Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mashahuran mawaƙan Hausa da tarihinsu ya yi amo a duniya
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 7
Ƙasar Hausa ta jima tana renon mashahuran mutane da tarihinsu ya yi amo a fannoni daban-daban, kama daga ilimi da sana'a da kuma fagen nishaɗantarwa da sauransu.
A duk lokacin da aka yi maganar nishaɗi, batun waƙa na da matuƙar muhimmanci, inda ya kasance ɗaya daga cikin manyan ɓangarorin nishaɗi.
A wannan fanni na waƙoƙai ƙasar Hausa ta yi mashahuran mawaƙan maza da mata da suka yi fice, kuma har yanzu ake tunawa da su duk kuwa da shuɗewar zamani.
Waɗannan mawaƙa sun bayar da gagarumar gudunmowa a fannin adabin baka na da ma na zamani a Hausa.
An samu rubuce-rubucen binciken kammala digiri na farko da na biyu har da na uku kan waƙoƙi da rayuwar wasu daga cikin waɗannan mawaƙa.
A wannan maƙala mun yi ƙoƙarin tattaro muku wasu daga cikin mawaƙan da suka yi fice a ƙasar Hausa.
Mamman Shata
An haifi Mamman Shata a shekarar 1923 a garin Musawa da ke jihar Katsina, kamar yadda Dakta Ibrahim Sheme ya bayya acikin littafinsa mai taken ''Shata Ikon Allah''.
Bayan da ya ɗan tasa an sanya shi a makarantar allo, kamar yadda aka saba gani cikin al'adar Hausawa kuma Musulmi, inda kuma yake haɗawa da tallar goro.
Mamman Shata ya fara waƙa ne tun yana matashi daga dandali, kuma a lokacin ba don samun kuɗi ba, sai don nishaɗantar da abokansa da kuma ƴan matan dandali.
- Tashensa
A shekarar 1952 ne Mamman Shata ya fara yin suna lokacin da ya yi wasa a wurin bikin wasu ƴaƴan sarki su 12, tun daga nan kuma tauraruwarsa ta ci gaba da haskawa har tsawon shekaru 50 zuwa 60 da ya shafe a fagen na waƙa.
Babu wani adadi da za a iya cewa shi ne yawan waƙokin Shata kasancewar ba a tattara waƙoƙinsa da dama ba, musamman waɗanda ya yi su a lokacin da yake matashi.
Yayin rayuwarsa, fitaccen mawakin ya karɓi kambu da kuma lambobin girmamawa da dama, ciki har da wadda gwamnatin Najeriya ta ba shi ta MON, da wadda ƙungiyar mawaka ta ƙasa PMAN ta ba shi, sai wadda gwamnatin jihar Kano da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya da jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da Jami'ar Carlifornia ta Los Angeles duk a Amurka suka ba shi da sauransu.
Shata ya koma ga mahaliccinsa ranar 18 ga watan Yulin 1999 a asibitin Malam Aminu Kano bayan jinya a wani asibiti da ke birnin Jidda na Saudiyya a sakamakon cutar tsoƙoƙin jiki.
Wasu cikin fitattaun waƙoƙinsa
- Na tsaya ga Annabi Muhammadu
- Kuɗi A Kashe su ta Hanya Mai Kyau
- Ahmadun Gaya
- Bashar Mai Daura
- Lamin Shagamu
- Bakandamiya
- Gagabadau
- Dankabo
Dankwairo
Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, na Jami'ar Bayero da ke Kano, fitattcen masanin waƙoƙin Makaɗan Hausa, ya ce duk da saɓanin tarihin haihuwa, ana ɗaukar cewa an haifi Musa Ɗanƙwairo a 1909.
Haihuwar Musa Ɗanƙwairo ta wakana a garin Ɗankadu na gundumar Bakura a yau ta Jihar Zamfara, kafin iyayensa su koma Tunga, Birnin Ƙaya ta gundumar Maradun, kamar yadda Farfesa Gusau ya bayyana cikin wata maƙala da ya gabatar kan rayuwar Ɗanƙwairo ranar 13 ga watan satumban 2021 a Jami'ar Bayero da ke Kano.
Malamin Jami'ar ya ce an raɗa wa Ɗanƙwairo sunan yanka na Musa.
Shi kuwa Ɗanƙwairo wata alkunya ce ake yi masa. Bayan ya kai shekara bakwai da haihuwa, ya fara sa hannu a harka ta kiɗa da waƙa a ƙarƙashin mahaifinsa Makaɗa Usman Ɗankwanagga.
- Shaharsa
Farfesa Gusau ya ce Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya samar da wata tawaga mai aiwatar da kiɗa mai zurfin tunani wadda kuma ta amsa sunanta.
A wannan tawaga Ɗanƙwairo ne Jagora, kuma yana bai wa ƴan amshinsa damar yin ƙari da ajewa da sauka da saukar sauka da takidi da rakiya ko karɓeɓeniya, wani bi ma da bayayyeniya, sannan da yin takidi na ginin waƙa.
Haka kuma a rera wasu waƙoƙi, Alhaji Musa Ɗanƙwairo yakan tafi da Sanƙirori da wasu hadiman waƙa duk a ƙungiyar kiɗa ta Musa Ɗanƙwairo.
Musa Ɗanƙwairo Maradun ya rasu ne ranar Juma'a 13 ga watan Satumban 1991 bayan gajeruwar jinya a gidansa da ke ƙaramar hukumar Maradun.
Wasu cikin fitattun waƙoƙinsa
- Waƙar Sarkin Muri
- Sarkin Gombe
- Atiku Turakin Adamawa
- Waƙar Sarki Ado Bayero
- Ahmed Aruwa
- Alhaji Kabiru Mafo
Barmani Mai Choge
Asalin sunanta na ainihi shi ne Sa'adatu Aliyu.
An haifeta a shekarar 1943 a garin Funtuwa da ke jihar Katsina a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Shahararriyar mawaƙiya ce, mai kiɗan ƙwarya ko kiɗan amada, kuma ta fara waƙa tana da shekara 27.
Barmani Choge ta kasance ɗaya daga cikin fitattun mawaƙa mata a da sunansu ya yi shuhura a ƙasar Hausa.
Waƙar Amada ta samu karɓuwa da yaɗuwa sanadiyar Barmani Choge, ganin irin tashe da ta yi a cikin harkar waƙar, kuma hakan ya sa ta zama mafi ɗaukaka a cikin mata masu waƙa na Arewacin Najeriya, kamar yadda tarihi ya nuna.
Waƙoƙinta suna faɗakarwa ga mata a kan neman ilimi, da yin sana'o'in hannu da kuma nunin illar zaman kashe wando, ta hanyar raha da yin tsokana a kan kishiyoyi a gidan aure.
Barmani Choge ta rasu a shekarar 2013 bayan fama da jinya.
Wasu daga cikin fitattun waƙoƙinta
- Mu kama sana'a mata
- Waƙar Kishiya
- Sakarai Ba Ta Da Wayo
- Duniya Kashe Ahu
- Waiwaya Baya
- Waƙar Gonnai
- Allah Ka Ba Mu Nairori
- Sama Ruwa Ƙasa Ruwa
- Gorne Ikon Allah
Narambaɗa
Asalin sunansa na yanka shi ne Ibrahim Maidangwale, a cewar Farfesa Aliyu Muhammad Bunza, Malami a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto.
An haife shi a shekarar 1890 a garin Tubali da ke jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Mahaifinsa, Maidangwale dan asalin garin Filinge ne na Jamhuriyar Nijar ne, amma ya koma garin Tubali da zama har ya auri mahaifiyar Narambaɗa, a cewar Farfesa Bunza.
Maidangwale dai shahararren ɗan dambe ne da ya yi fice a lokacinsa, kamar yadda Farfesa Bunza ya bayyana.
An haifi Narambada a garin Tubali kuma a nan ya yi karatu, ya yi rayuwarsa duka.
Mahaifiyar Narambada kuwa makiɗiya ce, don haka a iya cewa ya yi gadon kiɗa ne daga wurinta.
Ya samu sunan Narambada ne dalilin wata karyarsa da ake ce wa Rambaɗa, don haka sai aka yi masa laƙabi da Narambada.
Mawaƙin ya shahara a shekarun baya, inda sunansa ya kai har wuraren da bai je ba.
Farfesa Bunza ya ce "a ganina dukkanin ƙasar Zamfara ba a yi mawakin da ya kai Narambada ba. Kuma ba a kasarsa kawai yake waka ba. Ma'ana, duk duniyar kasar Hausa."
Fitaccen mawaƙin ya rasu a shekarar 1963 yana da shekara 73 a duniya.
Wasu daga cikin waƙoƙinsa
- Dokin Iska Ɗahilinge
- Gwarzon Shamaki na Malam Toron Giwa
- Ahmadun Babukar Gwarzon Yari
- Madogara Na Malam Iro
Dan maraya Jos
An haifi Adamu Dan Maraya a shekarar 1946 a garin Ɓukur da ke cikin jihar Filoto da ke yankin tsakiyar Najeriya.
Bayan rasuwar uwayensa, aka fara kiransa Dan Maraya (saboda ba shi da iyaye)
Ɗan Maraya Jos, ya yi suna sosai a arewacin Najeriya da wasu yankunan ƙasashen Yammacin Afirka.
Yawancin waƙoƙin ɗan Maraya suna bayani ne a kan al'amurra na yau da kullum da ke fuskantar mutane a ƙasar Hausa.
Mawaƙin ya shafe fiye da shekara 60 yana waƙa a duniya, inda waƙoƙinsa suka zama zakaran gwajin dafi a zamaninsa.
Dan-Maraya Jos ya yi suna sosai wajen yin wakokin da ke bayyana halin dan adam, wadanda suka hada harda wadda ya yi take 'Mutun Dan Adam Mai Wuyar Gane Hali".
Ya ƙware sosai wajen kiɗan kuntigi, kuma ya samu manyan kyaututtuka da yawa a ciki da wajen Najeriya saboda irin gudummuwar da wakokinsa suka bayar wajen neman zaman lafiya.
Wasu daga cikin waƙoƙinsa
- Mai Akwai Da Babu
- Waƙar Mamser
- Waƙar Dan Amalanke
- Wakar Bikin Fatima
Magajiya Dambatta
Asalain sunanta shi ne Halima Malam Lasan, kuma an haife a garin dambatta da ke jihar Kano a arewacin Najeriya.
Shahararriyar mawaƙiyar Hausa ce wadda ta samar da waƙoƙi na shawarwari masu yawa a cikin shekaru 70 kan mahimmancin ilimi, kyawawan dabi'u, da tarbiyyar yara, yayin da kuma take tir da munanan halayen jama'a, da sauransu.
Magajiya Ɗanbatta ta fara waƙa ne tun tana da shekaru 12, kuma ta yi waƙoƙi da dama inda ta shahara a wancan lokaci ta yadda idan ba ta je taro ta yi waƙa ba, taron bai cika yin daɗi ba.
Ta haɗu da Shata a lokacin bikin cikar Gidan Rediyon Najeriya Kaduna shekara 30, inda ta rera wakarta mai suna Soriyal.
Ta kasance cikin mawaƙa manya da duniyar Hausa ke sauraro kuma suka yi takama da su a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.
Wasu daga cikin waƙoƙinta
- Waƙar Soriyel
- Waƙar Lilo
Uwani Zakari
Uwani zakirai ta kasance ɗaya daga cikin mashahuran mawaƙan da suka yi tashe a shekarun baya.
An haifi mawaƙiyar ranar a shekaar 1933 a garin Jigoron Kanawa da ke yankin ƙaramar hukumar Gabasawa ta yanzu a jihar Kano, kamar yadda Dakta Ibrahim Sheme ya bayyana cikin littafinsa mai taken ''Tarihi da Waƙoƙin Uwani Zakirai''.
Cikakken sunanta shi ne Hajiya Salamatu Zakirai.
Ta fara tashe ne a farkon shekarun 1955, kamar yadda Dakta Sheme ya bayyana cikin littafin nasa.
Wasu daga cikin fitattun waƙoƙinta:
- Dan-Alhaji Mainama
- Lalayyo Allah Ya Ba Mu Lafiya (1)
- Allah Bar Mana Dan Da Nake So
- Allah Ya Jikan Kankiya Iro
- Taken Direbobi
- Asauwara
- Lalayyo Allah Ya Ja Kwana
- Yara lye Nanaye Ayyara Iye Nanaye
- Tausa Kalangu Nababa Ka Ji Batun 'Yar Na
- Azizu Dan Makaranta (ta 1)
- Azizu Dan Makaranta (ta 2)
- Sojan Kwango (1)
- Sojan Kwango (2)
- Lalayyo Allah Ya Ba Mu Lafiya (2)
- Babu Kokwanto