Sudan za ta aike da dakarun soji yankin Darfur

Sudanese refugees in Chad. File photo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An kashe fiye da mutum 80 a hare-hare biyu da aka kai a yammacin Sudan, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Gwamnatin Sudan za ta aike da karin dakaru yankin Darfur, sakamakon rikice-rikicen da suka barke a yankin.

Firaiminista Abdalla Hamdok ya ce dakarun za su kare mutane a lokacin da suke zuwa gonakinsu.

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kashe mutum fiye da 60 a yankin ranar Asabar, sannan suka sake kashe mutum 20 ranar Lahadi, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Dubban daruruwan mutane ne suka mutu a yakin da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye tun shekarar 2003. Rikicin ya raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Bayan an kwashe shekaru, mutane sun soma komawa gidajensu domin soma noma daga watan Yuli zuwa Nuwamba bayan an cimma yarjejeniyar da gwamnati ta dauki nauyinta wata biyu da suka wuce.

Sai dai hakan ya haddasa sabon rikici a kan mallakar filaye tsakanin mutanen da suke aiki a gonakin da kuma wadanda suka koma don ci gaba da aiki a gonakin nasu.

Bayanan bidiyo, Wakilin BBC Mohanad Hashim na daya daga cikin 'yan jarida na farko-farko da suka dinga bulaguro a yankin ba tare da takurawa ba cikin shekara 10

A rikicin baya-bayan nan, an kona kauyuka da dama, da kasuwanni da shaguna sannan aka sace abubuwan da ke ciki, a cewar shugaban kungiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.

"Ci gaba da rikici a yankuna da dama na Darfur ya haddasa karin raba mutane da gidajensu, lamarin da zai shafi aikin gona, da kuma asarar rayuka da kara yanayin gudun hijira," a cewar sanarwar da ta fitar.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin rikicin.

Kotun hukunta masu manyan laifuka ta duniya tana neman tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir, wanda aka hambarar daga kan mulki a bara, inda take zarginsa da aikata laifukan yaki da kisan kare-dangi a yankin.

Zai iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifi.

Tuni dai aka sami Bashir da laifin cin hanci.

Map of Sudan