Su wane ne janar-janar da ke yaƙi da juna a Sudan

Asalin hoton, Getty Images
Ƙarar kiɗan tashin bam, layukan wutan da ke yawo a sama, baƙin hayaƙi da furgici da ake ciki da rashin tabbas lokacin da harsashi da roka suka cika faɗin Khartoum.
Rayuwa a babban birnin Khartoum da sauran birane a ƙasar, ta wayi gari cikin wani mummunan yanayi, ta kuma ƙazanta.
A tsakiyar rikicin akwai janar-janar biyu – Abdel Fattah al-Burhan shugaban sojojin Sudan da kuma Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemedti shugaban tawagar masu kasayar sarki ta RSF.
Su biyun suna aiki ne tare, tare kuma suka yi juyin mulki – yanzu kuma suna rikicin wane zai fi iko, abin da yake lalata Sudan.
An samu koma baya mai yawa tsakanin laƙar mutanen biyu.
Dukansu sun taka rawar azo a gani wajen kawo ƙarshen tashin hanakin da aka samu daga ‘yan tawayen Darfur, a wani yakin basasa da aka yi a yankin yammacin Sudan a 2003.
Janar Burhan ne ya samu iko wajen tafiyar da lamuran sojin Sudan a Darfur.
Hemedti ɗaya ne daga cikin kwamandojin manyan ƙungiyoyin masu makami ta Larabawa, waɗanda ake kiransu da Janjaweed a taƙaice.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Waɗanda gwamnati ta kafa domin kawo ƙarshen kungiyoyin ‘yan tawayen da ba na Larabawa ba a Darfur.
Majak D’Agoot shi ne mataimakin daraktan hukumar leken asiri a lokacin, kafin ya zama mataimakin ministan tsaro na ƙasar Sudan ta Kudu lokacin da aka raba su a 2011.
Ya haɗu da Janar Burhan da Hemedti a Darfur, inda ya yaba musu yana cewa aikinsu tare na tafiya daidai. Amma ya shaida wa BBC cewa ya ga alamar ɗaya daga cikinsu na yunƙurin neman ɗarewa kan iko.
Hemedti ba wani ba ne bayan shugaban ƙungiyar masu rike da makami “waɗanda suke aikin taimaka wa sojoji wajen daƙile ‘yan tawaye,” Amma shi Burhan soja ne da ya samu horo.
Sojoji ne suke riƙa tafiyar da Sudan gabanin a bata ‘yancin kai.
Amma cikin dabarun gwamnati a Darfur, akwai amfani da sojoji a-kai-a-kai da kabilu masu ƙarfi da jiragen sama domin yaƙar ‘yan tawayen – kuma babu abin da ya shafe su idan hakan zai rutsa da fararen hula.
An bayyana rikicin Darfur a matsayin na kisan kiyashi a ƙarni na 21, yayin da Janjaweed ke kan gaba wajen kashe ƙabilu masu yawa da fyaɗe a matsayin makamin yaƙi.
Hemedti daga bisani ya zama kwamandan abin da za a iya bayyana shi a matsayin tsiro ko gyauron sojojin sa-kai na Janjaweed, wato rundunar RSF.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙarfin faɗa ajin Hemedti ya faɗaɗa ne lokacin da ya fara shigo da makamai ga dkarun haɗin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta da ke yaƙi a Yemen.
Shugaban soji na Sudan na lokacin Omar Al-Bashir ya dogara ne kacokan kan tawagar RSF domin taimakawa sojoji, manufar hakan ita ce daƙile ƙarfin duka dakarun kasar ka da wani ya samu cikakken iko.
A ƙarshe bayan kwashe watanni ana gudanar da zanga-zangar – Janar-janar ɗin sun haɗe kansu sun suka hamɓarar da Bashir a watan Afrilun 2019.
A ƙarshen shekarar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa da farar hula za ta jagoranta, Janar Burhan ya zama shugaban ƙasa shi kuma Hemedti ya zama mataimaki.
Bayan shekara biyu – har zuwa ƙarshen watan Oktoba 2021 – yayin da sojojin suka ƙwace iko daga hannunsu – Janar Burhan ya zama shugaba yayin da Hemedti ya sake zamar masa mataimaki
Siddiq Tower Kafi mamba ne a cikin gwamnatin farko da aka ruguje kuma akai-akai yana tattaunawa da shugabannin biyu.
Ya ce bai ga alamar wata rashin jituwa ba, har sai bayan juyin mulkin 2021.
Daga nan kuma sai “Janar Burhan ya fara dawo da tsofaffin abokansu ma su ra’ayin rikau,” ya shaida wa BBC.
“A buɗe abin yake cewa Janar Burhan yana sake ƙafa tsofaffin abokansa ne da suka yi aiki lokacin Omar al-Bashir.”
Mista Saddiq ya ce wannan ne ya sanya Hemedti shakku a cikin tafiyar, yana jin cewa abokan Bashir ba su taɓa aminta da shi ba.
Siyasar Sudan kullum a mamaye take da masu ƙarfin faɗa a ji, daga kabilu manya da ke Khartoum da kuma tamfin Nilu.

Asalin hoton, Getty Images
Hemedti ya fito ne daga yankin Dafur, kuma manyan ƙasa a Sudan kan yin magana a kan shi da sojojinsa cikin raini, wanda suke cewa mutumin ƙauye ne ba zai iya mulkin al’umma ba.
Cikin shkara biyu ko uku da suka gabata, ya yi ƙoƙarin kai kansa wani babban matsayi a ƙasara matsayinsa na wanda ya fito daga ƙabilar da ba ta da rinjaye – ya na ƙoƙarin haɗa hannu da ‘yan tawaye da ke Darfurda kuma na kudancin Kordofan da a baya a ka nemi a kashe su.

Ya sha kwashe lokacin yana magana akan buƙatar da ake da ita ta dimokradiyya duk da cewa dakarunsa sun kashe fararen hula a yayin zanga-zanga a baya.
Alaƙa ta riƙa tsami tsakanin sojoji da RSf lokacin da ake ƙara kusantar wa’adin kafa gwamnatin farar hula, inda suka mayar da hankali kan neman a tabbatar da kasancewar RSF cikin dakarun ƙasar.
Wuta da hayaƙi kawai ake gani a saman Khartoum yayin da janar-janar ɗin suka fara faɗa da juna.











