Sauyi a Sudan: An soke hukuncin ridda, an ba da damar shan giya a kasar

Asalin hoton, AFP
Bayan shekaru fiye da 30 ana amfani da dokokin Musulunci a Sudan lokacin mulkin tsohon Shugaba Omar al-Bashir, yanzu hukomomi a kasar sun gabatar da wasu sauye-sauye cikinsu har da barin mutanen da ba Musulmi ba su rika shan giya, da soke dokokin hukunta masu ridda da daina hukunta masu laifi ta hanyar bulala a bainar jama'a.
"Za mu soke dukkan dokokin da suka keta hakkin dan adam," in ji Ministan Shari'ar kasar Nasredeen Abdulbari.
An amince da wani bangare na sabbin dokokin a makon jiya amma wannan ne karon farko da aka yi wa jama'a bayani kan abubuwan da suka kunsa.
Kazalika Sudan ta haramta yi wa mata kaciya.
A cikin sababbin dokokin, ba sai mace ta nemi izinin mijinta ba kafin ta yi tafiya da 'ya'yansu.
Ana gudanar da wadannan sauye-sauye ne shekara guda bayan tumbuke tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir sakamakon jerin zanga-zanga.
Gwamnatin da ke mulki ba ta ga-maciji da mutanen da suka jagoranci kifar da gwamnatin Mr Bashir da tsoffin abokansa da ke rundunar soji, wadanda suka yi masa juyin mulki.
Mece ce sabuwar doka kan shan giya?
Yanzu an amince mutanen da ba Musulmi ba su sha barasa a boye, ko da yake za a ci gaba da hukunta duk Musulmin da aka kama ya sha giya, a cewar Mr Abdulbari a hirarsa da gidan talbijin na kasar
Kazaliza su ma wadanda ba Musulmi ba za a hukunta su idan aka same su tare da Musulmi suna shan giya, in ji jaridar Sudan Tribune wacce ta ambato shi yana shaida mata hakan.
Ya kara da cewa gwamnatin tana kokarin kare hakkin mutanen da ba Musulmai ba, wadanda su ne kashi uku na al'ummar kasar.
Yanzu an amince su rika shan giya, su shiga da ita kasar su kuma sayar.
"Fatanmu shi ne mu kawar da dukkan wani bambanci wanda tsohuwar gwamnati ta nuna da sannan mu bai wa kowanne dan kasa dama kuma a samu sauyin dimokradiyya," in ji shi.
Tun a watan Afrilu aka amince da sauye-sauyen amma wakilin BBC a Khartoum Mohamed Osman ya ce sai yanzu za su soma aiki.
Yaya sauran sauye-sauyen suke?
Kafin yanzu, duk mutumin da ya yi ridda zai iya fuskantar hukuncin kisa.

Asalin hoton, AFP
Misalin da ya fi shahara shi ne na Meriam Yehya Ibrahim Ishag, mace mai ciki wacce aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta auri wani Kirista a 2014.
Ta samu damar tserewa daga kasar amma dokar ridda tana kunshe a cikin tsarin mulkin kasar kafin wannan sauyi.
Ayyana cewa wani ya yi ridda "barazana ce ga tsaron al'umma," a cewar Mr Abdulbari.
Lokacin mulki Shugaba Bashir, 'yan Hisbah suna yawan yi wa mutanen da aka samu da laifi hukuncin bulala a bainar jama'a amma yanzu Mr Abdulbari ya ce an soke hukunci.











