‘A shafukan sada zumunta na tsinci labarin mutuwar ɗana'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Khadidiatou Cissé
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
Yayin da matasan Afirka ke ci gaba da yin kasadar zuwa Turai ta Tsibirin Canary, firaministan Sifaniya ya fara tattaunawa da ƙasashen Senegal da mauritaniya, da Gambiya domin daƙile yunƙurin nasu.
Sai dai kuma wannan ba wani abin jin daɗi ba ne ga Amina.
"A shafukan sada zumunta na samu labarin mutuwar ɗana," kamar yadda ta shaida wa BBC daga gidanta da ke kusa da babban birnin Senegal.
"Muna yawan yin magana har ma ya faɗa min cewa ya na son zuwa Morocco," a cewar matar mai shekara 50.
"Bai taɓa faɗin cewa a jirgin ruwa yake shirin tafiya ba."
Lokaci na ƙarshe da ta ji daga ɗan nata mai suna Yankhoba shi ne a watan Janairu.
Duk fafutikar neman matashin mai shekara 33 kuma tela da aka yi bai yi nasara ba.
Sai kuma a farkon watan Agusta, masunta suka gano gawarsa a gefen Tekun Atalantika kusan nisan kilomita 18 daga gabar ruwan ƙasar Dominican Republic.
Aƙalla gawar mutum 14 ne ke cikin ɗan ƙaramin jirgin na katako, in ji ƴansanda. Takardu da wayoyin salula da aka gani a jikinsu sun nuna cewa akasarinsu daga Senegal suke, da Mali, da Mauritaniya.
An ga katin shaidar Yankhoba a cikin jirgin.
Jami'an ƙasar Dominica sun ce an kuma ga wasu ƙunshin abubuwa 12 da ke ƙunshe da ƙwayoyi.
Ana ci gaba da nazartar lokaci da kuma musabbabin mutuwar mutanen, duk da cewa an yi imanin fasinjojin suna yunƙurin kaiwa Tsibirin Canary ne gabanin salwantar tasu.
Jirgin nasu ya yi kama da irin waɗanda aka saba yin safarar mutane zuwa Turai da su ta ɓarauniyar hanya.
Yankhoba ne na farko a wajen mahaifiyarsa kuma shi kaɗai ne. Ya bar matarsa da ƴaƴa biyu, har ma da jaririn da ba a kai ga haihuwarsa ba.
"Na yi ta fatan ko an kulle Yankhoba a gidan yari a Morocco, ko kuma Tunisiya," in ji mahaifiyarsa.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Baƙin haure da ke son zuwa Turai daga Afirka na yawan bi ta Tsibirin Canary da ke ƙasar Sifaniya.
Duk da hatsarin da ke tattare da hakan, sau ɗaya kawai za a yada zango, ba kamar bi ta cikin Sahara ba da kuma Tekun Baharrum.
A shekarar da ta gabata kaɗai an ga ƙaruwar kashi 161 idan aka kwatanta da shekara da ta gabace ta, na yawan masu bin hanyar, a cewar hukumar kula da iyakokin Turai mai suna Frontex.
Sifaniya na cikin ƙasashen Turai da suka fi karɓar baƙin hauren.
Masu barin Senegal kuma, ana samun ƙaruwar ma'aikata masu kuɗi da ke tafiya Amurka maimakon Turai duk da tsadar tafiyar.
Abin da Fallou ya yi ke nan.
Duk da cewa yana da gonar kiwon awaki da tsuntsaye a birnin Dakar mai kawo masa kuɗi, amma yana fama da matsin rayuwa.
"Na ji ba na motsawa da kyau. Bayan aiki a gonata, ina kuma aiki a wata ma'aikata, amma duk da haka da kyar nake kaiwa," a cewarsa.
Yana da shekara 30 da haihuwa, sai ya sayar da komai da komai kuma ya sayi tikitin jirgi zuwa Nicaragua a nahiyar Amurka ta Tsakiya. Daga nan kuma ya zarce zuwa Amurka.
"Mahaifiyata ba ta so na tafi ba, amma ni kuma na gama shirin fuskantar mutuwa," in ji shi.
Fallou ya yi balaguro na kwana 16 ta cikin Nicaragua, da Guatemala, da kuma Mexico bisa taimakon masu safarar mutane. A jimlace, ya kashe sama da dala 10,000 a balaguron.
Idan aka kwatanta da matasan da ke tsallaka ruwa zuwa tsibirin Canary, sukan biya masu safara abin da bai wuce dala 450 ba.

Asalin hoton, AFP
Fallou ya ce sadaukarwar da ya nuna na ƙunshe da ƙalubale.
"Mutane da yawa sun mutu a kan idona," in ji shi.
"Amma kuma na ga matan da suka jajirce, wasu ma tare da ƴaƴansu a baya, sai na ji: "'Ya kamata na jajirce.'"
Bayan tsare shi a wani sansanin baƙin haure na Amurka na ƴan kwanaki, Fallou ya samu damar fita don ya zama mai neman mafaka. Tuni kuma ya haɗu da ɗan'uwansa kuma yanzu yana aiki a matsayin bakanike.
Fallou dai ya yi sa'a, amma da yawa daga cikin baƙin haure daga Afirka a Amurka ba su yi ba.
A watan Satumban da ya gabata, an mayar da ƴan Senegal sama da 140 gida bayan sun tsallaka iyakar Amurka da Mexico.
Duk da yawan ƴan Afirkan da ke sauya hanyar kaiwa Turai, har yanzu akasarinsu sun fi bi ta Tekun Baharrum.
Cikin shekara 10 da suka wuce, hukumar kula da masu ƙaura ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta IOM ta ce sama da baƙin haure 28,000 ne suka nutse a ruwan Baharrum ɗin kaɗai.
Alƙawuran siyasa
"Mutane na barin Afirka ta Yamma ne saboda suna fuskantar matsalolin tsaro, da na abinci, da tsafta, da tasirin korona, da ma sauran matsaloli na muhalli," a cewar wani ƙwararre kan harkokin hijira, Aly Tandian.
Mutanen da ke barin Senegal musamman na ƙaruwa, duk da cewa tana cikin ƙasashen da suka fi saura kwanciyar hankali, ga kuma sabon shugaban ƙasa da ke alƙawarin ƙirƙirar sabbin ayyukan yi ga matasa.
Tun bayan da aka zaɓi sabuwar gwamnati a watan Maris, ta yi nasarar rage farashin wasu kayan masarufi kamar na man girki, da burodi, da shinkafa - abin da ya sa tsadar rayuwa ta ragu.
Sai dai hakan bai isa ba.
"Mun zaci sauya gwamnatin zai jawo raguwar masu fita daga ƙasa, amma lamarin bai tsaya ba," kamar yadda Boubacar Sèye, shugaban ƙungiyar Horizon Without Borders, ya bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
A watan Yuli, bayan an gano gawar mutum 89 a kusa da gaɓar ruwan Mauritaniya, Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya roƙi matasa da su daina bin hanyar Tekun Atalantika mai haɗari zuwa Turai.











