Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mun kai hari kan ƴan ƙungiyar IS a Najeriya - Trump
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta ƙaddamar da wani mummunan hari kan mayakan IS a arewa maso yammacin Najeriya.
"Dakarun Amurka sun ƙaddamar da hare-hare masu kyau," in ji Trump.
Cibiyar sojin Amurka a Afrika daga baya ta ce an kai hare-haren ne a jihar Sokoto.
Shugaban ya zargi ƙungiyar da kai hari tare da kashe Kiristocin da ba su ji ba su gani ba a ƙasar.
A shafinsa na Social Truth, Trump ya wallafa da yammacin Alhamis cewa "a ƙaƙashin shugabancina, ƙasarmu ba za ta bar masu tsattsauran ra'ayin Musulunci sun girmama ba."
Mista Trump bai faɗi lokacin da aka yi kashe-kashen ba da yake magana a kai amma kuma ya yi zargin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya wanda batu ne da ya yi ta wadari tsakanin masu kaifin ra'ayin Kiristanci a Amurka.
Sakataren harkokin tsaron Amurka Pete Hegseth, ya ce ya gamsu da hadin kai da kuma goyon bayan da gwamnatin Najeriya ta ba su.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce harin wani bangare ne daga cikin hadin gwiwar tabbatar da tsaro da aka ƙulla da Amurka.
A watan Nuwambar da ya gabata shugaba Trump ya bayar da umarni ga rundunar sojin kasarsa ta shirya daukar mataki kan Najeriya domin magance mayakan kungiyar na ISIS.
Ya yi zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi, abin da gwamnatin Najeriya ta musanta tare da watsi da ikirarin nasa
Gwamnatin Najeriya ta ce kungiyoyin masu dauke da makamai da ke kai hare-hare a Najeriya ba sa bambance kirista ko musulmi wajen kai hari.
Najeriya ta shafe fiye da shekara 10 tana yaƙi da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.
Ma'aikatar tsaron Amurka daga baya ta wallafa wani taƙaitaccen bidiyo da yake nuni da yadda aka harba makami mai linzami daga wani jirgin yaƙi.
Da safiyar ranar Juma'ar nan ne ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, ta fitar da wata sanarwa cewa gwamnati "na cikin yarjejeniyar samar da tsaro da ƙasashen waje da suka haɗa da Amurka domin dakile ta'addanci da tsauraran aƙidu.
"Kuma wannan ya haifar da kai hare-hare ta sama wuraren ƴan ta'adda a arewa maso yammacin Najeriya." in ji sanarwar.
Ƙungiyoyi da ke saka ido kan rikice-rikice sun ce babu shaidar da ke nuna cewa ana kashe Kiristoci fiye da Musulmai a Najeriya.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar watsa labarai, Daniel Bwala ya shaida wa BBC cewa ya kamata duk lokacin da za a ɗauki matakin soji ga ƙungyoyin to a yi hakan ta bai ɗaya.
Bwala ya ƙara da cewa Nigeria za ta yi maraba da taimakon da Amurka za ta ba ta a fagen yaƙi da ta'addanci amma kuma ya bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai ikon cin gashin kanta.
Ya kuma ƙara da cewa masu iƙrarin jihadi ba wai kawai suna kai hare-hare ne kan Kiristoci ba, sun kashe ƴan ƙasa ne daga dukkan addinai.
Shugaba Tinubu ya kafe cewa babu alamun rashin haƙuri tsakanin mabiya addinai a Najeriya sannan ya ce matsalolin tsaro suna shafar mabiya dukkan addinai guda biyu a yankunan ƙasar.