'Shekara bakwai ke nan ban sanya ɗana a ido ba' - Rayuwar ƴan gudun hijirar Sudan

Asalin hoton, Michel Mvondo/BBC
- Marubuci, Paul Njie da Michel Mvondo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Aiko rahoto daga, Farchana
- Lokacin karatu: Minti 4
Miriam na zaune a kan tabarma a cikin ɗakin girkinta tana kallon hoton babban yaronta Mohamed, wanda shekara bakwai ke nan ba ta gan shi ko ji daga gare shi ba.
Miriam na zubar da hawaye lokacin da take bayar da labarin wahala da ƙalubalen da ɗanta Mohamed ya fuskanta wajen gwagwarmayar isa Turai da yaƙinin cewa rayuwar iyalin zai canja gaba ɗaya ta hanya mai kyau.
Mohamed dai ya bar gidansu da ke a jihar Darfur a Sudan ta Yamma domin yin tafiya mai haɗari daga Sudan ta amfani da hanyar Hamadar Sahara mai haɗari.
"Masu sace mutane sun yi garkuwa da shi sau biyu a lokacin da ya isa Libiya," Miriam ta shaida wa BBC.
"Da farko dai, waɗanda suka sace shi sun buƙaci a biya su kuɗin fansa, inda iyalaina da maƙota muka haɗa kuɗin kuma muka biya."
Ta ce maganarta ta ƙarshe da yaronta ta faru ne ranar 10 ga watan Disamban 2017.
"Kafin yunƙurinsa na ƙarshe wajen tsallakawa zuwa Turai, ya kira ni ta wayar abokinsa." in ji Mariam, yayin da take tuna fatan da yaronta ke da ita ta shiga Turai washegari.
Amma kuma yanzu ta ce ba ta san ko yaronta na da rai ko ya mutu ba.

Asalin hoton, Michel Mvondo/BBC
A watan Afrilun 2023, yayin da rikici ya ɓarke tsakanin ɓangarorin sojojin Sudan da ke gaba da juna, rikicin ya tilasta wa Mariam tserewa zuwa gabashin Chadi tare da karamin ɗanta, Ahmed.
Yanzu suna zaune a sansanin Farchana, wanda kusan fararen hula 42,000 na Sudan waɗanda suka tsere daga yaƙin basasar da ya ɓarke a farkon shekarar 2000 da kuma tashe-tashen hankula na Afrilun 2023, ke samun mafaka
Duk da sun samu mafaka, ƙarancin abinci, da rashin damammaki suna sa matasa kamar Ahmed su yanke ƙauna saboda yanayin takaici da mummunan halin da suke ciki.
Dalilin haka ne ya sanya Ahmed tunanin bin sawun ɗan'uwansa ta yin tafiya mai haɗari zuwa Turai, inda ake bi ta cikin Libya da Tunisia.
"Lokacin da muke zaune a Sudan, ni ɗalibi ne a jami'a inda nake da babban buri da fata mai kyau na rayuwata," in ji Ahmed.
Mummunan tashin hakalin uwa
Mariam yanzu ta ce tana cikin fargaba da mummunan tashin hankali saboda yiwuwar rasa ɗanta na biyu a cikin hamadar Sahara.
“Na roƙe shi kada ya tafi domin na riga na yi rashin ɗa guda ɗaya. Ina cikin tsoro da fargaba kan abin da zai same shi," in ji Mariam, muryarta cike da damuwa.
Duk da roƙon da ta yi, Ahmed ya ci gaba da dagewa kan tafiya, inda ya ce yana da yaƙinin zamansa a Chadi ba shi da makoma.
E, mahaifiyata ba ta son in tafi, amma ba zan iya zama a Chadi ba. Babu wata damar yin karatu ko wata fata a nan," in ji Ahmed.
"Ba zan iya barin rayuwata ta ƙare ta wannan hanyar ba."
Kalaman Ahmed sun yi daidai da ra'ayin miliyoyin matasa a duk duniya wanda hakan ya zama abin tunatarwa game da mummunan tasirin da yaƙin ya yi kan fararen hula na Sudan.

Asalin hoton, Michel Mvondo/BBC
Yunƙurin da ya gaza cimma nasara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɓacin rai da ƙuncin da Ahmed ke fuskanta na da alaƙa da Sidik, ɗan shekara 28, wani ɗan gudun hijira ɗan Sudan wanda ya zauna a Farchana tsawon shekaru ashirin.
Ya yi yunƙurin tsallakawa Turai daga Libya da Tunisiya sau uku ba tare da samun nasara ba.
“Halin da muke ciki a nan na da wahala. Babu wani tsayayyen aiki, dalilin da ya sa na yi ƙoƙarin yin tafiya ta Libya sau da yawa ke nan," in ji Sidik.
Ya yi gudun hijira zuwa ƙasar Chadi tare da iyalansa yana da shekaru bakwai kuma ya bar makaranta saboda rashin kuɗi.
Kamar Ahmed da wasu da yawa a sansanin Farchana, yana jin cewa jefa rayuwarsa cikin haɗari yana da amfani idan hakan yana nufin kyakkyawar makoma ga yaransa.
"Har yanzu dai shirinmu na tafiya zuwa Turai yana nan, kuma ba za mu daina ba saboda ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba," in ji shi.
Hamadar Sahara na ɗaya daga cikin hanyoyin hijira mafi haɗari a duniya.
A cewar Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM), baƙin haure 161 ne suka mutu a ƙoƙarin tsallakawa zuwa Turai ta wannan hanya a shekarar 2023 kaɗai.
Hukumar ta IOM da abokan hulɗar ƙasashen duniya sun ɓullo da shirye-shiryen yin hijira kan ƙa'ida ga ƴan gudun hijira a Chadi.
A tsakanin shekarar 2017 zuwa 2019, shirin ya taimaka wajen mayar da ƴan gudun hijira kusan 2,000 daga Chadi zuwa Faransa.
Ying Hu, mataimakin jami'in bayar da rahoto a ofishin Farchana na UNHCR, ya lura cewa ana iya samun shirye-shiryen sake tsugunar da ƴan gudun Hijira dangane da isassun kuɗaɗen da ake da su.











