Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyar Saudiyya na neman Messi, Arsenal ta koma maganar Vlahovic
Kungiyar Al Hilal, ta Saudiyya wadda ke hamayya da sabuwar kungiyar Cristiano Ronaldo Al Nassr, na neman sayen Lionel Messi a kan albashin dala miliyan 300 a shekara. (Mundo Deportivo)
Arsenal ta sake komawa kan maganar sayen dan gaban Juventus Dusan Vlahovic, na Serbia mai shekara 22, wanda aka kiyasta kudinsa zai kai yuro miliyan 110 (La Repubblica )
Haka kuma Gunners din sun mika sabon tayi a kan dan wasan gaba na gefe na Shakhtar Donetsk Mykhaylo Mudryk, dan Ukraine, kuma cinikin na daf da kammala. (Fabrizio Romano)
Tottenham na sha’awar sayen dan wasan gaba na gefe naBelgium Leandro Trossard, daga Brighton. (Evening Standard)
Kungiyoyin Sifaniya da Faransa da Jamus da kuma Italiya na sanya ido kan yadda za ta kasance a game da dan bayan Portugal Joao Cancelo, bayan da ya rasa matsayinsa na kasancewa cikin ‘yan wasan farko-farko a Manchester City. (Telegraph)
Paris St-Germain ta karbi tayin Wolves a kan dan wasanta na tsakiya dan Sifaniya Pablo Sarabia, (AS )
Watakila Southampton ta nemi dan bayan Luton Town James Bree, dan Ingila, yayin da take neman dn baya a watannan. (The Athletic)
Cinikin Leeds na sayen matashin dan wasan gaba na kungiyar Faransa ta Hoffenheim Georginio Rutter, mai shekara 20, zai kusa fam miliyan 35. (Sky Sports)
Everton na neman sayen ‘yan gaba biyu a watan nan. (Football Insider)
Besiktas na sha’awar sayen dan wasan gaba na Wolves da Mexico Raul Jimenez, domin maye gurbin dan gabanta Wout Weghorst, dan Holland wanda zai tafi Manchester United. (Fotospor ta Metro)
Wolves za ta sayi matashin dan wasan gaba Matheus Cunha na Brazil da ke zaman aro a kungiyar daga Atletico Madrid a kan kudin da ya kai fam miliyan 44.4 (Fabrizio Romano)
Brentford ta gabatar da tayin sayen dan gaban Antalyaspor dan Amurka Haji Wright. (Tom Bogert)
Bournemouth na da kwarin guiwar sake sayen dan wasan tsakiya na Netherlands Arnaut Danjuma, mai shekara 25, daga Villarreal, yayin da rahotanni ke cewa Everton na sha’awarsa. (The Athletic )