An kona kauyuka sama da 100 a yakin Sudan

sudan

Asalin hoton, reuters

Bayanan hoto, Yakin babasar Sudan ya raba miliyoyin farar hula da muhallansu

Kungiyoyin kare hakkin dan adama da suka nazarci shafukan sada zumunta da hotunan taurarin dan adam sun ce sama da kauyuka 100 aka bankawa wuta a yammacin Sudan tun soma yakin basasar kasar kusan shekara guda yanzu.

Masu bincike a wata cibiyar tattara bayanai sun ce da gangan ake tada gobara a matsayin wani makamin yaki, yanayin da ya tilastawa dubbai tserewa daga gidajensu.

Akasarin wadannan kauyuka da aka kona a Darfur suke. Kungiyoyin sun ce akwai wani gari mai suna Misterei da aka rinka bi layi-layi ana banka musu wuta.

Mayakan larabawa da dakarun RSF aka daurawa alhaki ko zargin amfani da wannan salo a yakin Sudan, batun da suke musanta.

Wannan rahoto na zuwa ne adaidai lokacin da dubban 'yan kasar ke cigaba da tserewa da kuma neman wajen mafaka, bayan biris da kiraye-kirayen tsagaita wuta da bangarorin da sa ga maciji suka yi.

A lokacin wata ziyara a sansanin 'yan gudun hijirar Sudan da ke makwabciyar kasar Chadi, Ministan cigaba da harkokin Afirka na Burtaniya, Andrew Mitchell, ya bayyana tsananin bukatar karuwar kayayyakin agaji ga Sudan.

Ya kuma sake jan hankali da rokon dakarun da ke wannan yaki su sassautawa al'ummarsu.

Wannan kiran na zuwa adadai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke sake gargadi matsananciyar yunwa ta afkawa yankin.

Ita ma jakadaciyar Amurka a Majalisar, Linda Thomas-Greenfield, ta ce a kullum lamuran sake rincabewa suke yi.

''Yanayin ya ta'azzara sama da abin da aka gani a bara. Muna ganin karuwar mutanen da ke tsallaka iyaka. Muna ganin yanayi na akuba wajen mutanen da suka tsallaka iyaka zuwa Chadi, da yanayi na yunwa da suke ciki.

Mutane sun galabaita saboda rashin abinci, kuma bai kamata a ce mun yasar da su ba. Suna bukatar taimakonmu kamar yada muke baiwa duk wani wuri da ake fama da irin wannan rikici a duniya,'' in ji Linder.

Yayinda ake gab da cika shekara guda cur da soma wannan yaki tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, alkaluma na nuna cewa sama da 'yan kasar miliyan 10 ne suka gudun hijira, yawancinsu na kasashe makofta kamar Tchadida Sudan ta Kudu.