Ba su so in yi gaba
Harkar na zam shugaba
Makauniya - Auta MG
Fasihin mawaƙi Auta MG ne ye rera waƙar nan ta 'Makauniya' wadda ta ja hankali matuƙa a wannan shekarar ta 2025.
Sabuwar jaruma Aisha Soba ce ta taka rawa a bidiyon waƙar wadda mawaƙin da kansa ya fito a ciki.
Daga ranar 1 ga watan Oktoban 2025 da aka fitar da waƙar zuwa lokacin tattara wannan labarin an kalle ta sama da dubu 570.
Waƙa ce ta soyayya da mawaƙin ya baza kalaman soyayya ga masoyiyarsa makauniya.
Daga cikin baitocin da aka bayyana soyayya akwai:
Sonki kamar ya kashe ni x3
Har hauka ya saka ni
Ban da tsimi da dabara yadda ya so haka ya yi da ni
Tun da na fara sonki har yau ba wata mai burge ni
Mai haske na idanu
Kamfanin Arewa Mediun Production ne ya shirya waƙar, sannan Sir Zeezu ya bayar da umarni.
Uwar gida - Ali Jita
Fitaccen mawaƙi da ya daɗe yana jan zarensa a harkar waƙoƙin Hausa Ali Jita ne ya fitar da waƙar 'Uwargida' wadda ta tayar da ƙura a kafofin sadarwa, inda aka yi tafka muhawara a kanta.
Saboda irin ƙurar da waƙar ta tayar dole shi kansa Ali Jita ya sake rera wata waƙar ta 'Amarya' sannan wasu mawaƙan suka yi wa amare wasu waƙoƙin domin a yayyafa ruwa.
Daga cikin baitocin da mawaƙin ya kanbama uwargida:
Uwargida mai capacity
Uwargida kin fi quality
Uwargida na da quantity
Ba mai taɓa miki identity
Dole su gane reality
Uwargida ce security
Daga ranar 26 ga watan Yuni da ya fitar da bidiyon waƙar, an masu kallo sama da miliyan 1.400 ne suka kalla a YouTube, duk da cewa waƙar ta fi yin tashe a kafofin sadarwa, inda aka riƙa yi wa amare habaici.
Amanata - Hamisu Breaker
Wannan waƙar ta 'Amanata' a ranar 15 ga watan Afrilun 2025 ne mawaƙi Hamisu Breaker ya fitar da ita, inda cikin kwanakin kaɗan kafofin sadarwa suka ɗauki zafi da muhawara kan wasu baitocin waƙoƙin.
Hukuma ma ta hana sauraron waƙar, lamarin da ya ƙara ja mata farin jini kasancewar sun neme ta domin sauraron me ya sa aka hana.
Daga lokacin da ya fitar da waƙar a YouTube, an saurare ta sama da miliyan 1.2, sannan a watan Disamba ya fitar da bidiyon waƙar.
Mai sona ina sonki
me zan ba ki na aure ki
Sonki yana ta ginan daki
Mu yi zamanmu a tare da ke ciki
A cikin ciki can ciki
Waɗannan baitocin ne aka zargi mawaƙin da cewa ba su dace, musamman yadda ƴan mata suka riƙa hawa baitoci suna rawa suna rangaji.
Beauty Sleep (na biyu) Rumerh da Magnito
Fitacciyar mawaƙiyar gambara ta Hausa wadda a yanzu take jan zarenta a masana'antar waƙoƙi Rumasa'u Adamu Muhammad wadda ake fi sani da sunan Rumerh ce ta rera waƙar 'Beuty Sleep'
Waƙar ta ja hankali musamman a kafofin sadarwa inda ma'abota waƙoƙin kudancin Najeriya suka riƙa ɗaura waƙar suna yaba mata tare da nuna mamakin ashe akwai mawaƙiya mace Bahaushiya haka, har suke mata laƙabi da 'Nicki Minaj'.
Alqur'an in na kwance to kamo zai wahala ne
Kai! ba tsoro ba ne in durƙusa in roƙe su, to ba su isa ba ne
Sun sha bugun ruwan cikina malam ban faɗa ba ne
Sun ɗauke ni yarinya mace ba wasan ƙasa ba ne
Ƙauna na ba ki - Soja Boy
Waƙar 'Ƙauna na ba ki' ita ma tana cikin waƙoƙin da suka ja hankali matuƙa a wannan shekarar da take ƙarewa.
Mawaƙi Soja Boy ne ye rera waƙar ta soyayya tare da jaruma Iftihal Madaki, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce sosai a kafofin sadarwa bayan ya fitar da tsakuren bidiyon waƙar.
Zama na duniya komai a hankali ake yi
Sam babu kuskure ke ce nake kira ta yayi
Na ba ki lasisi ki fada da ni kike yi
Ki daina tantama ki gyara zuciyar masoyi
Zan zage damtse domin da ke mu yo rayuwa
Ki sa zamanki ba za na so a raina ki ba
Ƙauna na ba ki
Ƙwarai ina ta yin godiya
Daga ranar 1 ga Nuwamban da ya fitar da bidiyon zuwa yanzu an kalle ta a YouTube sama da sau 832.
Malawu
Mawaƙi Lilin Baba ne ya rera waƙar Malawu, wadda ta samu karɓuwa sosai a tsanakin matasa.
Daga ranar 20 ga watan Mayun 2025 da ya fitar da bidiyonta a YouTube zuwa lokacin tattara waɗannan bayanan an kalle ta sama da dubu 692.
Malawu, malawu, malawu yeye
Ga kiɗa waiwai'
Kiɗi ke sa rawa
Malawu, malawu, malawu
Sama, sama, sama!!!