Man Utd da Chelsea na son Walker-Peters, Aubameyang na son komawa Barca

Manchester United da Chelsea na duba yuwuwar sayen dan bayan Southampton da Ingila Kyle Walker-Peters. (Talksport)

Pierre-Emerick Aubameyang, na son barin Chelsea domin ya koma tsohuwar kungiyarsa Barcelona. (AS)

West Ham ta tattauna da kungiyar Amiens ta Faransa a kan cinikin dan wasan tawagar Senegal na baya Formose Mendy, mai shekara 22. (The Athletic)

Leeds na samun cigaba a kokarin da take yin a sayen matashin dan wasan Hoffenheim na tawagar ‘yan kasa da shekara 21 ta Faransa Georginio Rutter. (The Athletic)

Tottenham ta yanke shawarar kada ta nemi tsawaita kwantiragin dan gabanta naBrazil Lucas Moura, fiye da kakar da ake ciki. (Telegraph)

An yi watsi da tayin da Aston Villa ta yi a kan dan wasan tsakiya na Marseille Matteo Guendouzi.

Dan wasan na Faransa ya taka leda a karkashin kociyan Villa Unai Emery a Arsenal. (Mail)

Wolves na kara tattaunawa a kan cinikin fam miliyan 10 domin dawo da tsohon dan wasan tsakiya na Southampton da Fulham Mario Lemina, gasar Premier. A yanzu dan wasan tawagar Gabon din yana Nice. (Sun)

Haka kuma kungiyar ta Wolves na son sayen dan bayan Atletico Madrid Felipe, na Brazil. (Reuters)

Watakila Atleticon ta nemi dan wasan Leicester da Turkiyya Caglar Soyuncu, a matsayin wanda zai maye gurbin Felipe. (Matteo Morretto, a Twitter)

West Ham na tare duk wata dama ta neman sayen dan gabanta Michail Antonio, dan Jamaica wanda Wolves ke so. (Express da Star)

Kungiyar Watford ta gasar Championship na son sayen matashin dan wasan Uruguay na gaba Facundo Pellistri daga Manchester United. (Telegraph)

Dan gaban Portugal Joao Felix, ya tafi Chelsea aro har zuwa karshen kakar nan, amma kuma mai yuwuwa ya koma Atletico Madrid a bazara, abin da ka iya sa kociyan kungiyar Diego Simeone ya tafi kasancewar dangantaka ta yi tsami tsakaninshi da dan wasan. (Mirror)

Zuwan Felix Stamford Bridge ba zai hana Blues ci gaba da neman wasu ‘yan wasan ba, saboda har ma ta ci gaba da tattaunawa da Borussia Monchengladbach a kan dan gaban Faransa Marcus Thuram. (Fabrizio Romano)