'Fasa-kwaurin mutane zuwa Turai ya fi na miyagun ƙwayoyi kawo kuɗi'

- Marubuci, Daga Lucy Williamson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Calais
Wasu mutum biyu da ke ɓoye cikin ciyayi a gaɓar teku da ke arewa da Calais na jiƙa wa sabuwar firaministar Birtaniya aiki.
A ɓoye cikin duhu, sun shirya wani kwale-kwalen da zai tsallaka teku da wasu 'yan ci-rani a daidai wurin da ake tsallaka teku na Channel.
A sararin samaniyar yankin ana iya jin ƙarar wani jirgi maras matuki da Birtaniya ta tura domin a fara farautar abin da ya zama jiki a yanzu.
Kasa da kilomita guda daga wurin kuma, wasu jandarmomin Faransa na nazarin hoton mutum biyun da kyamarorin jirgi maras matukin ke dauka, wanda da yake cikin dare ne, yana bayar da launukan ƙwai da na ruwan goro.
Cikin wasu dakikoki jandarmomin suka fada cikin wata ƙaramar mota ta musamman, wadda ita ma Birtaniya ce ta samar da ita, kuma jim kadan bayan haka sun nufi wurin da mutanen ke ɓoye.
Isa wurin bai wuce tsawon minti biyar ba a motar, amma yanayin wurin mai sarkakiya yasa tilas a kafa za jandarmomin za su taka domin isa wurin, inda akwai ciyayi da shuke-shuken da kan kai wa mutum har kirji.
Mutanen biyu sun tsere yayin da suka hango jandarmomin da suka nufi wurin da suke, kuma sun bar kwale-kwalen da ba su kammala shiryawa ba, ciki har da man fetur da injin din kwale-kwalen da wasu buhuna biyu dauke da rigunan ceto wanda ruwa ya ci a teku.
"Sarkakiyar wannan wurin na hana mu aikinmu," inji Janar Frantz Tavart ya shaida min.
"Masu fasa-kwaurin sun san haka, shi yasa suke boye kwale-kwale a wurin da gangan."
End of Karin labaran da za ku so ku karanta
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Janar Tavart ya yaba wa kokarin Birtaniya:
"Jirage marasa matukin na da muhimmanci sosai domin su kan gano wuraren da aka ɓoye sosai kamar wannan."
Sai dai an kashe makudan kudade a wannan gabar tekun mai tsawon kilomita 160 na tsawon shekaru.
Faransa da Birtaniya sun rika zuba kudi domin samar da kimiyya da fasahar da za su taimaka wajen magance matsalar masu yin fasa-kwaurin 'yan ci-rani.
Jami'an Faransa sun ce kawo yanzu suna iya hana rabin masu tsallakawa cimma muradunsu, amma kimanin mutum 30,000 sun sami damar tsallakawa zuwa cikin Birtaniya a cikin wannan shekarar kawai.
Sai dai ba 'yan cirani ne kawai ke amfana da wannan hanyar ba.
An gano wasu sababbin wuraren da 'yan sumoga ke amfani da su.
Wani babban jami'in Faransa ya shaida mana cewa wasu masu fasa-kwauri daga Albaniya sun fara aiki a yankin na Calais, wadanda ba su da alaka da wasu Kurdawa da 'yan Iraki 'yan fasa-kwaurin.
Janar Tavart ya ce: "Ganin tsadar kudin da ake biya domin tsallaka wa da mutumguda (wanda ya kai dala dubu hudu), inda ake sanya kimanin mutum 40 cikin kwale-kwale daya.
"Idan ka yi lissafi da kanka, za ka gane cewa akwai kazamar riba a wannan kasuwancin, har ya zarce na masu safarar miyagun ƙwayoyi."

Asalin hoton, Getty Images
Wasu jama'a sun bayar da shawara cewa karancin ma'aikata da ya biyo bayan ficewar Birtaniya daga tarayyar Turai ya taimaka wajen jan hankulan mutane zuwa Birtaniya.
Yan kasar Albaniya ne dai suka fi yawa cikin turawan da ke tsallaka teku daga Faransa zuwa Birtaniya, inda wani mai otel ya ce ya yi mamakin yawan Albaniyawan da ke shigewa a kullum:
"Anya akwai sauran 'yan Albaniya a kasarsu ta asali kuwa?"
A kan wani titi da ke wajen garin Calais, da sanyin safiya mun hadu da Sikunder, wani matashi mai shekara 17 da haihuwa tare da abokansa sanye da barguna masu kyalli.
Dukkansu 'yan Afgahnistan ne, kamar yadda suka shaida mana, kuma sun ce 'yan sandan Faransa ne suka ceto su daga wani kwale-kwalen da ya kusa nutsewa da su.

Asalin hoton, Getty Images
Na tambayi Sikunder ko ya san cewa akwai wani shiri na gwamnatin Birtaniya na mayar da 'yan ci-rani zuwa kasar Ruwanda?
Sai ya ce, "Na ji labarin haka, amma wasu 'yan uwana mazauna Birtaniya sun shaida min cewa tuni aka yi watsi da wannan shirin, kuma muna iya zuwa Birtaniya."
Wannan ne karonsa na biyu na kokarin tsallakawa, amma ya ce ba zai fasa gwada tsallakawa ba har sai ya yi nasara.

Asalin hoton, Getty Images
Na gamu da mutane masu yawa da ke ganin sauyin firaminista a Birtaniya zai kawo karshen shirinta na mayar da 'yan ci-rani zuwa Ruwanda.
Sannan babu alamar cewa sabuwar Firaminista Liz Truss na goyon bayan shirin.
Jess Sharman ta kungiyar Care4Calais ta ce mutane na sa rayukansu cikin hadari kawai domin su tsallaka teku zuwa Birtaniya saboda aba za a ba su damar zama a Faransa ba.
"Bai dace a bar su su shigo nan ba. Haka na kasancewa ne saboda dokokin Birtaniya sun bayar da kafar neman mafaka a nan."
Komai na iya sauyawa, amma kafin haka ya faru, wasu 'yan fasa-kwaurin na can suna kokarin tsallakwa da masu bukatar shiga cikin Birtaniya ko da kuwa za su halakar da su domin shigar da su Birtaniya.










