Muhimman abu biyar kan ganawar Trump da Zelensky a Washington

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya sake komawa fadar White House domin ganawa da shugaban Amurka, Donald Trump, inda suka sake tattaunawa kan yaƙin Ukraine.
Shugabannin ƙasashen turai da dama ne suka raka Zelensky Washington ganawar, wadda ta zo kwanaki kaɗan bayan Trump ya gana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin a Alaska, duk da ganawar tasu ba ta samar da sakamako mai kyau da aka yi tunani ba.
Duk da irin maganar da Trump ya riƙa yi, da kuma maganganu masu daɗi da takwarorinsa na ƙasashen turai suka yi bayan taron, har zuwa yammacin Litinin babu wata muhimmiyar sanarwar game da nasarar da aka samu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ga wasu muhimman tsaraba da muka tattaro daga ganawar.
Putin da Zelensky za su gana?
Bayan ganawar shugabannin biyu, Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta wato Truth cewa ya kira Putin a waya, kuma sun fara shirya yadda shugaban na Rasha da na Ukraine za su haɗu.
Trump ya ce bayan shugabannin biyu sun gana, za su sake haɗuwa a tare, su tattaunawa domin samar da mafita.
Yanzu za a sa ido ne a ga yadda za a iya haɗa shugabannin guda biyu da suke tsananin adawa da juna a ɗaki guda, su zauna ido da ido su tattauna, wanda shi ne zai zama karo na farko tun bayan ɓarkewar yaƙin Ukraine a watan Fabrailun 2022.
Tsagaita wuta ko ƙarshen yaƙi?
Trump ba ya so a fara maganar tsagaita wuta ba tare da an cimma yarjejeniyar mai kyau ba, wadda yake tunanin za ta kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya.
A baya, Ukraine ta sha nanata cewa ba za ta fara tattaunawa kan shiga wata yarjejeniya ba har sai Rasha ta daina kai mata hari.
Sai dai alamu na nuna tsagaita wuta za ta fi sauƙin samuwa, sama da kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, domin cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin zai ɗauki watanni, kuma ba dole ba ne Rasha ta tsaya da kai hare-hare a lokacin.
Trump ya ce bai da yaƙinin za a samu yarjejeniyar a zama na gaba, amma shugabannin ƙasashen turai suna ganin zai fi kyau a tursasa Rasha a samu yarjejejiyar.
Tallafin tsaro ga Ukraine
Trump ya bayyana wa Zelensky cewa Amurka za ta tallafa wa Ukraine wajen samar da tsaronta, duk da cewa bai fayyace irin tallafin da zai bayar ba.
Da manema labarai suka tambaye shi ko tallafin zai kai tura sojojin Amurka domin kare Ukraine, bai bayar da amsa ba kai-tsaya, amma sai ya ce, "za mu ba su kariya sosai."
Wannan maganar za ta yi tasiri sosai a yunƙurin tsara yarjejeniya a tsakanin Rasha da Ukraine.
Amma a taron manema labarai a ranar Litinin, Zelensky ya ce daga cikin tallafin tsaron akwai shiga yarjejeniyar makamai na dala biliyan 90 tsakanin Amurka da Ukraine, inda ya ce za su mallaki wasu manyan makamai daga Amurka.
Zelensky ya shiga da Amurka da ƙarfinsa
Ganin yadda aka ziyararsa fadar shugaban Amurka a baya ba ta yi daɗi ba, shugaban na Ukraine a wannan karon sai ya shirya da kyau.
A wannan karon, Zelensky da kwat ya shiga ƙasar, maimakon rigar sojoji da yake sakawa, wadda a wancan lokacin Trump ya masa shaguɓe cewa, "baƙon nawa ya yi shiga mai kyau."
Haka kuma Zelensky ya yi amfani da damar wajen ƙulla alaƙa, inda ya miƙa saƙon matarsa, Olena Zelenska zuwa da uwargidan shugaban Amurka, Melania Trump, ta hannun shugaban na Amurka.










