Baƙar azabar da 'yan ci-rani ke fuskanta tare da 'ya'yansu

Asalin hoton, Getty Images
Gargadi: Wannan labari na kunshe da bayanai a farko da za su tayar da hankalin mai karatu.
Dr Yesenia Williams ta kadu matuka da abin da ta gani a wata cibiyar marabtar ‘yan cirani da ke arewa da yankin Darien Gap mai hadari, ta kasa fadawa ko da abokanan aikinta kan batun a farko.
"Ban sammani cewa suna shan wuya da kuma mawuyacin hali ba,’’a cewar likitar yaran.
A tsawon kwanaki tara da ta dauka a wani asibitin ‘yan cirani da ke San Vicente, ita da abokan aikinta sun yi jinyar dubban ‘yan cirani da suka jigata, wadanda kuma suka yi tafiyar cikin manyan dazuka tsakanin Panama zuwa Colombia.
A labaran da suka bayar, likitocin sun bayyana irin matsanancin wahala da kuma hanya mafi hadari a duniya da ‘yan ciranin ke bi don zuwa wurare, inda a yanzu suke fatan samun sauki a Amurka.
Yanayin da yawancin yara ke ciki ne ta yi matukar kada Dr Williams.
Kishirwa ta sanya idanun yaran bushewa da kuma komawa ciki-ciki. Idan suka yi kuka, hawaye ba sa fita, in ji likitar. Wasu sun shiga dimuwa da ba za su iya tuna sunayensu ba.
"Sun fuskanci abubuwa da bai kamata ace kamar su sun gamu da su ba,’’ a cewar likitar. Ta kuma bayyana irin cin zarafi da hare-hare da ‘yan ciranin suka fuskanta yayin tsallakawa.
Bakar azaba
Yankin na Darien Gap na da daji da ya kai hekta 575,000, wanda ya raba yankin da Kudancin da kuma Tsakiyar Amurka.

Babu hanyoyi masu kyau da za su kai zuwa yankin cikin sauki, wuri kuma da fashi da fyade suka yi kyamari.
Duk da irin haduran, ‘yan cirani da yawa na yin tafiyar da ta kai kilomita 97 a kafa tsakanin koramu da tsaunuka, inda suke kai kusan mako daya kafin su isa.
Cikin ‘yan cirani 133,000 da aka kiyasta sun tsallaka zuwa yankin na Darien Gap a shekara da ta gabata, kusan 30,000 daga ciki yara ne.
Yawancin wadanda ke yin balaguron kan hanyar mafi hadari, sun kasance iyalai ne da suka fito daga kasashen Haiti da Cuba da Venezuela. Sai dai Dr Williams ta ce ta ga yara da ke zuwa yankin da kansu.
A cikin kwanaki tara da likitocin suka yi a San Vicente, sun yi jinyar wasu ‘yan cirani 500 da suka tsallaka zuwa yankin, inda suka tattauna da 70 daga ciki.
Mika yara ga baki
Dr Jose Antonio Suarez, wani likitan cutuka masu yaduwa cikin tawagar kwararrun likitocin, ya tuno yadda ya kula da wani mutumin Venezuela mai shekara 60 da ke yin tafiya da wasu yara biyu, masu shekara hudu da biyar.

Asalin hoton, Getty Images
Dr Suarez ya dauka cewa mutumin kakan yaran ne, amma dan ciranin ya fada masa cewa ba shi da wata alaka da su.
Dan ciranin ya ce mahaifiyar yaran, wacce ta kasance ‘yar Haiti, da ya hadu da ita a dazuka kan hanyar zuwa yankin, ya fada cewa ta bukaci ya dauke su zuwa San Vicente saboda ba ta da sauran karfi da za ta iya tafiya.
"Damuwa da tsananin wahalar ta kai ga iyaye kan mika yaro zuwa hannun wani bako da basu san shi ba,’’ in ji Dr Suarez.
Labaran tashin hankali na ‘yan cirani da ke tsallakawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dr Roderick Chen-Camaño, wani likita mai bincike kan barkewar cutuka dan kasar Panama, da ya dauki tsawon shekaru yana aiki da al’ummomi a yankin, ya ce da farko yana sammanin cewa ya shiryawa abin da zai tarar a asibitin na ‘yan cirani.
"Ban yi tunanin zan ga wani abu sabo ba,’’ in ji likitan. Ya kuma tuno yadda wani dan cirani daga Venezuela ya barke da kuka bayan fadawa likitan abin da idonsa ya ganin a asibitin.
Mutumin ya ce yana cikin kungiyar ‘yan cirani hawa tsaunuka da dama da suka raba Colombia da Panama lokacin da wata ‘yar cirani daga Haiti ta fado daga wani tsauni.
Abin da ya faru gaba ya jefa mutumin cikin tashin hankali.
A daidai lokacin da mijin matar ya fahimci cewa ta mutu, kawai sai ya jefa daya daga cikin ‘ya’yansu kan bakin dutse, in ji dan ciranin.
Mutumin dan Venezuela ya bayyana irin kokari da ya yi na dakatar da mahaifin yaron dan kasar Haiti kan yunkurin jefa dansa, sai dai bai samu nasara ba.
Bai kuma samu damar dakatar da dan kasar Haitin yin tsalle ya fada shi ma.
Yayin da BBC bata samu damar tabbatar da gaskiyar labaran wasu ‘yan ciranin ba, alkaluma daga Hukumar Kula da ‘Yan Cirani ta Duniya sun nuna cewa gwamman ‘yan cirani ne ke mutuwa duk shekara yayin tsallakawa zuwa yankin Darien Gap.
Ratsawa cikin gurbataccen ruwa
Dr Williams ta ce abin bacin rai ne cewa abu kadai da tawagar likitocin suka iya yi a asibitin da aka kaf ana wucin gadi, shi ne rage alamun cutuka ba tare da magance musabbabin su ba.
"Mun ga kadan daga cikin wahalhalu da ‘yan cirani ke fuskanta,’’ a cewar likitar.
Sai dai Dr Suarez, da ya fito daga Venezuela, na cike da farin ciki cewa zai iya taimaka wa wasu ‘yan kasar sa.

Asalin hoton, GORGAS INSTITUTE
Yayin da ya kasance ‘yan Haiti ne ke jurewa zuwa yankin na Darien Gap a shekara da ta gabata, said ai a wannan shekara ta 2022, ‘yan Venezuela ne ke tururuwar zuwa.
Yawancinsu sun baro Venezuela ne a shekarun baya-bayan nan, daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki da kuma kokari da mutane ke yi na samun na kaiwa bakin salati a wasu kasashen Kudancin Amurka.
Amma dokar kulle da aka sanya lokacin annobar korona, ta sanya ‘yan ciranin shiga matsanancin wahala, wanda ke nufin cewa yawancinsu na tafiya zuwa arewaci don neman saukin rayuwa.
Wata mara lafiya da Dr Suarez ta yi wa jinya a asibitin, ta samu fitowar kuraje da ba a saba gani ba a kan yatsunta da kuma kafafu.

Asalin hoton, GORGAS INSTITUTE
Kafafun masu kaikayi da kuma suka yi ja, sun tunawa wani likita mai shekara 67 wani abu da bai gani ba tun yana dan samari lokacin da ya kai ziyara tsibirin Unare da ke mahaifarsa ta Venezuela.
Dr Suarez ya duba marar lafiyan da wasu karin mutum 20 da suka zo sansanin jim kadan bayan nan da wasu cutuka na kurajen.
Sai dai wani daga cikin abokan aikin Dr Suarez ne, Rosela Obando, ta gano cewa yawancin mutanen na dauke da kuraje, sai dai wasu yara basa dauke da su.
Sun ce sun kamu da kurajen ne yayin ratsawa cikin gurbataccen ruwa dake hanyar zuwa yankin na Darien Gap, amma yara sun kubuta saboda iyayensu sun dauke su a sama don kada ruwa ya tafi da su.

Asalin hoton, Getty Images
Dr Suarez ya yi gargadin cewa a lokacin da kurajen ke musu lahani, wani abu da yafi tayar da hankali shi ne shan gurbataccen ruwa da suke yi wanda shi ma zai janyo musu wasu cutuka na daban.
Amma ya ce ‘yan cirani d ake tsallakawa zuwa yankin Darien basu da zabi, saboda idan suka ce za su dauki ruwa cikin robobi, zai iya zamo musu wani nauyi kan hanyarsu.
Likitan ya ce shan ruwa daga wanda ya gurbata zai iya janyo musu cutuka a cikinsu, sannan rashin shan ruwa kuma zai haifar musu karancin ruwa a jiki.
‘Ruwa ya tafi da wasu mutane’
Kowanne Daya daga cikin likitocin, ya fuskanci labaran da suka tayar musu da hankali.
Wani mai nazarin halittu, Yamika Diaz, ya ce ya dauki matakin yin aiki a sansanin na yankin Darien Gap bayan haduwa da Delicia. An samu yarinyar ‘yar shekara biyar kusa da mahaifiyarta a tsakiyar daji.
An dauki Delicia zuwa cibiyar da Dr Diaz ke aiki domin gwajin jininta ko tana dauke da wasu cutuka na zazzabin cizon sauro da wasu cutuka na daban.
Lokacin Dr Diaz ya tambayi Delicia ko za ta iya tuna abin da ya faru da ita, kawai cewa ta yi ‘ruwa ya tafi da ‘yan uwanta’.
Dr Diaz ya ce baiwa ‘yan ciranin kulawa ya canza rayuwarta da ta sauran mutane.
‘Kana ganin komai daban,’’ a cewar likitar, da ta baro asibitin na wucin gadi da ke sansanin da kafarta saboda ta baiwa wata ‘yar cirani takalmarta saboda ta ta sun lalace.











